Tuesday, March 24
Shadow
Wani Magidanci ya je ofishin ‘yansanda na jihar Kano inda yace zai kara aurene shine ya baiwa matarsa Naira Miliyan 2 toshiyar baki, shine yake neman shawara ko hakan ya sabawa doka?

Wani Magidanci ya je ofishin ‘yansanda na jihar Kano inda yace zai kara aurene shine ya baiwa matarsa Naira Miliyan 2 toshiyar baki, shine yake neman shawara ko hakan ya sabawa doka?

Duk Labarai
Wani magidanci ya je ofishin 'yansanda na jihar Kano inda yace zai kara aurene dan haka ya baiwa matarsa toshiyar baki ta Naira Miliyan 2. Shine yake neman shawara ko hakan ya dace da doka? Kakakin 'yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.
Kalli Bidiyon yanda aka shirya yakin neman zabe a Legas dan kira ga Shugaba Tinubu ya fito takara a 2027

Kalli Bidiyon yanda aka shirya yakin neman zabe a Legas dan kira ga Shugaba Tinubu ya fito takara a 2027

Duk Labarai
Mutane da yawa ne a Legas suka fito dan kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake fitowa takara a shekarar 2027. An ga mutanen na daga kwalaye masu dauke da hotunan shugaban kasar. Saidai wasu sun yi zargin an baiwa mutanen kudi ne. Hakanan hukumar zabe me zaman kanta INEC a hana irin wannan yakin neman zabe tun kamin lokacin zabe yayi. https://twitter.com/GossipMillNaija/status/1979661716872216952?t=7guCszb453jpOzWzCHCLGg&s=19
Babban Sojan Najeriya Lt. Col. Aliyu Saidu Paiko da wasu sojoji 5 dake tare dashi sun rigamu gidan gaskiya a fagen daga a jihar Borno

Babban Sojan Najeriya Lt. Col. Aliyu Saidu Paiko da wasu sojoji 5 dake tare dashi sun rigamu gidan gaskiya a fagen daga a jihar Borno

Duk Labarai
Sojan Najeriya, Lt. Col. Aliyu Saidu Paiko da wasu sojoji 5 sun rigamu gidan gaskiya a jihar Borno a yayin da aka kai musu Harin Kwantan Bauna. Lamarin ya farune ranar 17 ga watan October 2025 inda kuma aka kashe CJTF 3. https://twitter.com/Edrees4P/status/1979681137967690102?t=BsJtahuOK0wLPAnT2ZDUVA&s=19
Muma Mun samu bayanan cewa lallai an shirya yiwa Shugaba Tinubu Juyin Mulki, kuma Sojojin da aka kama dalilin haka suna da yawa>>Inji Jaridar Punchng

Muma Mun samu bayanan cewa lallai an shirya yiwa Shugaba Tinubu Juyin Mulki, kuma Sojojin da aka kama dalilin haka suna da yawa>>Inji Jaridar Punchng

Duk Labarai
Jaridar Punchng ta zama ta uku kenan data ruwaito cewa, an kama wasu sojoji da suka shirya yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki. Jaridar tace wata majiyar soji ta tabbatar mata da cewa kamen da kawa wasu sojoji sama da 16 na da alaka da shirin juyin Mulkin da suke shirin yiwa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Jaridar Punchng ta kara da cewa wani janar ne ka jagoranar sojojin da ke shirin kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu wanda suka shirya yi ranar 1 ga watan October. Saidai Hukumar sojojin Najeriya ta ce karyane babu wani shirin jurin mulki aka yiwa shugaba Tinubu. Jaridar Sahara reporters ce ta fara kawo labarin tace an kama sojoji 16 inda daga baya Premium times itama ta ce ta samu wanan rahoto inda tace an kama sojoji 20. Rahoton jaridar Punchng yace amma k...
Mutum Biyu sun taba nunawa mamana Bidiyon wakokin da nake yi, na duresu, saboda me yasa zasu nuna mata salon su tayar mata da hawan jini? Inji Soja Boy me waka yana tabawa da Rhunghumar mata

Tauraron mawakin Batsa da kuma waka tare da runguma da taba mata na Arewa, Soja Boy ya bayyana cewa, ya taba daure wasu mutane 2 da suka nunawa mahaifiyarsa Bidiyon wakar da yake. Yace Ai ta zaginshi da tsinuwa bai damu ba amma me zai saka a rika nunawa mahaifiyarsa irin Bidiyon wakokin da ake yi? https://www.tiktok.com/@_soulja.boy/video/7562676307440438549?_t=ZS-90fmkGFdxzd&_r=1
Kalli Bidiyon: Na fara Bushara kuma nan gaba kadan Karfin wa’azina zai sa a Rushe Masallatan Maiduguri>>Inji Abubakar da ya yi ridda koma Kirista

Kalli Bidiyon: Na fara Bushara kuma nan gaba kadan Karfin wa’azina zai sa a Rushe Masallatan Maiduguri>>Inji Abubakar da ya yi ridda koma Kirista

Duk Labarai
Matashi daga jihar Borno da ya yi ridda ya koma Kirista ya bayyana cewa, ya fara Bushara. Yace nan gaba za'a rushe masallatan Maiduguri. Sannan yace ya nemi a bashi aya da tace ayi Sallah sau biyar a Qur'ani amma an kasa dan haka yanzu abinda yake so shine a kawo mai mutum daya daya shiga Aljannah sanadin Qur'ani. https://www.tiktok.com/@musa.n.ndirmbitah/video/7562693046136016136?_t=ZS-90floVSlv2v&_r=1
Kalli Bidiyo: Soja ta baiwa Abokan aikinta maza shawarar cewa, su san irin matan da zasu rika aure, dan wasu matayen sojojub so suke a kaisu yaki a Kshekye su ci gado

Kalli Bidiyo: Soja ta baiwa Abokan aikinta maza shawarar cewa, su san irin matan da zasu rika aure, dan wasu matayen sojojub so suke a kaisu yaki a Kshekye su ci gado

Duk Labarai
Wata soja ta baiwa abokan aikinta shawara cewa, ya kamata su san irin matan da zasu rika aure dan kuwa wasu matan ba da gaske suke son su ba. Ta bayyana hakane a cikin wani Bidiyo data wallafa a shafinta na Tiktok inda take cewa wasu matan na fatan ma a kai mutum yaki ya mutu su ci gado. Kalli Bidiyon ta anan: https://www.tiktok.com/@numcy5/video/7562213981507783943?_t=ZS-90fjbZewzOy&_r=1
Talauci ne babban makiyin dan Adam>>Inji Atiku Abubakar

Talauci ne babban makiyin dan Adam>>Inji Atiku Abubakar

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, Talauci shine babban makiyin dan Adam. Ya bayyana hakane a cikin sakonsa na ranar yaki da Talauci ta Duniya. Yace Talauci na kawo Jahilci, Cutuka, Matsalar tsaro, da rashin Tabbas a rayuwa. Yace saka wannan rana a matsayin ranar yaki da Talauci ta Duniya kira ne ga gwamnatoci da kungiyoyin fafutuka dama duka masu ruwa da tsaki kan a hada hannu dan yakar Talauci. Yace dolene a dauki matakan yaki da Talauci a Najeriya.