Wednesday, January 15
Shadow

Gyaran nono su tsaya

Nono
Akwai hanyoyin gyaran nono da yawa, a wannan rubutu zamu yi maganane akan yanda zaki gyara nonuwanki su tsaya. Saidai kamin mu fara bayani,bari mu gaya muku abubuwan da a likitance aka tabbatar suna sanya nonuwa su zube. Shekaru: Idan mace shekarunta suka fara ja, nonuwanta zasu zube. Rashin Kuzari: Idan na fama da rashin kuzari wanda yawanci ke samo asali daga rashin samun ingantaccen abinci me gina jiki shima yana sanya nonuwa su zube. Rashin Sha'awa: Idan ya zamana mace bata da sha'awa ta jima'i ko sha'awarta ta yi kasa sosai, bata damu da jima'iba, hakan yana iya kaiwa ga zubewar nono. Abinda ke jawo hakan shine yawanci rashin cin abinci me gina jiki da kuma rashin samun nutsuwa da aikin karfi. Gravity: Yanayi ne da babu yanda mace zata yi indai tana raye sai nonuwant...
Hukumar NCC ta gano mutum 1 me layukan waya dubu dari(100,000) a Najeriya

Hukumar NCC ta gano mutum 1 me layukan waya dubu dari(100,000) a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar kula da sadarwa,NCC ta bayyana cewa ta gano wani mutum 1 wanda ke da layukan waya dubu dari (100,000) shi kadaai. Wakilin Hukumar, Reuben Muoka ne ya bayyana hakan inda ya jaddada cewa ranar 14 ga watan Satumba me zuwa ne rana ta karshe ga kowa ya hada layinsa da lambar NIN. Yace suna aiki ne tare da ofishin Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu dan dakile barazanar tsaro. Sannan yace suna aiki tukuru dan hana sayar da layukan wayar da aka riga aka musu rijista.
Abin a Yaba: Ya tsinki Dala $10,000 kwatankwacin Naira Miliyan 15 a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ya mayarwa mesu

Abin a Yaba: Ya tsinki Dala $10,000 kwatankwacin Naira Miliyan 15 a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ya mayarwa mesu

Duk Labarai
Wani ma'aikacin filin jirgin sama a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano me suna Auwalu Ahmed Dankade ya tsinci dala $10,000 kwatankwacin Naira Miliyan 15 amma ya mayar da ita ga maishi. Auwalu Ahmed Dankade yanawa wani kamfanin kula da karbar sako aiki ne a filin jirgin saman kjma a hirarsa da Daily Trust ya bayyana cewa iyayensa sun masa tarbiyyar kada ya dauki duk wani abu da ba nashi ba, ya wadata da abinda Allah ya bashi. Kamfanin da yakewa aiki dake Legas,ya gayyaceshi zuwa Legas din inda ake tsammanin za'a girmamashi ne.
Mun baku wata daya ku sauko da farashin kayan abinci ko mu daureku>>Gwamnatin Tarayya ga ‘yan kasuwa

Mun baku wata daya ku sauko da farashin kayan abinci ko mu daureku>>Gwamnatin Tarayya ga ‘yan kasuwa

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar dake kula da tsaftar gasa a kasuwanci da kiyaye hakkokin masu sayen kaya, FCCPC ta baiwa 'yan kasuwa wata daya su karya farashin kayansu ko su dandana kudarsu. sabon shugaban hukumar, Mr. Tunji Bello ne ya bayyana haka a wajan wani taro na masu ruwa da tsaki ranar Alhamis daya gudana a Abuja. Yace bayar da misalin wani lemu da ake sayarwa a kasar amurka akan $89 wadda yace kwatankwacin Naira 140,000 ne amma a wani babban shagon sayayya dake Legas sun ga ana sayar da lemun akan Naira 944,999. Yace wannan yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ne wanda kuma ba zasu lamunta ba. Yace duk wanda aka kama akan wannan laifi zai iya fuskantar tara me yawa ko kuma dauri.
Ji Martanin da Hadiza Gabon tawa wani da yace mata ta bashi kudi

Ji Martanin da Hadiza Gabon tawa wani da yace mata ta bashi kudi

Duk Labarai, Hadiza Gabon
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta wallafa wannan hoton nata a shafinta na sada zumunta inda masoyanya suka rika yabawa. Saidai wani ya roketa da ta yiwa mutane kyautar kudi kamar yanda dan siyasa na jihar Kaduna,Bello ElRufai ke yi. Saidai Hadizar ta mai martanin cewa, ya je ya samu aikin yi. Ya dai mayar mata da martanin cewa, ko ya kawo takardunsa ta bashi aiki a dakin hada shirye-shiryenta na Youtube? Daga nan dai Hadizar bata sake takashi ba. A baya dai, Abokiyar aikin Hadizar, Rahama Sadau ta rabawa masoyanta kudade ta shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram.