Friday, December 5
Shadow

Duk Labarai

Hukumar ‘yansanda ta saki sunayen mutane dubu 10 da suka yi nasara wajen neman aikin

Hukumar ‘yansanda ta saki sunayen mutane dubu 10 da suka yi nasara wajen neman aikin

Tsaro
Hukumar 'yansanda ta PSC ta saki bayanan mutane dubu 10 da suka yi nasarar tsallakewa mataki na gaba a neman aikin dansandan. Mutane 61,092 ne dai aka ajiye gefe wanda basu tsallake ba zuwa wannan matsayi. Hukumar tace dan tabbatar da an yi adalci wajan fitar da sunayen ta yi aiki tare da majalisar tarayya, da hukumar tabbatar da an yi raba daidai wajan bada aikin gwamnati, da kuma hukumar 'yansanda. Tace ta tabbatar an baiwa kowace karamar hukuma a Najeriya cikin 774 da ake dasu damar wakilci a cikin wadanda aka dauka din. Shugaban hukumar, Ikechukwu Ani ne ya bayyana hakan.
Farashin Naira zai tsaya akan 1,450 akan kowace dala

Farashin Naira zai tsaya akan 1,450 akan kowace dala

Siyasa
Wata hukumar dake saka ido akan farashin kudaden Duniya, Fitch Ratings ta yi hasashen cewa, farashin Naira zai kare akan 1,450 ne akan kowace dala har zuwa karshen shekarar 2024. Daraktan hukumar, Gaimin Nonyane ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi kan Najeriya da kasar Misra/Egypt. Ya kara da cewa, har yanzu Naira bata daidaita ba akan farashi daya tun bayan da aka cire tallafin dala. Yace zuwa shekara me zuwa ma Nairar zata ci gaba da faduwa amma ba zasu iya bayyana a farashin da zata tsaya ba.
Gwamnoni sun kashe Naira Biliyan dari tara da sittin da takwas(968,000,000) wajan Shan kayan zaki da Alawus din taruka a watanni 3 da suka gabata

Gwamnoni sun kashe Naira Biliyan dari tara da sittin da takwas(968,000,000) wajan Shan kayan zaki da Alawus din taruka a watanni 3 da suka gabata

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Najeriya 30 sun kashe Naira biliyan dari tara da sittin da takwas, N986.64bn wajan shan kayan ruwa da alawus din taruka da tafiye-tafiye da sauransu. Watau dai wadannan kudade ba'a kashesu kai tsaye wajan yin wani aiki da zai amfani al'uma ba. An samo wadannan bayanai ne daga kundin tattara bayanan yanda gwamnati ke kashe kudaden kasa saidai babu bayanan jihohi 6, Benue, Imo, Niger, Rivers, Sokoto da kuma jihar Yobe. Bayanan sun nuna cewa jihohi 3 din sun kashe Naira Biliyan 5.1 wajan baiwa baki kayan ruwa watau lemu da ruwan sha da sauran kayan zaki. Sannan sun kashe Naira Biliyan 4.67 a matsayin Alawus ga ma'aikatan gwamnati. Jihohin sun kuma kashe Naira Biliyan 34.63 wajan tafiye-tafiye a cikin gida da kasashen waje hakanan kuma sun k...
‘Yan majalisar tarayya dake jam’iyyun Adawa sun nemi Gwamnati data biya ma’aikata Naira Dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi

