Yadda ake gyaran fuska da nescafe
Nescafe ko kuma nace Coffee na da matukar amfani sosai wajan gyaran fuska.
Wasu daga cikin abubuwan da Nescafé ko Coffee kewa fuska sun hada da:
Kawar da tattarewar fuska da alamun tsufa.
Maganin kurajen fuska.
Maganin fatar dake tattarewa karkashin ido.
Kawar da duhun fuska wanda dadewa a rana ke kawowa.
Yana sa hasken fuska.
Yana cire matacciyar fatar fuska.
Yana bada garkuwar kamuwa da cutar daji ta fata.
Yana kawar da tabon kurajen fuska, yana maganin kumburin fuska.
Yadda ake gyaran fuska da nescafe
Ana kwaba garin Nescafé da ruwa a shafa a fuska a bari yayi mintuna 15 zuwa 20 sai a wanke da ruwan dumi.
Domin kawar da tattarewar fatar kasan ido kuwa, Ana samun garin Nescafé a hada da man zaitun a kwaba, a shafa a kasan ido da sauran fuska a bari yay...