Sunday, December 14
Shadow
Ke Uwace, Ki yi hakuri da rashin Kunyar da matan jihar mu suka miki, daukar nauyinsu aka yi>>Wike ya baiwa matar shugaban kasa, Remi Tinubu hakuri bayan matan jihar Rivers sun tashi sun fice daga dakin taro yayin da take jawabi

Ke Uwace, Ki yi hakuri da rashin Kunyar da matan jihar mu suka miki, daukar nauyinsu aka yi>>Wike ya baiwa matar shugaban kasa, Remi Tinubu hakuri bayan matan jihar Rivers sun tashi sun fice daga dakin taro yayin da take jawabi

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya baiwa matar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu watau Remi Tinubu hakuri kan abinda matan jihar Rivers suka mata. A jiya Juma'a ne dai hutudole ya kawo muku rahoton cewa, matan jihar ta Rivers ana tsaka da taro sun tashi sun tafi yayin da matar shugaban kasar ke tsaka da jawabi inda suka ce basa son saurarenta. Wike ta bakin kakakinsa, Lere Olayinka ya bayyana cewa wannan abin kunyane kuma daukar nauyin matan aka yi. Yace wanda ke cewa yana neman sulhu ne wai yake irin wannan abin inda yace ba da gaske yake ba. Wike yace a madadin al'ummar jihar Rivers kuma a matsayinsa na dattijo daga jihar Rivers yana baiwa matar shugaban kasar Hakuri.
Manyan Malaman Najeriya, Sheikh Daurawa, Bin Uthman, da Gidado Triumph sun roki Allah yasa kada gobarar kasar Israyla ta mutu

Manyan Malaman Najeriya, Sheikh Daurawa, Bin Uthman, da Gidado Triumph sun roki Allah yasa kada gobarar kasar Israyla ta mutu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} A yayin da annobar gobarar daji ta Dumfari kasar Israyla mutane nata bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. Manyan Malam Arewacin Najeriya ma ba'a barsu a baya ba. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1918519721491570788?t=2-0V3cJ7oi64ly1SW_1BFQ&s=19 Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Sheikh Muhammad Bin Uthman, da Sheikh Abdulmudalib Gidado Triumph duk sun yi fatan Allah yasa kada wutar ta mutu. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1918520226720678252?t=qq6f5cmVzbYaH0q3Ow...
Katsinawa sun nishadantar dani sosai, ji na yi kamar a garin mu nake>>Shugaban kasa, Bola Ahmad

Katsinawa sun nishadantar dani sosai, ji na yi kamar a garin mu nake>>Shugaban kasa, Bola Ahmad

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Katsinawa sun Nishadantar dashi sosai a ziyarar da ya kai jihar. Tinubu ya bayyana hakane bayan da mawaka ciki hadda Rarara suka wakeshi da yaren Yarbanci. https://twitter.com/NTANewsNow/status/1918607611420660172?t=hq3bHIKxYRmmRMKg7N5mYw&s=19 Ya jinjinawa mawakan inda a wasu lokutan aka hangoshi yana rausayawa.
An gano motoci 150 da aka sato daga kasar Canada a Najeriya, Gambia, Mauritania da sauran kasashen Afrika

An gano motoci 150 da aka sato daga kasar Canada a Najeriya, Gambia, Mauritania da sauran kasashen Afrika

Duk Labarai
'Yansandan kasa da kasa, Interpol sun gano motoci 150 da aka sato daga kasar Canada a kasashe daban-daban na Afrika. An yi bincikenne a tsakanin kasashen Afrika 12 a tsakanin ranekun March 17 to 30, 2025. Interpol sun ce sun hada kai da 'yansandan wadannan kasashe na Afrika wanda suka hada da Najeriya da Ghana. Hakanan sun ce an binciki motoci 12,600 inda aka gano wasu motoci an satosu ne daga kasashen Faransa, Jamus, Netherlands Yawanci motocin da aka kama Toyota ne, Honda da Peugeot. Mot9da yawa ne ake sacewa a Duniya duk shekara
Ƴànbìndìgà sun yi gàrkùwà da mata 25 a hanyar zuwa biki a Zamfara

Ƴànbìndìgà sun yi gàrkùwà da mata 25 a hanyar zuwa biki a Zamfara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mata 25 a garin Kurmi na ƙaramar hukumar Maru An ce dai an yi garkuwa da matan ne suna kan hanyar zuwa gidan bikin. Haka ma wasu ƴan bindigar sun yi garkuwa da aƙalla mutum 19 yayin da suka raunata ƙarin wasu da dama, a garin Galadi da ke ƙaramar hukumar Tsafe, duk dai a jihar ta Zamfara.
Kalli Bidiyon yanda Rarara ya kai matarsa ta gaishe da shugaban kasa, Tinubu

Kalli Bidiyon yanda Rarara ya kai matarsa ta gaishe da shugaban kasa, Tinubu

Duk Labarai
A yayin ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a daren ranar Juma'a, Tauraron mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara ya gabatarwa da shugaba Tinubu da matarsa, A'isha Humaira inda ta gaishe da shugaban kasar. https://twitter.com/abdullahayofel/status/1918552250688975253?t=ujjnjfaaHXn-GJEWleawMw&s=19 Shugaba Tinubu dai ya ji dadin wakar da Rarara ya masa sosai.