‘Yan majalisar tarayya dake jam’iyyun Adawa sun nemi Gwamnati data biya ma’aikata Naira Dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
'Yan majalisar tarayya dake jam'iyyun Adawa irin su PDP, Labour party da sauransu, sun yi kiran cewa, ya kamata gwamnati ta biya ma'aikata Naira dubu 100 a matsayin mafi karancin Albashi. Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Punch. Yace a halin da ake yanzu, duk albashin da za'a biya dake kasa da Naira 298,000 ba zai kai ma'aikaci ko ina ba. Ya kara da cewa, kasa biyan albashin da zai ishi ma'ikata yin rayuwa me kyau, sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya ne.
Kungiyar Kwadago ta sauko daga dubu dari hudu(400,000) yanzu tace zata amince idan gwamnati ta biya dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Kungiyar Kwadago ta sauko daga dubu dari hudu(400,000) yanzu tace zata amince idan gwamnati ta biya dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
Kungiyar kwadago ta NLC ta dauko daga matsayinta na sai gwamnati ta biyata dubu dari hudu da casa'in da hudu(494,000) a matsayin mafi karancin Albashi. A yanzu kungiyar tace zata iya amincewa da dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi idan gwamnati zata iya biyan hakan. Hakan ya bayyana ne daga bakin wasu 'yan kungiyar wanda basuso a bayyana sunayensu ba. A zama na karshe dai da gwamnati ta yi da 'yan kwadagon ta ce zata biya Naira dubu sittin a matsayin mafi karancin albashi saidai kungiyar kwadagon tace bata amince ba. Labari na karshe dai shine wanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa ministan kudi, Wale Edun umarnin ya gabatar masa da sabin daftari na biyan ma'aikatan mafi karancin Albashi.
Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu

Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu

Siyasa
Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu. Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawar da tawagar ta yi da shugaban ƙasar a Aso Rock Villa, a ranar Talata.
Ba zamu amince da kari dan kadan ba akan Dubu 60>>NLC

Ba zamu amince da kari dan kadan ba akan Dubu 60>>NLC

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa, ba zata amince da kari dan kadan, wanda bai kai ya kawo ba akan Naira Dubu 60 ba. Kungiyar Kwadago ta NLC dai ta amince ta dakatar da yajin aikin da take dan bayar da dama ga gwamnati ta mata kari akan Naira Dubu 60 na mafi karancin Albashi. Shugaban kungiyar Kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana haka a wata ganawa da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Yace su basu nace wai sai an biyasu Naira Dubu dari hudu ba amma dai abinda suke cewa, shine a biyasu albashi me kyau.
Mun kunno wutar lantarki bayan janye yajin aiki – Ma’aikatan lantarki a Najeriya

Mun kunno wutar lantarki bayan janye yajin aiki – Ma’aikatan lantarki a Najeriya

Duk Labarai
Ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta ƙasa a Najeriya ta ce an sake kunna babban layin wutar da aka kashe bayan janye yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka yi.Shugaban ƙungiyar National Union of Electricity Employees (NUEE), Adebiyi Adeyeye, ya faɗa wa jaridar Punch cewa sun kunna layin ne bayan janye yajin aikin a safiyar yau."An janye yajin aiki kuma hakan yana nufin layin ya koma aiki yadda ya dace. An kunna shi tuni," in ji Mista Adeyeye.Sai dai har yanzu akasarin ƙasar na cikin duhu duk da wannan iƙirari da shugaban ya yi.Tun a jiya Litinin kamfanin kula da rarraba lantarki a Najeriya TCN ya ce mambobin ƙungiyar ƙwadago ne suka tilasta wa ma'aikatan lantarkin shiga yajin aikin ta hanyar kashe babban layin.
Hotuna da Bidiyo: Ya baiwa ‘yan mata 2, kawaye miliyan 1 su je yayi lalata dasu, saidai ya kash-she su ya yi tsafi dasu

Hotuna da Bidiyo: Ya baiwa ‘yan mata 2, kawaye miliyan 1 su je yayi lalata dasu, saidai ya kash-she su ya yi tsafi dasu

Tsaro
Wasu 'yan mata da suka dauki hankula a kwanannan su biyu kawayen juna sun je wajan wani mutum dan yin lalata. Saidai tin da suka tafi wajensa ba'a sake ganinsu ba. Hakan yasa aka yi kiyasin cewa sun bata. Saidai daga baya an gano mutumin inda aka kamashi. Amma ana kan hanyar da za'a kaishi ofoshin 'yansanda, sai ya yi kokarin tserewa wannan yasa 'yansandan suka kasheshi. An gano cewa, mutumin yana da alaka da wata kungiyar Asiri. Wasu karin bayanai da suka bayyana kan lamarin sun nuna cewa, mutumin ya baiwa 'yan matan Naira Miliyan daya ne dan su je yayi lalata dasu. Saidai ashe ajali ne yake kiransu. Labarin wadannan 'yan mata biyu dai sai ci gaba da kara daukar hankaki yake, domin kuwa zuwa yanzu an gano gawarwakinsu a kusa a gidan mutumin da ya gayya...