Monday, December 16
Shadow

Kiwon Lafiya

Amfanin kankana ga namiji

Amfanin Kankana
Kankana na daya daga cikin kayan marmari da ake amfani dasu a kasar Hausa, a wannan rubutun, zamu kawo muku jawabin amfanin Kankana ga Namiji. Kankana na taimakawa maza wajan lafiyar gabansu musamman maraina ga mazan da suka fara manyanta. Tana da sinadaran Antioxidant wanda ke boye alamun tsufa. Tana kara gudun jini a jikin mutum wanda hakan zai karawa namijin dake shanta karfin Azzakari. Masana sunce ga maza wanda suka manyanta wanda ke amfani da maganin karfin maza dan Azzakarin su ya tashi, zasu iya yin amfani da kankana a madadin shan wadannan magunguna. Kankana na taimakawa wajan samun ingantaccen bacci. Kankana na taimakawa maza wajan kara ingancin maniyyinsu. Kankana na taimakawa karin lafiya ga zuciya. Kankana na kuma da sinadaran dake yaki da cutar Daji w...

Amfanin waken suya a jikin mace

Amfanin Waken Suya
Waken suya na daya daga cikin manyan abinci a kasar Hausa inda ake abubuwa dashi da yawa kama daga Awara, madara, kai wasu ma na soyashi a rika ci kamar gyada. A wannan rubutu zamu bayyana amfanin waken suya a jikin mace. Waken suya na da amfani sosai musamman ga mace wadda ta fara manyanta, alamomin tsufa da kuma sakin jiki ba zasu bayyana sosai ba idan tana amfani da waken suya. Matan da suka kai matakin manyanta,sukan yi fama da zufar dare, yawan amfani da waken suya na magance wannan matsala. Hakanan ga matan dake son rage kiba, waken suya na taimakawa sosai a wannan bangaren. Hakanan yana taimakawa mata wajan rage matsalolin jinin al'ada. Wani bincike yace waken suya na taimakawa wajan garkuwa ga hana kamuwa da cutar dajin mama watau Breast cancer. Yana kuma taim...

Maganin yawan tusa

Kiwon Lafiya, Magunguna
Cin abincin dake da wahalar narkewa ko shan wasu kalar magunguna na sa a rika yin tusa da yawa. Yawanci dai Tusa na da alaka da kalar abincin da mutum ke ci ne ko kuma wata rashin lafiya. Wata tusar na da kara, wata bata da kara yayin da wata ke da wari wata kuma bata da wari, ko ma dai menene masana kiwon lafiya sun ce mafi yawan mutane sukan yi tusa sau 10 zuwa 20 a rana. Mafi yawan abincin dake kawo Tusa sun hada da Wake ko ganye wanda ba'a dafa ba, irin su latas, da shan madara, lemun kwalba, Alkama da sauransu. Sauran abubuwan dake kawo yawan tusa sun hada da shan Alewa,shan taba, shan giya,shiga yanayi na matsi ko damuwa, Yin tusa ba matsala bane amma idan ta yawaita tana iya zama illa ga mai yinta. Ana iya samun waraka daga yawan tusa ta hanyar canja kalar abincin da...

Yadda ake gane mace mai ni’ima tun kafin aure

Auratayya, Ilimi, Jima'i, Nishadi
Mafi yawancin lafiyayyun mata na da ni'ima inda wasu kuma rashin lafiya ko rashin wadata da kwanciyar hankali da samun cima me kyau ke hanasu samun ni'ima. Ni'ima a wajan mace ta hada abubuwa da yawa, ba kawai tana nufin dadin farjin mace bane ko kuma ruwan dake gabanta ba. Tabbas Ruwan dake gaban mace shine jagora a wajan ni'imarta amma ba shi kadai bane. Ni'ima a tattare da mace ta hada da: Surar jikinta. Laushin fata. Nonuwa masu daukar hankali. Mazaunai masu daukar hankali. Murya. Da kuma iya soyayya. Ruwan gaba. Iya Kwanciyar aure. Gashi. Kwalliya. Macen data hada wadannan abubuwa tabbas tana da ni'ima kuma mijinta zai ji dadin tarayya da ita sosai. Surar jiki halittace daga Allah, wadda wata zaka ganta tsayuwarta kawai ko tafiyarta na da d...

Gyaran nono lokacin yaye

Nono
A yayin da jaririnki ya daina shan nono kika yayeshi. Nononki zai iya daukar kusan kwanaki 5 zuwa 10 yana dan kumburi nan da can, hakan ba matsala bane,duk da ba kowace mace ce ke fuskantar wannan matsala ba. Idan hakan ya faru dake, zaki iya rika yiwa nonon naki tausa sannan zaki iya rika matso ruwan nonon kadan-kadan. Hakanan ga wanda nonuwan ke zafi bayan kammala shayarwa, ana iya rika dira ruwan sanyi ko a nade kankara a tsumma me kyau a rika dorawa akan nonon. Yana da kyau kuma a rika shan ruwa ko abinda ya danganci riwa. Ana iya shan magungunan rage radadin ciwo irin su Ibuprofen. Sannan maganar gyaran nono ya koma kamar yanda yake kamin ki dauki ciki kuwa, daya daga cikin hanyoyin da ake samun nasarar hakan shine ta hanyar motsa jiki. An fi son motsa jikin da zai ...

