Tuesday, February 17
Shadow

Duk Labarai

Ofishin Jakadancin Ingila a Najeriya sun kaiwa Anthony Joshua ziyara a Asibitin da yake kwance

Ofishin Jakadancin Ingila a Najeriya sun kaiwa Anthony Joshua ziyara a Asibitin da yake kwance

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin jakadan kasar Ingila a Najeriya, Simon Field ya kai wa dan Damben Najeriya, Anthony Joshua ziyara a Asibitin da ya ke kwance a jihar Ogun bayan Hadarin da ya rutsa dashi. Sannan kuma ya gana da Gwamnonin Ogun, Dapo Abiodun dana Legas, Babajide Sonwo Olu kamar yanda me magana da yawun Gwamnan jihar Ogun,Kayode Akinmade ya bayyana. Yace suna bibiyar lamarin. A hukumance aka sanar da ofishin jakadancin kasar Ingila lamarin. Hakanan sauran wanda suka yi hadarin da Anthony Joshua suma an sanar da ofishin jakadancin kasashensu abinda ya faru.
Sai da na gargadi Anthony Joshua ya dana shigewa ‘yan Siyasar Najeriya, gashinan yanzu yaje yayi Hadari>>Inji Omoyele Sowore

Sai da na gargadi Anthony Joshua ya dana shigewa ‘yan Siyasar Najeriya, gashinan yanzu yaje yayi Hadari>>Inji Omoyele Sowore

Duk Labarai
Omoyele Sowore, dan Fafutuka kuma mamallakin Jaridar Sahara Reporters ya bayyana cewa, a baya yasha gargadin dan Damben Najeriya, Anthony Joshua kan ya daina shigewa 'yan siyasar Najeriya amma yaki. Yace gashinan yanzu ta fito fili, yayi hadari babu wani taimakon gaggawa na musamman da ya samu. Sowore yace shuwagabannin Najeriya cin hanci da rashawa ya musu yawa sannan kuma azzalumaine. A karshe yace yana taya AJ fatan Allah bashi Lafiya. https://twitter.com/sowore/status/2005896438425813219?t=XGLuxNIb8eJtHmye4dY_rA&s=19
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa zai tsaya takarar neman kujerar Sanata Natasha Hadiza Akpoti

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa zai tsaya takarar neman kujerar Sanata Natasha Hadiza Akpoti

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa, zai tsaya neman takarar sanata na kujerar da Sanata Natasha Akpoti ke kai. Ya bayyana hakane a fadar sarkin Ohinoyi dake Okene ranar 29 ga watan Disamba. Hakan ya kawo karshen rade-radin da ake kan cewa ko zai tsaya takarar ko kuwa. Yahya Bello dai na da case a EFCC inda suke Tuhumarsa kan zargin cinye wasu kudade har Biliyan 80 na jiharsa.
Kwankwaso da Sheik Isa Ali Pantami sun mika sakon jaje ga Anthony Joshua

Kwankwaso da Sheik Isa Ali Pantami sun mika sakon jaje ga Anthony Joshua

Duk Labarai
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da Sheikh Isa Ali Pantami duk sun aika sakon ta'aziyya ga dan Damben Najeriya, Anthony Joshua bayan da yayi Hadari. Sheikh Pantami yace yana mika sakon Jaje ga Anthony Joshua da iyalansa sannan yana mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/2005861959137145258?t=fl9bGYOHG6ZMOq5ksSCg7Q&s=19 Shima Kwankwaso ya nuna Alhini inda yayi fatan Allah ya baiwa Anthony Joshua lafiya. https://twitter.com/KwankwasoRM/status/2005708488199340207?t=ZhXdnfUTpZjYg7V3KAE6AA&s=19
Allah Sarki: Wannan Shine daya daga cikin abokan Dandamben Najeriya, Anthony Joshua da ya rasu a hadarin da suka yi Jiya

Allah Sarki: Wannan Shine daya daga cikin abokan Dandamben Najeriya, Anthony Joshua da ya rasu a hadarin da suka yi Jiya

Duk Labarai
Wannan da ake kira da Healthy Mindset daya daga cikin abokan dan damben Najeriya, Anthony Joshua ne da suka rasu a hadarin da ya rutsa dashi jiya Hadarin ya farune yayin da suke kan hanyar Legas zuwa Ibadan kuma abokansa 2 sun rasu shi kuma ya ji raunuka yana karbar magani. Healthy Mindset na daga cikin wadanda suka rasu kuma musulmi ne. A wannan Hoton an ganshi yana yiwa su Anthony Joshua Limanci. https://twitter.com/smile2jannah/status/2005718398173647173?t=tmes4ugW93GJiN_p8Oj_YQ&s=19 https://twitter.com/Alhamdhulillaah/status/2005682927980753396?t=Ty2WAB5FDILKBVFKsqxkVg&s=19
Allah Sarki: Wannan Fasto ne da ya karbi Shahada ranar Kirsimeti

Allah Sarki: Wannan Fasto ne da ya karbi Shahada ranar Kirsimeti

Duk Labarai
Wannan wani fasto ne Bayerabe da ya karbi Shahada Ranar Kirsimeti. Yace yana cikin karanta Baibul ne sai ya je inda yaga cewa Jesus yayi Sallah irin ta musulmai. Yace kuma yaga inda Jesus ya la'anci masu bauta ta hanyar rawa da waka, yace shine ya je ya nunawa faston dake gaba dashi. Amma sai yace masa wai kuskurene aka yi. Yace to shine yace waye yayi kuskuren, Jesus ne yayi kuskuren ko wanene? Shine fa ya fara neman yanda zai musulunta inda yace bari yaje wajan malaman Hausawa yasan sune ba zasu karbi kudi da yawa ba. Shine ya tambaya cewa nawa malaman Hausawa ke karba idan za'a shiga Musulunci? Aka ce masa kyautane shine ya musulunta. https://www.tiktok.com/@yusuf__t1/video/7588036613431741717?_t=ZS-92e4Qk61UlU&_r=1
Wata Sabuwa: Daya daga cikin manyan malaman Arewa ya nemi auren matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari

Wata Sabuwa: Daya daga cikin manyan malaman Arewa ya nemi auren matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin manyan malaman Arewa ya nemi auren matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari. Saidai tace masa bata so kuma ya kiyaye ta idan ba haka ba zata tona masa Asiri. Daya daga cikin malam ne ya tona wannan asiri. https://www.tiktok.com/@zaidou1taza/video/7589412053593459980?_t=ZS-92e3HqKAYxE&_r=1 A baya dai, Hajiya A'isha Buhari tace bata da niyyar yin aure bayan rasuwar Mijinta, tace zata ci gaba da rayuwa tsakanin 'ya'ya Da jikoki ne.