Saturday, December 6
Shadow
Majalisar Jihar Kano ta mayar da Yaren Hausa a matsayin wanda za’a rika amfani dashi wajan koyar da dalibai a makarantun Firamare da karamar Sakandare

Majalisar Jihar Kano ta mayar da Yaren Hausa a matsayin wanda za’a rika amfani dashi wajan koyar da dalibai a makarantun Firamare da karamar Sakandare

Duk Labarai
Majalisar Jihar Kano ta mayar da yaren Hausa a matsayin yaren da za'a rika amfani dashi wajan koyar da dalibai a makarantun Firamare da karamar Sakandare. Majalisar ta aiwatar da wannan doka ne ranar 5 ga watan Nuwamba. Hakanan Kwamitin majalisar dinkin Duniya na UNESCO ya amince da wannan mataki saboda karfafa Amani da harshen uwa.
Majalisar Tarayya zata yi dokar tilasta Amfani da motoci masu amfani da wutar Lantarki kadai

Majalisar Tarayya zata yi dokar tilasta Amfani da motoci masu amfani da wutar Lantarki kadai

Duk Labarai
Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wa ƙudirin dokar amfani da ababen hawa masu amfani da lantarki. Ƙudirin mai taken Electric Vehicle Transition and Green Mobility Bill 2025, Sanata Orji Uzor Kalu (daga jihar Abia) ne ya gabatar da shi, wanda ke neman ɗora Najeriya kan "hanyar kyautata muhalli". Mista Kalu ya ce dokar "za ta taimaka wa ɓangaren ƙera ababen hawa, da makamashi, da ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma samar da ayyukan yi". "Dokar ta ba da damar yafe haraji, da harajin shigo da kaya, da harajin kan hanya, da bayar da tallafi ga masu amfani da motoci masu amfani da lantarki da masu samar da su," in ji shi. Ta kuma tilasta kakkafa tashoshin caji a duka gidajen mai da ke faɗin ƙasar.
A karo na 4, Trump ya sake nanata cewa ba zai kauda ido kan Chin Khashin da akewa Kiristoci a Najeriya ba

A karo na 4, Trump ya sake nanata cewa ba zai kauda ido kan Chin Khashin da akewa Kiristoci a Najeriya ba

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a karo na 3 ya sake maimaita cewa, ba zai zuba ido yana kallon Irin kokarin karar da kiristoci da ake yi a Najeriya ba. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da shafin Fadar White House ta wallafa. Trump yace ba lallai ne 'yan Najeriyar su ji dadin matakin da zai dauka ba amma ba zai zuba ido ba. Yace bama a Najeriya ba kadai, dama duka Duniya duk inda ake kokarin karar da Kiristoci zasu kai dauki. https://twitter.com/WhiteHouse/status/1986195249769697516?t=itL37G4-FmScFF5ayc1lfg&s=19
Muma bama son Kharin da America zata kawo, Maimakon haka ta taimaka mana a yi zaben jin ra’ayi dan a raba Najeriya a bamu kasar mu>>Inji Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo

Muma bama son Kharin da America zata kawo, Maimakon haka ta taimaka mana a yi zaben jin ra’ayi dan a raba Najeriya a bamu kasar mu>>Inji Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo

Duk Labarai
Itama dai Kungiyar Ohanaeze Indigbo reshen matasa,OYC ta bayyana cewa, bata son kawo harin da kasar Amurka zata yi zuwa Najeriya. Kungiyar tace maimakon haka, tana neman kasar Amurka ta taimaka musu a gudanar da zaben jin ra'ayi dan a raba Najeriya a basu kasarsu. Kungiyar ta bakin shugabanta, Comrade Igboayaka O. Igboayaka tace ba ita kadai bace hadda kungiyar Jihohin dake tsakiyar Najeriya duk suna neman a yi zaben ba raba gardama dan a raba kasarnan.
Kalli Bidiyon yanda Sabon Magajin garin New York City, na kasar Amurka, Zohran Mamdani ke karatun Qur’ani

Kalli Bidiyon yanda Sabon Magajin garin New York City, na kasar Amurka, Zohran Mamdani ke karatun Qur’ani

