Friday, December 5
Shadow
Gwamnatin Kano na neman a kama Ganduje, saboda yunkurin kafa kungiyar tsaro ta sa kai

Gwamnatin Kano na neman a kama Ganduje, saboda yunkurin kafa kungiyar tsaro ta sa kai

Duk Labarai
Majalisar zartaswar jihar Kano ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike tare da kama tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa wasu kalamai da ta bayyana a matsayin tsokana da kuma tada zaune tsaye kan matsalar tsaro a jihar. Hakan ya biyo bayan tattaunawa ne a taron majalisar zartarwa karo na 34 da aka gudanar a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar Kano, inda ƴan majalisar suka yi nazari kan kalaman Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin na baya-bayan nan, inda suka yi zargin cewa Kano na kara fuskantar matsalar ƴan fashi da kuma bayyana shirin ɗaukar mutane 12,000 aikin ƴan sandan rundunar tsaro mai suna Khairul Nas. Da yake yiwa manema labarai ƙarin haske game da sakamakon taron a ranar Juma’a, kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim...
Kirista Grace ta ce Kalaman Baffa Hotoro akan Sheikh Dahiru Usman Bauchi basu kamata ba

Kirista Grace ta ce Kalaman Baffa Hotoro akan Sheikh Dahiru Usman Bauchi basu kamata ba

Duk Labarai
Wata Kirista Grace Charles ta bayyana rashin jin dadin kalaman da Baffa Hotoro yayi akan Marigayi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Tace kalaman basu dace ba lura da cewa, Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu. Tace duk me bin Baffa Hotoro ba zai shiga Aljannah ba https://www.tiktok.com/@gracecharles792/video/7577801632377769224?_t=ZS-91mosZIAbVB&_r=1 Baffa Hotoro na daga cikin malaman da suka soki Dahiru Usman Bauchi duk da ya rasu wanda wasu ke ganin hakan bai dace ba.
Ji ta’asar da zaratan Tshàgyèràn Dhàjì 3 sukawa wata karamar yarinya a jihar Naija

Ji ta’asar da zaratan Tshàgyèràn Dhàjì 3 sukawa wata karamar yarinya a jihar Naija

Duk Labarai
Wasu 'yan Bindiga 3 sun yiwa karamar yarinya me shekaru 13 fyàdè a kauyen Kudodo dake yankin Galko na karamar hukumar Shiroro jihat Naija. Wani dan jam'iyyar APC a jihar Naija, Babangida Wassa Kudodo ne ya bayyana hakan. Yace lamarin ya nuna irin yanda rashin tsaro ke kara munana a jihar. Tuni aka kai yarinyar Asibiti dan kula da lafiyarta. Jihar Naija na daga cikin jihohin Arewa masu fama da matsananciyar matsalar tsaro.
Doka ta bayar da dama idan Gwamnati ta gaza, ‘yan Najeriya zasu iya neman taimakon kasashen Duniya game da harkar tsaro>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Doka ta bayar da dama idan Gwamnati ta gaza, ‘yan Najeriya zasu iya neman taimakon kasashen Duniya game da harkar tsaro>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Doka ta bayar da dama idan Gwamnatin tarayya ta gaza, 'yan Najeriya zasu iya neman dauki daga kasashen waje kan matsalar tsaro. Obasanjo yace a lokacin da yayi mulki yasan cewa, Najeriya na da karfin da zata iya magance matsalar tsaro. Yayi kira ga Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu da ta tashi tsaye ta magance matsalar dake ci gaba da ruruwa a sassa daban-daban na kasarnan. https://twitter.com/SaharaReporters/status/1994506045570298037?t=2HQSwJzNtNfBOmSza4elHQ&s=19
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Kalli Bidiyon yanda ya Afkàwà wannan baiwar Allahn tana tsàkà da Sallah ya aìkàtà Alfàshà da ità

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Kalli Bidiyon yanda ya Afkàwà wannan baiwar Allahn tana tsàkà da Sallah ya aìkàtà Alfàshà da ità

Duk Labarai
Wani matashi me suna Muhamad Adam Haiqal Abdullah dan kimanin shekaru 19 dan kasar Malaysia kenan a wannan Bidiyon inda ya afkawa wata mata tana tsaka da Sallah. Ya tsaya sai da ta yi sujada sannan ya afka mata ya mata Fyàdè inda aka ganshi ya rufe fuskarsa. Saidai bai sani ba ashe kyamarar CCTV na daukarsa. https://twitter.com/KieraDiss/status/1994389984565137859?t=UPoIk7q_89ShT9NlWc0wWg&s=19 An kamashi inda da farko ya amsa laifinsa amma daga baya yace bai aikata ba. Alkali yace a kaishi a mai gwajin lafiyar kwakwalwa, zuwa yanzu dai ba'a san hukuncin karshe da aka yanke masa ba.
Kalli Bidiyon gwanin ban Tausai Yayi Mùmmùnàn Khàdàrìn mòtà a Abuja yayin da yake sauri ya kai mahaifinsa da bashi da lafiya Asibiti

Kalli Bidiyon gwanin ban Tausai Yayi Mùmmùnàn Khàdàrìn mòtà a Abuja yayin da yake sauri ya kai mahaifinsa da bashi da lafiya Asibiti

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum ya yi mummunan hadarin mota a Abuja. Ya iske wata babbar mota ce ta daki bayanta. Kuma nan take ya rigamu gidan gaskiya. Yana sauri ne ya kai mahaifinsa da bashi da lafiya Asibiti yayin da hatsarin ya rutsa dashi. Wasu shaidun gani da ido sun ce yana tsaka da yin wayane yana tuki yayin da hadarin ya faru. https://twitter.com/abujastreets/status/1994370300226703500?t=mwKKj3k4W83S1v4Ym37kJA&s=19
Kalli An Gano Mawakin Najeriya Davido yayi amfani da hoton karya dan ya burge masoyansa

Kalli An Gano Mawakin Najeriya Davido yayi amfani da hoton karya dan ya burge masoyansa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraron Mawakin Najeriya, Davido yayi amfani da wani hoto a shafinsa na X. Hoton na dauke ne da abinci me kyan gani. Saidai an gano hoton ba nashi bane a Google ya dakkoshi. Bayan gano hakan an rika masa tsiya ana cewa bai kamata yawa masoyansa karya ba. https://twitter.com/MachalaDoctor/status/1994362469356060938?t=DYs3YB1pbsHW_19I4O_Jhw&s=19
Tshàgyèràn Dhàjì da suka dàukì daliban jihar Kebbi, tserewa suka yi da suka ga jami’an saro, ba’a biya kudin Fànsà ba>>Inji Majalisar Dattijai

Tshàgyèràn Dhàjì da suka dàukì daliban jihar Kebbi, tserewa suka yi da suka ga jami’an saro, ba’a biya kudin Fànsà ba>>Inji Majalisar Dattijai

Duk Labarai
Majalisar Dattijai ta bayyana cewa, 'yan Bindiga da suka yi garkuwa da daliban makarantar MAGA dake jihar Kebbi, tserewa suka yi da suka ga jami'an tsaro. Me magana da yawun majalisar, Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai. Yace ba'a biya kudin fansa ba kamar yanda ake yamadidi. Yace kuma wai dan ba'a ga an kama kowa ba ko ba'a ga gawar wadanda suka yi garkuwa dasu din ba, hakan ba yana nufin ba'a yi fadan ba. Yace sannan kuma Ba dole bane sai jami'an tsaro sun sanar da yanda suka kubutar da daliban ba, kawai dai ana son a kubutar dasu kuma an kubutar dasu din.