Da Duminsa: Dangote ta hannun gidan man fetur din MRS ya rage farashin man fetur zuwa Naira 739 a Legas kadai
Rahotanni daga Legas na cewa, Dangote ya rage farashin Man fetur inda gidan man MRS ya fara sayar da man akan Naira 739 akan kowace lita.
An ga masu motoci na ta layin shiga gidaje man MRS a Legas dan sayen man me sauki.
Hakan na zuwane bayan da Dangote ya rage farashin da yake sayarwa gidajen man fetur zuwa Naira 699 akan kowace lita.
Dangote dai yasha Alwashin wannan ragi zai kai kowane sashi na Najeriya inda yace za'a rika sayen man aka Naira 740 akan kowace lita.
Ya zargi 'yan kasuwar man fetur da ke shigo da man daga kasashen waje da kara masa kudi da gangan dan su ci kazamar riba.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/2001239798380683416?t=-LTXiIhd9krAX3VvMMmQtw&s=19