Duk Labarai
A wani Bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga Sabon Magajin Garin New York City, dake Kasar Amurka, Zohran Mamdani na karatun Qur'ani. Zohran Mamdani dai ya lashe zaben magajin garin New York City ne ranar Talata. Kuma hakan na zuwane duk da yake cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump baya sonsa. https://www.tiktok.com/@americas.muslim.network/video/7568927947562782007?_t=ZS-919PCoRieWX&_r=1
Na kusa da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na karbar kudi(Cin Hanci) kamin su bayar da dama a ganshi>>Inji Sanata Ali Ndume

Na kusa da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na karbar kudi(Cin Hanci) kamin su bayar da dama a ganshi>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume yayi zargin cewa, na kusa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna neman a basu kudi, cin hanci kamin su bari mutum ya samu damar ganin shugaban kasar. Ali Ndume ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Arise TV inda yace wasu kalilan ne suke samun damar ganin shugaban kasar ba tare da shamaki ba. Ndume yace yakan ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne kawai a wajan taro.
Kalli Bidiyo: Kawai daga Trump yace zai kawo mana dauki kun kasa bacci, Kune ‘yan tà’àddàn kenan? Inji Kirista Mary

Kalli Bidiyo: Kawai daga Trump yace zai kawo mana dauki kun kasa bacci, Kune ‘yan tà’àddàn kenan? Inji Kirista Mary

Duk Labarai
Wata Kirista me suna Mary ta bayyana damuwa kan yanda tace ake ta tayar da hankula da jin cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump zai kawowa Kiristoci Dauki a kasarnan. Mary Tace duk wanda ya tayar da hankalinsa saboda wannan lamari to shine dan ta'addan. Tace kuma taimako sai an kawoshi saidai wanda bai son gani kamin a kawo ya Mhutu. https://www.tiktok.com/@ryma5570769784231/video/7568129427104746764?_t=ZS-919K0F3gdQe&_r=1
Sanatan Kasar Amurka da ya zuga Donald Trump ya kawowa Najeriya Khari yace kwanannan zasu bayyana sunayen masu goyon bayan Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya

Sanatan Kasar Amurka da ya zuga Donald Trump ya kawowa Najeriya Khari yace kwanannan zasu bayyana sunayen masu goyon bayan Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya

Duk Labarai
Sanata Ted Cruz wanda shine ya kai kudirin dokar saka Najeriya cikin jerin kasashen da kasar Amurka zata sakawa ido ya godewa shugaban kasar Amurkar, Donald Trump bisa wannan mataki da ya dauka. Yace sun cimma burinsu na farko inda yace nan gaba kadan zasu shiga mataki na gaba. Watau wanda yace watau zasu fara bayyana sunayen 'yan Najeriya masu hannu a Muzgunawa Kiristoci. https://twitter.com/SenTedCruz/status/1985831621678023014?t=S5DuWr9XfVI8fNYSLbgX1w&s=19
Kalli Bidiyo: Muna nan kan bakan mu muddin Gwamnatin Najeriya bata magance matsalar ba, sai Mun kai mata Khari>>Inji Sakatariyar Fadar Gwamnatin Amurka

Kalli Bidiyo: Muna nan kan bakan mu muddin Gwamnatin Najeriya bata magance matsalar ba, sai Mun kai mata Khari>>Inji Sakatariyar Fadar Gwamnatin Amurka

Duk Labarai
Sakatariyar fadar Gwamnatin Amurka, Karoline Leavitt ta jadada maganar shugaban kasar Amurka, Donal Trump inda yace gwamnatin Tarayya ta dauki matakin kawo karshen cin Zarafin da akewa Koristoci ko kuma su janye duk wani tallafi da suke baiwa Najeriya sannan kuma su kawo Hari. Ta bayyana hakane ga manema labarai a fadar ta Whitehouse Hakan na zuwane yayin da ake ci gaba da cece-kuce akan lamarin a Najeriya inda da yawa ke ganin cewa Amurkar bata da hurumin kawowa Najeriya hari ba tare da amincewar Gwamnati ba. https://www.tiktok.com/@foxnews/video/7568948087582887198?_t=ZS-9196CNtqclc&_r=1