Saturday, March 28
Shadow
Kalli Bidiyon: Ta karbi Tallafin Abinci na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tace zata ci amma ba zata zabeshi ba

Kalli Bidiyon: Ta karbi Tallafin Abinci na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tace zata ci amma ba zata zabeshi ba

Duk Labarai
Wannan matar data karbi tallafin Gwamnatin tarayya da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke rabawa na Renew Hope Agenda tace zata ci amma ba zata zabeshi ba. Tace dalilinta shine, wannan abinci dama hakkintane a matsayinta na 'yar kasa. Tace dan haka zata ci amma ba zata sabi shugaban kasar ba. Ta bude kwalin inda ta nuna abubuwan dake ciki. https://twitter.com/i/status/2032179899788570761
Kalli Bidiyon: Kirista Dalibar Kadpoly dake Kaduna ta koka da cewa, ana takura musu sai sun rufe jikinsu kamin su shiga makaranta saboda Musulmai na Azumi

Kalli Bidiyon: Kirista Dalibar Kadpoly dake Kaduna ta koka da cewa, ana takura musu sai sun rufe jikinsu kamin su shiga makaranta saboda Musulmai na Azumi

Duk Labarai
Wata Kirista Dalibar Jami'ar Kaduna Polytechnic dake Kaduna ta koka da cewa ba'a musu Adalci inda tace sun saka kaya basu nuna komai na tsiraici ba amma an hanasu shiga makaranta. Ta koka da cewa, Ana tilasta musu rufe jikine saboda musulmai dake Azumin watan Ramadana. Tace wannan ba adalci bane. Dalibar ta bayyana hakane a Bidiyon data yi a kofar makarantar bayan da aka hanasu shiga inda ta yi kira ga hukumomin makarantar su dauki mataki. https://twitter.com/i/status/2032145110322827750
Kalli Bidiyon: Wannan matar ta dauki hankali saboda cewa duk wanda baya son Tinubu ya zarce Allah yass ya rigamu gidan gaskiya kamin 2027

Kalli Bidiyon: Wannan matar ta dauki hankali saboda cewa duk wanda baya son Tinubu ya zarce Allah yass ya rigamu gidan gaskiya kamin 2027

Duk Labarai
Wannan wata mata ce da aka baiwa tallafin Gwamnatin tarayya na Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na kayan Azumi. Bayan karbar kayan, ta yi fatan cewa, duk wanda baya son shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce a shekarar 2027 Allah yasa ya rasu. https://www.tiktok.com/@olagucci1994/video/7616033699506834709?_r=1&_t=ZS-94cbuNMNdfl Saidai da yawa sun yi Allah wadai da hakan inda wasu ke tambayar duk kwana nawa abincin zai mata?
Matarnan data zargi Ministan ayyuka David Umahi da neman suyi soyayya duk da yasa tana da aure ta fito ta yi karin haske

Matarnan data zargi Ministan ayyuka David Umahi da neman suyi soyayya duk da yasa tana da aure ta fito ta yi karin haske

Duk Labarai
Tracy Ohiri, matarnan data zargi Ministan ayyuka, David Umahi da neman ta su yi soyayya duk da yasan cewa ita matar aure ce ta fito ta karyata kanta. Tace a yi hakuri abinda ta fada ba haka yake ba ko kuma an mata mummunar fassara ne. Tace bayan ganawa da danginta da lauyanta, ta yanke shawarar mantawa da wannan magana ta ci gaba da rayuwarta. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo data wallafa. A baya dai ta bayyana cewa, abinda ya kawo wannan rikici tsakaninsu, aiki ne tawa Ministan amma yaki biyanta hakkinta. https://www.youtube.com/watch?v=GHsjquvtlGU?si=FOC0GU1mAVyntD0e Saidai wasu na zargin cewa barzana aka mata ko kuma kudi aka bata ta janye wannan kalamai nata