Saturday, April 26
Shadow
Kalli Bidiyo: Yara ‘yan shekaru 15 zuwa 16 su 3 uwarsu daya ubansu daya wanda aka dauka daga Najeriya aka kaisu suna ka-ru-wan-ci a kasar Ghana

Kalli Bidiyo: Yara ‘yan shekaru 15 zuwa 16 su 3 uwarsu daya ubansu daya wanda aka dauka daga Najeriya aka kaisu suna ka-ru-wan-ci a kasar Ghana

Abin Mamaki
Bidiyon wasu kananan yara 'yan mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 16 su 10 da aka dauka daga Najeriya aka kaisu kasar Ghana yin karuwanci ya tayar da hankula. Bidiyon ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda aka gansu ana tambayarsu kowace na fadin shekarunta da jihar data fito, yawancinsu sun fito ne daga jihar Imo kuma daga cikinsu akwai guda 3 wanda uwarsu daya ubansu daya. https://twitter.com/Onsogbu/status/1799027863666262141?t=kBSG-jgJbFcfH_XL3BV3Rw&s=19 Ko da aka tambayesu iyayensu sun san sun tafi karuwanci? Sai suka ce a'a. Lamarin dai ya dagawa mutane hankula sosai inda akai ta musu Allah wadai. Tuni dai gwamnatin tarayya ta sanar da fara bincike kan lamarin. Ama kan hakane Gwamnatin ta yi sabuwar dokar da ta hana zuwan kananan 'yan mata da basu ci...
Gwamnatin tarayya ta haramtawa ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 18 shiga Otal

Gwamnatin tarayya ta haramtawa ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 18 shiga Otal

Siyasa, Tsaro
Gwamnatin tarayya karkashin Ma'aikatar mata ta haramtawa Kananan yara 'yan kasa da shekaru 18 shiga otal. Ministar matan, Uju Ohaneye ce ta bayyana hakan inda tace dole duka otal din dake Najeriya dolene su bi wannan umarni. Tace duk Otal din da aka samu bai bi wannan umarni ba zai iya fuskantar hukuncin dakatarwa. Tace an dauki matakanne dan kawar da matsalar safarar 'yan mata. Hakan na zuwane dai a yayin da wasu bidiyon 'yan mata dake da shekarun tsakanin 15 zuwa 16 aka ga an yi safarar su zuwa kasar Ghana dan yin Karuwanci.
Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima

Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima

Siyasa
Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima. DAGA: Abbas Yakubu Yaura Wani jigo a jam’iyyar, NNPP, Buba Galadima ya ce ba zai taba yiwuwa ɗaukacin yankin Arewa su samu ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya a zaɓen 2027 ba. A wata hira da jaridar Sun, tsohon sakataren rusasshiyar jam'iyyar CPC, ya bayyana cewa a tsarin dimokuradiyya irin na Najeriya, masu zaɓe na da ƴancin yin zaɓi daban-daban. Da aka tambaye shi ko ƴan Arewa za su zaɓi Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ko kuma takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, Galadima ya ce, “Ba ma cikin còci; Ba ma cikin másallaci. Me ya sa za mu yi magana da murya ɗaya? “Dimokradiyya kenan."Idan ka haɗa mutane uku tare, kowa ya sami hanyar t...
Shekara ɗaya maƙiya Kano su ka yi su na cin dunduniyar gwamnatin Abba, Cewa Kwankwaso

Shekara ɗaya maƙiya Kano su ka yi su na cin dunduniyar gwamnatin Abba, Cewa Kwankwaso

