Thursday, December 18
Shadow
Idan Saurayinki ya miki alkawarin zai aureki amma daga baya ya ki aurenki ko ya auri wata, zaki iya kaishi kara kotu>>Inji Lauya Emmanuella

Idan Saurayinki ya miki alkawarin zai aureki amma daga baya ya ki aurenki ko ya auri wata, zaki iya kaishi kara kotu>>Inji Lauya Emmanuella

Duk Labarai
Lauya Emmanuella Ojialor ta bayyana cewa mata zasu iya kai duk namijin da ya musu Alkawarin aure amma daga baya yaki aurensu kotu. Ta bayyana cewa, doka ta bayar da dama muddin mace na da hujja ko shaidu ta kai kara ta nemi a biyata diyya. Ta yi gargadi ga mata masu daukar doka a hannu ta hanyar aikata abubuwan da basu dace ba.
Da Duminsa: Dangote ta hannun gidan man fetur din MRS ya rage farashin man fetur zuwa Naira 739 a Legas kadai

Da Duminsa: Dangote ta hannun gidan man fetur din MRS ya rage farashin man fetur zuwa Naira 739 a Legas kadai

Duk Labarai
Rahotanni daga Legas na cewa, Dangote ya rage farashin Man fetur inda gidan man MRS ya fara sayar da man akan Naira 739 akan kowace lita. An ga masu motoci na ta layin shiga gidaje man MRS a Legas dan sayen man me sauki. Hakan na zuwane bayan da Dangote ya rage farashin da yake sayarwa gidajen man fetur zuwa Naira 699 akan kowace lita. Dangote dai yasha Alwashin wannan ragi zai kai kowane sashi na Najeriya inda yace za'a rika sayen man aka Naira 740 akan kowace lita. Ya zargi 'yan kasuwar man fetur da ke shigo da man daga kasashen waje da kara masa kudi da gangan dan su ci kazamar riba. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/2001239798380683416?t=-LTXiIhd9krAX3VvMMmQtw&s=19
Naso in samar wa da jihata wutar Lantarki da bata daukewa amma shugaban kasa ya hanani>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Victor Atah

Naso in samar wa da jihata wutar Lantarki da bata daukewa amma shugaban kasa ya hanani>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Victor Atah

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Obong Victor Attah ya bayana cewa, ya so samarwa da mutanen jiharsa Wutar Lantarki da bata daukewa amma Shugaban kasa ya hanashi. Yace a wancan lokacin ya gina tashar samar da wutar lantarkin kuma har shugaban kasa ya je ya kaddamar da ita. Yace amma da shugaban kasa ya koma Abuja sai yayi sabuwar doka cewa jihohi ba zasu iya samar da wuta kuma su rarrabata ba. Yace a haka aikin ya lalace. https://twitter.com/NigeriaStories/status/2001195784100860330?t=y07yNhYPgverUhw3rthwOQ&s=19
Ashe Dama Shafa Wali Budurwace? Kalli Bidiyon inda tace ta haqura da soyayya

Ashe Dama Shafa Wali Budurwace? Kalli Bidiyon inda tace ta haqura da soyayya

Duk Labarai
Tauraruwar Kafafen sada zumunta kuma 'yar Kasuwa, Shafa Wali ta bayyana irin gwagwarmayar data yi wajan neman Masoyi na gari. Ta bayyana hakane yayin da takewa Amarya da Ango huduba watau diyar Hafsat Idris da Angonta. Tace ta yi soyayya a baya amma yaudararta ake. Tace dalili kenan ma da yasa ta hakura da soyayya. https://www.tiktok.com/@junior__media/video/7584622592963644689?_t=ZS-92IKGFWOaGn&_r=1 Hakan yasa da yawa suka rika cewa ashe Budurwa ce, wasu sun rika kiranta da ta zo ta auri mahaifisu. https://www.tiktok.com/@interio28/video/7584518639357889813?_t=ZS-92IMLaXvqXx&_r=1
Wannan Tsabar Muguntace, Inji Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu bayan da Dangote ya rage farashin man fetur dinsa zuwa Naira 740 aka kowace lita

Wannan Tsabar Muguntace, Inji Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu bayan da Dangote ya rage farashin man fetur dinsa zuwa Naira 740 aka kowace lita

Duk Labarai
Kungiyar 'yan Kasuwar man fetur masu zaman Kansu PETROAN ta yi Allah wadai da rage farashin man fetur da Dangote yayi zuwa Naira 740 akan kowace lita. Dangote ya rage farashinne daga yanzu har zuwa watan Fabrairu. Inda 'yan kasuwar suka ce hakan zai sa su rasa Kwastomominsu dakuma tafka asarar Naira Biliyan 100. Kungiyar tace sabawa doka ne ace mutum daya ne zai rika kayyade farashin man fetur a Najeriya. Tace a su kadai wannan lamari zai shafa ba haddashi Dangoten.
Kalli Bidiyon da Duminsa: Yanda Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, FCDA karkashin Wike ta kutsa da karfi cikin Ginin River Park duk da Umarnin Kotu

Kalli Bidiyon da Duminsa: Yanda Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, FCDA karkashin Wike ta kutsa da karfi cikin Ginin River Park duk da Umarnin Kotu

Duk Labarai
Hukumar babban birnin tarayya, Abuja FCDA ta rushe wani sahe na River Park sannan ta kutsa da karfi cikin ginin duk da umarnin kotu na hana hukumar shiga ginin. An ga Bidiyon faruwar lamarin wanda ya baiwa mutane mamaki. https://twitter.com/NigeriaStories/status/2001222213177933853?t=pvI_aZuJCsTxvX5Mbx_UrQ&s=19 https://twitter.com/ruffydfire/status/2001219785388966102?t=RFckjyKTTNVW2MVN0HEwfA&s=19
Ba gudu ba ja da baya sai mun yi zàngà-zàngàr da muka shirya>>Inji Kungiyar Kwadago bayan ganawa da shugaba Tinubu

Ba gudu ba ja da baya sai mun yi zàngà-zàngàr da muka shirya>>Inji Kungiyar Kwadago bayan ganawa da shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa, babu gudu ba ja da baya ta shirya tsaf dan ci gaba da zanga-zangar data shirya ayau. Hakan na zuwane bayan ganawar da kungiyar ta yi da shugaba Tinubu a daren ranar Talata. Shuganan NLC, Joe Ajaero ya bayyana wa manema labarai a hedikwatar NLC cewa zasu fita zanga-zangar da suka shirya yau ba fashi. Tuni hukumar 'yansandan Najeriya ta sanar da kai jami'an ta na musamman gurare daban-daban dan hana bata gari shiga zanga-zangar su batata.