Sojoji Ne Suka Ƙaƙaba Mana Obasanjo Ba A Barmu Munyi Zabin Mu Ba – Ambasada Wali
Sojoji Ne Suka Ƙaƙaba Mana Obasanjo Ba A Barmu Munyi Zabin Mu Ba - Ambasada Wali
Ɗaya daga cikin jigo a siyasar Arewacin Najeriya kuma tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Wali ya ce gabanin zaben shekarar 1999, sojojin da za su miƙa mulki ga farar hula ne suka ƙaƙaba wa 'yan siyasa Cif Olusegun Obasanjo wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a waccan shekarar.
Ambasada Wali wanda yana cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar PDP a shekarar 1998, ya ce "lokacin PDP da aka je kulla yarjejiniya a Jos a shekarar 1998, wanda kuma a lokacin soja ne ke mulki, ba a bar mu mun zaɓi abin da muke so ba."
"Da sai a ƙyale mu mu zaɓi wanda muke so. Amma haka ba ta samu ba. Ba don shigowar soja ba, suka dan saka hannunsu, watakila da Obasanjo bai zama ɗan takara ba".
"Kuskuren da muka yi lokac...