Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a wani hari kan bututun mai a Nijar
Wasu ƴan bindiga sun kai wa wata tawagar sojoji da ke sintirin aikin sa ido kan bututun man fetur a garin Tibiri da ke yankin Dosso a kudu maso yammacin Nijar harin kwantan ɓauna inda suka kashe sojoji akalla shida.
Rahoton wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta ya kara da cewa soja ɗaya ya ɓata sannan an lalata motoci biyu a harin.
Rahoton bai bayyana ko an samu asarar rai a ɓangaren ƴan bindigar ba, ko kuma bayyana alakarsu da wasu ƙungiyoyi.
Ƴan bindiga dai sun kasance suna gudanar da ayyukansu a wasu sassan Nijar da ke kan iyaka da arewa maso yammacin Najeriya.
Har yanzu dai rundunar sojin ƙasar ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba.
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, al'amuran tsaron ƙasar Nijar ke ƙara taɓarɓarewa, inda a lokuta da dama ...