Monday, April 6
Shadow
Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar ‘yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu’a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiyar Rashin Lafiya

Duk Labarai
Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar 'yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu'a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiya. Allah Ubangiji ya kawo masa ɗauki na gaggawa.
Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka hàrbè wani dan Daba me suna Halifa Baba a Kano wanda duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun sa a ciki

Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka hàrbè wani dan Daba me suna Halifa Baba a Kano wanda duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun sa a ciki

Duk Labarai
Rahotanni daga unguwar Gwammaja da ke nan Kano sun bayyana yadda a ka harbi wani rikakken dan daba, Halifa Baba, yayin arangama tsakanin jami'an tsaro da bata-gari a yankin. A na zargin cewa duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun Halifa Baba a ciki. Majiyarmu tace bisa dukkan alamu Halifa Baba rai ya yi halinsa. https://www.tiktok.com/@garkuwanyancrypto/video/7496266492581907717?_t=ZM-8vlrVEM7buw&_r=1 Shaidu sun ce jami'an 'yan sandan Dala Division ne su ka dauke Halifa Baba domin ci gaba da bincike. Daga NasaraRadio
Yaro mai shekaru 11 ya mùtù bayan ya fado daga bishiyar mangwaro

Yaro mai shekaru 11 ya mùtù bayan ya fado daga bishiyar mangwaro

Duk Labarai
Wani yaro dan shekara 11 mai suna Joshua Samson ya mutu bayan ya fado daga bishiyar mangwaro a kauyen Bugakwo da ke karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja. Wani mazaunin Bugakwo mai suna Danjuma, ya shaidawa DAILY TRUST cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, a lokacin da marigayin ya hau bishiyar mangwaro don ya tsinka. Ya ce yaron ya hau bishiyar mangwaron ne domin ya tsinko mangwaro, amma sai ya zame daga kan reshen ya fado kasa. Ya ce daya daga cikin yaran da suka je diban mangwaron ne ya ruga gida yana kuka ya kai rahoto ga iyayen marigayin, inda suka garzaya da shi asibiti. Ya ce yaron ya mutu ne bayan kansa ya bugu a kan dutse a karkashin bishiyar mangwaron, inda ya ce an binne yaron. “Ma’aikatan lafiya a cibiyar lafiya ta Kwaku sun tabbatar da mutuwarsa s...
Kada ku bai wa ƴansanda bashin da ba za su iya biya ba, IG ya shawarci ƴan Nijeriya

Kada ku bai wa ƴansanda bashin da ba za su iya biya ba, IG ya shawarci ƴan Nijeriya

Duk Labarai
Sufeto Janar na Ƴansanda, Dr. Kayode Egbetokun, ya shawarci al’ummomin da jami’an tsaro ke aiki a yankunan su da su daina ba su rancen manyan kudade waɗanda za su wahala wajen biya. IG ɗin, wanda Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kogi, Miller Dantawaye, ya wakilta, ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin bikin ƙaddamar da sabuwar hedikwatar ‘yansanda a gundumar Imane, karamar hukumar Olamaboro ta jihar. “Bari in ja kunnen al’ummar yankin cewa yayin da suke mu’amala da jami’an da za a turo musu, wasu daga cikinsu za su nemi taimakon kuɗi da rance, amma kada ku ba su rance mai yawa da za su gagara biya,” in ji Dantawaye. Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su kula da sabon ofishin ‘yan sanda, wanda shine irinsa na farko a yankin, wanda wani ɗan asalin yankin, Dr. Peter Ali, ya gina kum...
‘Yan Bindiga sun shiga uku, An kai jami’an ‘yansanda na musamman da suka kware da yaki da ‘yan Bìndìgà a kowace jiha a kasarnan>>IGP

‘Yan Bindiga sun shiga uku, An kai jami’an ‘yansanda na musamman da suka kware da yaki da ‘yan Bìndìgà a kowace jiha a kasarnan>>IGP

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya kai 'yansanda na musamman duka jihohin Najeriya dan su yaki 'yan Bindigar da ake fama dasu. Ya bayar da umarnin cewa kwamandojin 'yansanda na Squadron da su shirya runduna ta musamman ta 'yansanda na karta kwana wanda da an bukacesu a kowane lokaci zasu iya kai dauki. Ya bayar da umarnin ne a zaman ganawa da kwamandojin ranar Talata biyo bayan hare-haren da 'yan Bindiga suka kai jihohin Kwara, Benue da Sokoto suka kashe mutane 21. Hakanan an samu kazaman hare-hare a jihohin Borno, Enugu da Filato.
Ya kamata ‘yan Najeriya su rima godewa kokarin da muke domin ita matsalar tsaro ba’a magance ta a rana daya>>Inji Me baiwa shugaban kasa shawara kan matsalar tsaro, Nuhu Ribadu

Ya kamata ‘yan Najeriya su rima godewa kokarin da muke domin ita matsalar tsaro ba’a magance ta a rana daya>>Inji Me baiwa shugaban kasa shawara kan matsalar tsaro, Nuhu Ribadu

Duk Labarai
Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu yayi kira ga 'yan Najeriya da su rika godewa gwamnati kan kokarin da take dan magance matsalar. Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakanne a wata ganawa da yayi da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Benue a ziyarar da ya kai jihar. Yace idana aka kalli kasashe irin su Sudan zaka ga basu da gwamnati, hakanan kasashe irin su Afghanistan inda yace ya taba yin aiki a can suma wadanda Duniya ta taru dan ta yakesu sune a yanzu suke mulkar kasar. Yace kasashe Irin su Burkina Faso da Nijar da Mali yanzu sojoji ne ke mulki yace dan haka matsalar tsaro ba matsala bace da za'a ce a magance ta a rana daya. Yace ya kamata 'yan Najeriya su rika godiya su san cewa akwai wadanda ke aiki tukuru dan samar da tsaro a kasarna...