Friday, December 5
Shadow
Kalli Bidiyon: Me magana da yawun Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana wata babbar Karama ta malamin

Kalli Bidiyon: Me magana da yawun Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana wata babbar Karama ta malamin

Duk Labarai
Me magana da yawun Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Daha Al'Azhari ya bayyana cewa, malam ya bayyana musu sanda zai bar Duniya tun yana raye. Yace ya gaya musu hakane tun kusan shekaru 10 da suka gabata. Ya bayyana cewa malam ya bayyana musu cewa ba zai zarta shekaru 102 a Duniya ba. Yace kuma hakan ta tabbata inda yace watanni kadanne suka rage bai karasa hakan ba. Yace wannan ba karamar karama bace. https://www.tiktok.com/@sus__ride/video/7577694759100091656?_t=ZS-91mGaufAxOL&_r=1
Kalli Bidiyon: Idan Dan Bidi’a ya rigamu gidan gaskiya, ba’a cewa, Allah ya jikansa, saidai Sannunmu dai>>Inji Malam Ibrahim Matayassara

Kalli Bidiyon: Idan Dan Bidi’a ya rigamu gidan gaskiya, ba’a cewa, Allah ya jikansa, saidai Sannunmu dai>>Inji Malam Ibrahim Matayassara

Duk Labarai
Dalibin Marigayi, Dr. Idris Dutsen Tanshi, Malam Ibrahim Matayassara ya bayyana cewa, ba'a wa dan bidi'a Addu'a idan ya rasu. Malamin ya bayyana cewa saidai ace sannun mu dai. Ya soki Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami saboda yin ta'aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Ya kira Malam Pantami da Munafiki inda yace ba zai samu kujerar siyasar da yake nema ba. https://www.tiktok.com/@officialmustymodawa/video/7577651549132819719?_t=ZS-91mAOPyU25Y&_r=1
Kalli Bidiyon: Yanzu ace duk Sokoto ba gidan haya me Arha sai sama da Naira Miliyan 1, ta yaya samari zasu yi aure?

Kalli Bidiyon: Yanzu ace duk Sokoto ba gidan haya me Arha sai sama da Naira Miliyan 1, ta yaya samari zasu yi aure?

Duk Labarai
Wata matashiya daga jihar Sokoto ta yi Allah wadai da masu gidajen haya saboda tsadar da gidajen hayar suka yi. Tace matasa basa iya yin aure saboda tsadar gidajen haya a Sokoto inda tace gidan haya sai daga Naira Miliyan 1 zuwa sama. Ta ce hakan yasa 'ya'yan talakawa da yawa sun koma Mazinata inda tace dan haka in Allah ya yarda masu gidajen haya suma sai 'ya'yansu sun koma mazinata. https://www.tiktok.com/@safrat.muhammad.h/video/7577449793216089352?_t=ZS-91m8feL96yf&_r=1
Kalli Bidiyo: Allah Sarki, Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta taba Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami sosai

Kalli Bidiyo: Allah Sarki, Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta taba Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami sosai

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya tabu sosai da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Bayan Wallafa sakon ta'aziyya da yayi, ya kuma wallafa wani tsohon Bidiyon da suke tare da Dahiru Bauchi inda yaje gaisheshi. A yau ne dai bayan Sallar Juma'a ake sa ran yiwa gawar Marigayin Sutura a kaishi makwancinsa. https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/1994113635749429565?t=ByzUyOljGKR-diBRuGR2uA&s=19
Da Duminsa: Shugaban Amurka, Donald Trump yace zai hana duk kasashe Matalauta irin su Najeriya, Ghana, Nijar da sauransu zuwa Amirka ci rani

Da Duminsa: Shugaban Amurka, Donald Trump yace zai hana duk kasashe Matalauta irin su Najeriya, Ghana, Nijar da sauransu zuwa Amirka ci rani

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta hana 'yan kasashe Matalauta zuwa kasar Amurka cirani. Yace wannan hanin zai yi shine na dindindin. Ya bayyana hakane Ranar Alhamis a wani sako da ya fitar na shirin bukukuwan karshen shekara. Shugaba Donald Trump na daga cikin tsarinsa na hana baki shiga kasar Amurka.
Kalli Bidiyon: Ni dai Billahillazi ko nawa za’a biyani ba zan iya aikin soja ba, saboda banso a Shyekye ni a irin wannan hanyar>>Inji Sanata Ali Ndume

Kalli Bidiyon: Ni dai Billahillazi ko nawa za’a biyani ba zan iya aikin soja ba, saboda banso a Shyekye ni a irin wannan hanyar>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya bayyana cewa, shi ko nawa za'a biyashi ba zai iya aikin soja ba. Yace dalili kuwa shine ba ya son ya mutu a irin wannan hayar ba saboda ko ya mutu babu wanda zai san darajarsa. Ya bayar da misalin cewa, yanzu ga gawar Janar can watau(Brigadier Mohammed Uba) a daji har yanzu ba'a dawo da ita ba. https://twitter.com/channelstv/status/1994113706431496508?t=qyEyfHxF69l_yfczxx6Now&s=19
Maganar janye ‘Yansanda daga baiwa manyan mutane tsaro ba gudu ba ja da baya, Babu wanu Gwamna ki Minista da zan saurara saboda umarnin shugaban kasa ne>>Inji IGP Kayode Egbetokun

Maganar janye ‘Yansanda daga baiwa manyan mutane tsaro ba gudu ba ja da baya, Babu wanu Gwamna ki Minista da zan saurara saboda umarnin shugaban kasa ne>>Inji IGP Kayode Egbetokun

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa maganar janye 'yansanda daga baiwa manyan mutane tsaro abune wanda ba gudu ba ja da baya. Ya bayyana hakane a wata ganawa da manema labarai da yayi. Yace dama can suna haka amma tunda yanzu Umarni ya zo daga wajan shugaban kasa, babu wani Minista ko Gwamna da zai kirashi da sunan neman Alfarma. Yace ya ga ana ta yada wani labari wai akwai 'yansanda 130,000 dake baiwa manyan mutane tsaro a fadin Najeriya, yace ba gaskiya bane hakan. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1994070671362503142?t=bnMol8AgIrTz6aIacQM8YA&s=19
Ba Daidai bane ace an yankewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai ba amma wasu masu laifi irin nasa an yanke musu hukuncin daurin shekaru 20 ba>>Inji Bello El-Rufai

Ba Daidai bane ace an yankewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai ba amma wasu masu laifi irin nasa an yanke musu hukuncin daurin shekaru 20 ba>>Inji Bello El-Rufai

Duk Labarai
Dan majalisar Wakilai daga jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana rashin dacewar yankewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai amma kuma aka yankewa wasu a ake zargi da aikata tà'àddànci hukuncin daurin shakeru 20. Ya bayyana hakane a zaman Majalisar inda yake kawo muhimmancin samar da tsaro mazabu. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1994119629862826242?t=rF4RLikI_Qn5E0GffBNhyg&s=19