Monday, January 27
Shadow
Mulkin Tinubu ya talauta masu kudi da yawa>>Inji Atiku

Mulkin Tinubu ya talauta masu kudi da yawa>>Inji Atiku

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar wanda kuma shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata na shekarar 2023 ya soki gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bayan da ta cika shekara guda da kafuwa. Atiku yace tsare-tsaren gwamnatin Tinubu ta jefa mafi yawan al'umma cikin halin wahala inda kuma ta talauta masu kudi. Atiku yace Najeriya bata aiki a karkashin Tinubu inda yace Tinubun ya kasa kawo canji da ci gaban da ya mutane alkawari. Yace matakan da Tinubu ya dauka sun ma kara jefa mutanene cikin halin kaka nikayi. Yace matsayin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki a yanzu yafi muni idan aka kwatanta da shekara daya data gabata. Yace gwamnatin Tinubun ta karawa mutane wahala ne akan wahalar da ake ciki wadda gwamnatin tsohon s...
Sai an shekara 6 ana shan wahalar da cire Tallafin man fetur ya kawo>>Inji Shugaban ADC

Sai an shekara 6 ana shan wahalar da cire Tallafin man fetur ya kawo>>Inji Shugaban ADC

Siyasa
Shugaban jam'iyyar ADC, Dr Ralphs Okey Nwosu ya bayyana cewa, sai an shekara 6 ana wahala kamin a kawo karshen wahalar da cire tallafin man fetur ya jefa mutane. Ya bayyana hakane hirar da Daily Trust ta yi dashi. Cire tallafin man fetur ya jefa mutane da yawa a cikin matsin rayuwa inda mutane suka rika fama da abinda zasu ci wanda a baya ba haka bane. Saidai Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, wannan mataki ne data dauka dan amfanar al'umma baki daya wanda kuma na dolene.
Wata Sabuwa: Ana zargin kwaikwayar sa hannun Babban alkalin kotun Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya wanda yace a sauke Sarki Sanusi II daga kujerar sarautar Kano, Kalli Hotunan dake tabbatar da hakan

Wata Sabuwa: Ana zargin kwaikwayar sa hannun Babban alkalin kotun Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya wanda yace a sauke Sarki Sanusi II daga kujerar sarautar Kano, Kalli Hotunan dake tabbatar da hakan

Kano
Wasu alamu sun nuna cewa ga dukkan mai yiyuwa kwaikwakayar sa hannun babban alkalin kotun tarayya dake Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya da yace a cire sarki Muhammad Sanusi II daga kan kujerar sarautar Kano. A wani bincike da Kafar Daily Nigerian ta yi, ta gano cewa sa hannun da aka gani a takardar data dakatar da sarkin ta banbanta da sauran sahannun da alkalin ya saba yi. Kuma a baya, Alkalin yakan saka hannu a duka takardun hukunci ne amma a na hukuncin da ya sauke sarkin, a takardar karshe ce kawai aka saka hannun. Hakanan kuma Akwai wanda ake tuhuma a takardar kotun su 8 amma cikinsu babu wanda baiwa kwafin takardar sai kwamishinan 'yansandan jihar kadai. Wannan yasa ake zargin cewa takardar ta boge ce.
Ba A Taɓa Gwamnatin Da Ta Kawo Wa Nijeriya Bàĺà’ì Da Mùśìbà Kamar Gwamnatin Buhari Ba, Cewar Attahiru Bafarawa

Ba A Taɓa Gwamnatin Da Ta Kawo Wa Nijeriya Bàĺà’ì Da Mùśìbà Kamar Gwamnatin Buhari Ba, Cewar Attahiru Bafarawa

Duk Labarai
Daga Imam Aliyu Indabawa Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi Allah wadai da masu baiwa Buhari da gwamnatinsa kariya yana mai cewa duk mutumin da zai iya fitowa ya kare Buhari da gwamnatinsa to za su haɗu da shi a lahira a gaban Allah. A yayin tattaunawarsa da kamfanin watsa labarai na BBC Hausa tsohon gwamnan ya ce," Bala'in da Buhari ya kawo ƙasar nan na lalacewar damokraɗiya da cin hanci ni dai a rayuwata ban taba ganin gwamnatin da ta kawo mana bala'i da masifa kamar ta Buhari ba." Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda gwamnatin Buhari ta ciyowa Nijeriya mummunan bashi na tiriliyoyi amma babu wani aiki da aka yi da kuɗin, ya ce wannan sai an je lahira za a yi shari'a a kansa.
Zamu tafi Yajin aiki idan gwamnati bata mana karin albashi ba, Albashin da ake biyan mu yayi kadan>>Inji ASUU

Zamu tafi Yajin aiki idan gwamnati bata mana karin albashi ba, Albashin da ake biyan mu yayi kadan>>Inji ASUU

Ilimi
Kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ta kasa karawa membobinta Albashi da kuma inganta jami'o'in Najeriya. Wakilan kungiyar na jami'o'in Akwa-Ibom, Uyo, University of Cross River State, University of Calabar, da University of Uyo ne suka bayyana haka. Sunce rabon da a duba albashinsu dan kari shekaru 15 kenan duk da cewa sauran bangarori na kasarnan an kara musu albashin a lokuta da dama. Sun kuma ce akwai alkawuran kudade da gwamnati ta musu wanda har yanzu bata cika ba. Kungiyar tace amma ana hakane gwammatin ta dauki Biliyan 90 ta baiwa mahajjata a matsayin tallafi.