Friday, December 5
Shadow
Kalli Bidiyon: Ina Kira Ga ‘yan Izala da su fito su nesanta kansu da masu fadar kalaman da basu dace ba akan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi >>Inji Digital Imam

Kalli Bidiyon: Ina Kira Ga ‘yan Izala da su fito su nesanta kansu da masu fadar kalaman da basu dace ba akan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi >>Inji Digital Imam

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Digital Imam ya bayyana cewa, yana kira ga malaman Izala da su fito su barranta da masu fadar kalaman sa basu dace ba akan Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Yace yin Shiru kamar yadda da abinda masu zagin ke yi ne. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7577495912365182229?_t=ZS-91lD6xeBYum&_r=1
Kalli Bidiyon: Shin wai ina Kunyar mu take ne? Ji yanda mata kewa halittar Bilal Villa ba’a bayan ganinsa da gajeren wando

Kalli Bidiyon: Shin wai ina Kunyar mu take ne? Ji yanda mata kewa halittar Bilal Villa ba’a bayan ganinsa da gajeren wando

Duk Labarai
Matashin Mawakin Arewa, Bilal Villa ya wallafa wani Bidiyo inda aka ganshi sanye da gajeren Wando. A Bidiyon an ga yana saka kaya da daya-daya har ya kammala saka kayan gaba daya. Lamarin ya dauki hankula sosai inda musamman mata suka rikawa Al'aurarsa ba'a. Wata tace ta ganta kamar ta yara wata kuma tace ta ganta kamar Charbin malam da sauransu. https://www.tiktok.com/@bilalvillah/video/7576449008571387147?_t=ZS-91l92aI3L96&_r=1
Sheikh Ɗahiru Bauchi dattijo ne mai son zaman lafiya – Kwankwanso

Sheikh Ɗahiru Bauchi dattijo ne mai son zaman lafiya – Kwankwanso

Duk Labarai
Tshon ɗan takarar shugaban Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jimaminsa tare a miƙa ta'aziyya ga iyalai da ƴanuwan da makusantan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi bisa rasuwar malamin. Kwankwaso ya bayyana malamin a matsayin uba, kuma babban malami wanda koyarsa ta zama madubi ga ɗimbin al'umma. "Ta hanyar karantarwa, Sheikh Ɗahiru taɓa rayuwar al'umma da dama tare da jan hankalinsu wajen koyi da halaye masu kyau da kuma ƙaunar Alqur'ani da sunnar manzon Allah." Kwankwaso ya ce shehin mutum ne mai son zaman lafiya kuma dattijo mai ƙoƙarin haɗa kan ƴan ƙasa, "wanda kuma ba za mu manta da shi ba, kuma ƙasarmu ba za ta manta da shi." "A madadin iyalina da ni kaina, ina miƙa ta'aziya da iyalansa da ɗalibansa da gwamnati da al'ummar Bauchi bisa wannan rasuwa. Allah ya saka sh...
Duk Da rokon da ‘yan majalisar Tarayya suka wa shugaba Tinubu kar a janye, Hukumar ‘yansandan Najeriya ta janye ‘yansanda dubu sha daya masu Baiwa manyan mutane kariya a Najeriya

Duk Da rokon da ‘yan majalisar Tarayya suka wa shugaba Tinubu kar a janye, Hukumar ‘yansandan Najeriya ta janye ‘yansanda dubu sha daya masu Baiwa manyan mutane kariya a Najeriya

Duk Labarai
Sufeto Janar na 'Yansandan Najeriya Olukayode Egbetokun ya ce sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP. Yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, IG Egbetokun ya ce zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Najeriya. "Wannan karon za muj aiwatar da umarnin da kyau saboda umarnin shugaban ƙasa ne," in ji shi. "Babu wani gwamna, ko minista, ko abokaina da za su kira su takura min saboda sun san cewa umarnin shugaban ƙasa ne. Ina da tabbacin ba za su uzura wa kwamashinonin 'yansanda ba ma." Ya ƙara da cewa za su tura jami'an da aka janye zuwa "wuraren da aka fi buƙatarsu, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci".
Shugaba Tinubu ya yi Allawadai ta juyin mulkin Guinea-Bissau

Shugaba Tinubu ya yi Allawadai ta juyin mulkin Guinea-Bissau

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta yi Allah Wadai da juyin Mulkin da aka yi a Guinea-Bissau, inda ta buƙaci a dawo da mulkin dimokraɗiyya a ƙasar. A cikin wata sanarwa da ma'aikatar kula da harkokin ƙasashen waje na ƙasar ta fitar a yau alhamis, Najeriya ta ce ta damu matuƙa game da lamarin, inda ta bayyana ƙwace mulkin a matsayin 'abin takaici' '' Juyin mulkin na bayyana karya dokokin ECOWAS na mulkin dimokraɗiyya da gwamnati mai adalci, waɗanda suka haramta hawa mulki ta hanyar da ba na tsarin mulki ba.'' inji sanarwar. Ma'aikatar harkokin wajen ta kuma ce Najeriya na tare da ƴan ƙasar Guinea Bissau, kuma ta na kiran dawo wa mulkin dimokradiyyar, da dawo da dukkanin waɗanda ake riƙe da su.
Makarantar Horas da sojoji ta Najeriya, NDA zata bude damar neman aikin soja daga gobe

Makarantar Horas da sojoji ta Najeriya, NDA zata bude damar neman aikin soja daga gobe

Duk Labarai
Makarantar Horas da sojoji ta Najeriya, NDA ta sanar da fara daukar sabbin matasa masu sha'awar aikin soja. Sanarwar tace a gobe, Juma'a idan Allah ya kaimu za'a bayar da dama dan fara neman shiga makarantar. Hukumar ta sanar da hakane ta shafinta na sada zumunta. https://twitter.com/NDefenceAcademy/status/1993779635759235101?t=rKQRx_YcqCyBgweUVE38ww&s=19
Kalli Bidiyon yanda daliban Marigayi Dr. Idris Dutsen Tanshi ke murnar Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, suna fadar kalaman da basu kamata akansa

Kalli Bidiyon yanda daliban Marigayi Dr. Idris Dutsen Tanshi ke murnar Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, suna fadar kalaman da basu kamata akansa

Duk Labarai
Daliban Marigayi, Dr. Idris Dutsen Tanshi sun rika wallafa Bidiyo suna murna da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi Sun rika bayyana cewa wannan ramuwa ce akan abinda daliban Sheikh Dahiru Usman Bauchi suka musu bayan rasuwar malaminsu. Da yawansu sun rika fadar kalaman da basu dace ba akan malamin inda suka ce suna mayar da biki ne. https://www.tiktok.com/@isah_bello_assalafy_garo/video/7577396958919265556?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7577396958919265556&source=h5_m&timestamp=1764263018&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign...