Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ce Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya koma jihar Kebbi da zama har sai an kubutar da dalibai ‘yan mata
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle umarnin komawa jihar Kebbi da zama har sai an kubutar da dalibai mata da aka yi Gharkùwà dasu.
Ana taammanin nan da ranar Juma'a ne Bello Matawalle zai koma jihar Kebbin da zama dan ya jagoranci kubutar da 'yan matan.
Yara mata 25 ne dai aka sace daga makarantunsu inda kuma aka Khashye daya daga cikin malamansu
Lamarin ya jawo Allah wadai da kiraye-kirayen a dauki mataki.