Duk Labarai
Madugun Kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zargi 'yan adawa a Kano da cin dunduniyar gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf har tsawon shekara guda. Kwankwaso ya fadi haka ne a lokacin da gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta-baci kan ilimi a jihar Kano a yau Asabar. Ya ce, “Bari in fara da taya shi murnar wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Sanin kowa ne cewa gwamna yana aiki tun daga ranar da ya hau mulki a ko’ina a fadin jihar. “Duk da cewa gwamnan ya na fuskantar kalubale tsawon shekara guda. Nan da nan bayan zaɓe, maƙiyan Jiha sun kai shi Kotu, zuwa Kotun Daukaka Kara zuwa Kotun Koli. Mun ga abin da ya faru duk da sun san cewa babu bukatar a je wata Kotu. Kowa ya san cewa ya ci zabensa...
TIRKASHI: Ya Saki Matarsa Saboda Ganyen Shayi, Bayan Tsawon Shakara Goma Suna Zaman Aure

TIRKASHI: Ya Saki Matarsa Saboda Ganyen Shayi, Bayan Tsawon Shakara Goma Suna Zaman Aure

Auratayya
TIRKASHI: Ya Saki Matarsa Saboda Ganyen Shayi, Bayan Tsawon Shakara Goma Suna Zaman Aure Daga Mubarak Ibrahim Lawan "Da Asubahi ta gaya wa mijin cewa ganyan shayi ya ƙare. Wajen ƙarfe shida na safe kuma ƙaninsa ya zo ya ɗauke shi suka tafi jana'izar wani abokin kasuwancinsu. Bayan ya dawo gida wajen ƙarfe 9 na safiyar, sai ya tarar yaransa ba su tafi makaranta ba. Ya tambayi dalili sai ta ce ai bai kawo ganyen shayin da za su yi karin kumallo ba. Daga nan fitina ta fara. A yinin ya sallame ta. Lokacin da iyaye suka shiga maganar, sai ya ce ya gaji da zama da macen da ta ke kasa yi masa hidimar naira 100 duk da cewa shi ya na iya yi mata hidimar miliyan 5 domin, a shekarar bara ma ya kai ta Hajji, ya canja mata kujeru, kuma ya tabbatar cewa shi ya sama mata aikin da ta ke yi. Ya ƙa...
Idan Har Kina Sha’awar Shigowa Harkar Fim Amma Ba Ki Shigo Ba Tukun, To Ki Rufawa Kanki Asiri Ki Je Ki Yi Aure Ya Fi Miki, Shawarar Hadiza Gabon Ga ‘Yan Mata Masu Sha’awar Shiga Harkar Finafinan Hausa

Idan Har Kina Sha’awar Shigowa Harkar Fim Amma Ba Ki Shigo Ba Tukun, To Ki Rufawa Kanki Asiri Ki Je Ki Yi Aure Ya Fi Miki, Shawarar Hadiza Gabon Ga ‘Yan Mata Masu Sha’awar Shiga Harkar Finafinan Hausa

Hadiza Gabon, Kannywood
IDAN KUNNE YA JI. Idan Har Kina Sha'awar Shigowa Harkar Fim Amma Ba Ki Shigo Ba Tukun, To Ki Rufawa Kanki Asiri Ki Je Ki Yi Aure Ya Fi Miki, Shawarar Hadiza Gabon Ga 'Yan Mata Masu Sha'awar Shiga Harkar Finafinan Hausa. Daga Rariya.
Kalli Bidiyo: Kalli ya da jama’ar kasar Burki na Faso ke lakadawa tsohon Ministansu duka bayan samunsa da sace makudan kudade

Kalli Bidiyo: Kalli ya da jama’ar kasar Burki na Faso ke lakadawa tsohon Ministansu duka bayan samunsa da sace makudan kudade

Siyasa
Bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumuna na tsohon ministan sufuri a kasar Burkina Faso,Vincent Dabilgou inda aka ga mutane na zaneshi. An masa hakane bisa zargin cewa ya saci makudan kidade a kasar. https://twitter.com/PSAFLIVE/status/1799334263747465694?t=utEYAEYbq_Y905R_nO6sWA&s=19 Lamarin dai ya dauki hankula sosai inda da yawa suka rika cewa sun yi fatan a kasarsu ma za'a iya yin hakan