Sunday, March 1
Shadow
Baya halatta mace ta aikata Zyna saboda yunwa ko wata bukatar Duniya>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Baya halatta mace ta aikata Zyna saboda yunwa ko wata bukatar Duniya>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa yunwa ba uzuri bane ga mace ta aikata zina ko kuma tace wai dan 'ya'yanta su yi makaranta duk bai halatta ba. Yace a guri daya ne kawai ya halatta mace ta aikata Zyna shine idan aka ce za'a kasheta idan bata yadda ba. Malam ya bayyana hakane a wajan karatun da yakevna ranar Juma'a da yamma a masallacin Sultan Bello dake Kaduna, kamar yanda wakilin hutudole ya halarta.
Kalli Bidiyo: Amarya ta dauki hankula saboda yin karatu a wajan Bikinta

Kalli Bidiyo: Amarya ta dauki hankula saboda yin karatu a wajan Bikinta

Duk Labarai
Wannan amaryar data rera karatun Qur'ani a wajan Bikinta ta dauki hankulan mutane sosai inda akai ta muhawara. Wasu sun ce wajan ba muhallin karatun Qur'ani bane inda wasu kuma abinda angon yayi ne ya dauki hankulansu. Irin kallon da angon kewa amaryar yasa mutane ke ta fadar maganganu daban-daban. https://www.tiktok.com/@theluxurious_weddings/video/7553234492324973842?_t=ZS-9030EqUwwTJ&_r=1
Kalli Bidiyo: Itama Asiya Chairlady ta shiga sahun ‘yan matan Kannywood da suka mallaki sabuwar wayar iPhone 17 pro, saidai tace da kudinta ta siya

Kalli Bidiyo: Itama Asiya Chairlady ta shiga sahun ‘yan matan Kannywood da suka mallaki sabuwar wayar iPhone 17 pro, saidai tace da kudinta ta siya

Duk Labarai
Tauraruwar Kannywood, Asiya Chairlady ta bayyana mallakar sabuwar wayar iPhone 17 pro wadda ake yayi. Asiya ta zama ta biyu bayan Ummi Gayu a masana'antar Kannywood da suka fito suka bayyana mallakar wayar a fili. A Bidiyon data wallafa a shafinta na Instagram, an ganta a zaune a shagon da ta sayi wayar. Kalli Bidiyon anan:
Kalli Bidiyon yanda Aka warce wayar wannan Faston a kan Titin Birnin Landan yayin da yake daukar kansa hoton Bidiyo yana addu’a

Kalli Bidiyon yanda Aka warce wayar wannan Faston a kan Titin Birnin Landan yayin da yake daukar kansa hoton Bidiyo yana addu’a

Duk Labarai
Wani fasto me suna Pastor Isaac Anderson’s an warce masa waya akan titin birnin Landan yayin da yake daukar kansa hoto yana addu'a. Faston yace wani ne akan keke ya je ya warce masa wayar wadda yace iPhone 16 pro ce. Saidai yace abinda yafi damunsa shine abubuwan dake ciki. Kalli Bidiyon faruwar lamarin a kasa: https://twitter.com/vanguardngrnews/status/1971310965154312676?t=85aCbjx3K-O1qsthg45IdA&s=19
Kalli Bidiyo: Na yi mamaki da naji ance Kwankwaso zai dawo APC, saboda a baya ya Zhaghi shugaba Tinubu sannan yace masu shiga APC Mahaukata ne>>Inji Ganduje

Kalli Bidiyo: Na yi mamaki da naji ance Kwankwaso zai dawo APC, saboda a baya ya Zhaghi shugaba Tinubu sannan yace masu shiga APC Mahaukata ne>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana mamakin sa da jin labarin komawar Kwankwaso APC. A wata hira da aka yi dashi bayan taron masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC ta Kano, Ganduje yace Kwankwaso ya yi munanan kalamai na zagi da cin mutunci ga shugaban kasa da jam'iyyar APC amma gashi wai yau shine ke shirin komawa jam'iyyar. Kalli Bidiyon anan: https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1971447796122501280?t=jGM3xeLPD9upzrxQmB7HPA&s=19
Da Duminsa: Kwankwaso ya fara tattaunawa da shugaban jam’iyyar APC a shirin da yake na komawa Jam’iyyar

Da Duminsa: Kwankwaso ya fara tattaunawa da shugaban jam’iyyar APC a shirin da yake na komawa Jam’iyyar

Duk Labarai
Rahotanni sun ce tuni, tsohon Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fara tetaunawa da shugaban jam'iyyar APC a shirin da yake na komawa jam'iyyar. Alamun tattaunawar tasu ta bayyana ne jiya, Alhamis, Kamar yanda Jaridar Daily Trust ta bayyana inda tace Kwankwason ya fara tattaunawa da shugaban APC, Prof. Nentawe Yilwatda Rahoton yace tuni Kwankwaso ya aikawa da hedikwatar Jam'iyyar APC da aniyarsa ta son shiga jam'iyyar a hukumance. Wata Majiya daga APC ta tabbatarwa da jaridar cewa, Kankwaso da shugaban APC din sun tattauna sosai kuma suna gab da kammala tattaunawar dan shigar Kwankwaso jam'iyyar.
Matatar man Dangote ta kori duka ma’ikatanta na Najeriya bayan da suka shiga kungiyar kwadago ta PENGASSAN

Matatar man Dangote ta kori duka ma’ikatanta na Najeriya bayan da suka shiga kungiyar kwadago ta PENGASSAN

Duk Labarai
Rahotanni sun ce matatar man fetur ta Dangote ta kori duka m'aikatanta 'yan Najeriya. Matatar tace ta yi hakanne dan canja fasalin ayyukanta. Saidai hakan na zuwane bayan da ma'aikatan suka shiga kungiyar kwadago ta ma'aikatan man fetur ta PENGASSAN. Jimullar wadanda aka kora daga aikin sun kai mutane 1000 saidai matatar bata kori ma'akatan dake mata aiki 'yan kasashen waje ba. Rikici da rashin fahimtar juna yai kamari tsakanin Dangote da kungiyar ta PENGASSAN inda ta zargi Dangoten da hana ma'aikatan matatarsa shiga kungiyar wanda tace hakan ya sabawa dokokin aiki a Najeriya. Saidai Dangote ya sha cewa shiga kungiyar kwadagon zabine ba abune na dole ba.
Kalli Bidiyon: Rahama Saidu me babban Shago inda ta mikawa namiji da yaje sayayya hannu su gaisa amma yaki yadda ya bata hannu

Kalli Bidiyon: Rahama Saidu me babban Shago inda ta mikawa namiji da yaje sayayya hannu su gaisa amma yaki yadda ya bata hannu

Duk Labarai
Rahama Saidu me babban shago ta dauki hankula inda ta mikawa daya daga cikin kwatomominta hannu su gaisa amma yaki yadda ya mika mata hannu. Inda a gefe daya kuma ta mikawa Soja Boy hannu suka gaisa. Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa wai Namiji ne yake kin shan hannun mace amma ita tana mika masa hannu. A baya dai Soja Boy da Rahama Saidu sun gaisa hakanan ya ma rungumeta lamarin da ya jawo cece-kuce me zafi. https://www.tiktok.com/@abu_ayrin_backup/video/7553946644190989575?_t=ZS-9029A5Isqh7&_r=1