Gyaran nono da man kadanya

Amfanin Man Kadanya, Nono
Wasu bayanai sun nuna cewa man kadanya yana sanya nonon mace ya kara cikowa kuma ya mike sosai ko ya tashi tsayen, haka kuma a wani kaulin yana maida tsohuwa yarinya. Watau yana hana fatar nonon tsufa da wuri. Akwai hanyoyi biyu da wasu bayanai na gargajiya sukace ana amfani dasu wajan gyaran nono da man kadanya. Na farko shine, ana hadashi da man wanke baki watau Makilin a shafa akan nono zuwa wani lokaci a wanke. A bayani na biyu kuma, an samo cewa ana samun man kadanya ko man kade shi kadai a rika shafashi akan nono a hankali kamar ana mai tausa. Saidai duka wadannan bayanai basu da inganci a wajan likitoci, hanyoyi ne na gargajiya na gyaran nono a gida. Abinda ya tabbata shine, idan nononki na kaikayi, zaki iya shafa man kade, yana maganin kaikayin nono da kaikayin ka...

Gyaran nono da makilin

Nono
Ki nemi:-1-man kadanya2-man wanke baki(makilin) Za ki tautausa gefen nononki na kamar minti goma hakan yana bawa jijiyoyin jini damar kawo sinadarin (estrogen wanda yake sa nono girma, sai ki shafa man kadanyar a nonon ki shafa sosai daga sama zuwa kasa ta gefe yadda zai samu damar shiga fatar, sai ki sa man wanke bakin wato makilin akan tsinin nonon, in gari ya waye da safe sai ki wanke.Za ki Yi mamaki cikin sati biyu Insha Allah. DON MATAN AURE DA 'YAMMATAGYARAN NONO! Nono! (Breast) wani bangare ne mai matukar muhimmanci a jikin 'ya mace wanda ke kara mata kwarjini,kima da kuma ado ba ga namiji ba kad'ai harma a cikin 'yan uwanta mata,nono ya kasance wani guri da yafi ko ina jan hankalin tare da tayar da sha,awar da namiji a jikin mace.Binciken masana ya nuna cewa nono na iya ka...

Girman nono da hulba

Nono
YADDA ZA'A KARA GIRMAN NONO KUMA YA TASHI TSAYEDA IZNIN ALLAH ASAMO WADANNAN ABUBUWAN KAMARHAKA:1.Hulba2.ruwan inabi ko yayansa, 3.Albabunaj 30gm 4.nono 50mg..Sai kuma a hada *hulba* da Albabunaj atafasa da ruwa rabin lita bayan antafasa sai kuma azuba ruwan inabin acikida wannan nonan idan ana bukatar zuma sai asanya arika sha..Saikuma a hada ambar da man hulba arika shafawa anonan da yamma kafin ankwanta, amma da sharadin kada ashafa na shafawan idan anayin jinin alada..(2)-Ko kuma ita Hulba za'a samu a tafasa ki rinka gasa nono da shi ,sai kuma a shafa man hulba ko kuma aTafasa yayan hulba anasha yana kara girman nono.Sannan Idan akasami ruwan sanyi a kasanya masa gishiri kadan ana wanke nono dashi yana hana lalacewar nono..(3)-Dangane da tsayuwar nono kuma sai asamo alkama, da hulba, d...

Amfanin rigar nono ga budurwa

Nono
Akwai amfani da yawa ga budurwa ta rika saka rigar nono. A wannan rubutu, zamu bayyana wadannan amfani. Na 1. Rigar Nono na hana zubewar nono: Nono yakan tsaya da kansa ko da ba'a tareshi ba amma yana da kyau budurwa ta rika saka rigar nono dan yana taimakawa wajan hana zubewar nonon. A wani kaulin, an fi son budurwa ta saka rigar nono yayin da take aikin jijjiga jiki,amma a yayin da take zaune bata aikin komai, zai fi kyau kada ta saka rigar nonon. Na 2. Rigar Nono na taimakawa budurwa wajan jin dadin jikinta da kuma bayyanar surarta da kyau. Musamman mata masu girman nono,Rigar Nono zata taimaka musu sosai wajan tsaida nonuwan yanda ya kamata. Na 3. Yana karawa mace jin dadin jikinta da Alfahari da kanta. Mace zata samu nutsuwa sosai idan ta saka rigar nono. Na 4. Kare mutunc...

Sirrin tsayuwar nono ga budurwa

Nono
Mafi yawanci budurwa tana tasowa ne da nonuwanta a tsaye. Amma wsu dalilai sukan sa nonuwan su kwanta. Saidai budurwa ta sani cewa, idan tana da karancin shekaru, misali, daga 10 zuwa 15 nonuwanta basu gama girma ba, dan haka kada ta damu kanta da tsayuwar nonuwa ko karin girmansu. Ta dakata tukuna har sai jikinta ya kammala girma, nonuwan sun kammala fitowa gaba daya. Mafi yawan lokuta Nonuwan mace suna gama girma ne idan ta kai shekaru 18, saidai wasu matan nonuwansu na kara fitowa waje su kara girma har zuwa su kai shekaru 20 zuwa 25. dan haka idan mace tana tsakanin shekaru 10 zuwa 20 ko 25 kada ta yi gaggawar nemanaganin kara girman nono, ta jira tukuna ta ga nonuwan nata su gama girma. Kuma a sani mafi yawanci mata suna gadon girman nono ne a wajen iyayensu, idan mahai...