Muna ci gaba da kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace kuma zuwa yanzu mun kashe Naira Biliyan 29 a wajan gyaran>>Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin samar da wutar lantarki na kasa, TCN ta bayyana cewa zuwa yanzu ta kashe Naira Biliyan 29.3 a wajan gyaran wutar Lantarkin data lalace.
Karafunan wutar lantarkin 266 ne aka lalata a duka fadin Najeriya.
Ciki hadda wanda ya faru kwanannan wanda ya shafi wasu jihohin Arewa.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, Najeriya na tafka asarar Dala Biliyan 26 duk shekara saboda matsalar lalacewar wutar lantarki.
A baya dai irin wannan matsala ta faru a jihohin Abuja, Lagos, Kano, Enugu, Bauchi, Port Harcourt, da yankin Benin.