Ana zargin Ministan Shari’a da cire sunan Shugabar bankin Fidelity Bank daga zargin Almundahana duk da shaida karara
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta cire sunan shugabar bankin Fidelity Dr. Nneka C. Onyeali-Ikpe daga sunayen mutanen da take bincika.
Babban Lauyan Najeriya, kuma Ministan shari'a, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya fara bincikenta a baya bisa zargin damfara da Almundahana.
Wasu daga cikin zarge-zargen da ake mata shine amfani da kudin bankin wajan sayen hannun Jari na miliyoyin Naira.
Saidai gashi yanzu da Alama Gwamnatin ta yafe mata.








