Thursday, March 12
Shadow
Hukumar EFCC na tsaka mai wuya inda aka samu jami’anta da sace kudade da kadarorin da aka kwato daga ma’aikatan Gwamnati

Hukumar EFCC na tsaka mai wuya inda aka samu jami’anta da sace kudade da kadarorin da aka kwato daga ma’aikatan Gwamnati

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC na fama da matsalar jami'anta da ake kamawa da satar kudade da kadarori da aka kwato daga hannun jami'an gwamnati da masu rashawa da cin hanci. Wasu daga cikin jami'an hukumar an koresu daga aiki inda wasu kuma aka dakatar dasu dan yin bincike kan zargin satar kayan da aka basu kula wa dasu. Koda a shekarar data gabata, mutane 27 ne aka kora daga EFCC saboda satar kudaden da aka basu ajiya Hakanan kakakin EFCC a ranar 6 ga watan Janairu 2025 ya tabbatar da cewa suna binciken batan dala $400,000 da ake zargin wani jami'in hukumar ya sace. Hakanan akwai jami'an hukumar 10 da aka dakatar a reshenta na jihar Lagos inda ake zarginsu da satar Gwal da darajarsa ya kai na Naira Biliyan 1, da kudade dala $350,000 zuwa $400,00 wanda duka suka...
Kaso 77 na matan Najeriya na Amfani da man kara hasken fata>>Inji WHO

Kaso 77 na matan Najeriya na Amfani da man kara hasken fata>>Inji WHO

Duk Labarai
Kungiyar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cewa, kaso 77 cikin 100 na matan Najeriya na amfani da man kara hasken fata wanda ake cewa Bleaching. Hakan bmna zuwane yayin da wani rahoto yace ba matan ba kadai yanzu hadda kananan yara a Najeriya ana shafa musu man kara hasken fata. Rahoton na WHO yace mayukan kara hasken fata ne mafiya ci gaba da aka fi sayarwa a tsakanin mayukan shafawa a Duniya baki daya. Hakan na faruwa ne duk da irin illar da irin wadannan mayukan shafawar ke dauke da ita wanda ya hada da ragewa fata karfi da garkuwar da take dashi da kuma kara hadarin kamuwa da cutar daji.
Ana zargin DPO da yin lalata da karamar yarinya me shekaru 15 da aka tsare a fishin ‘yansanda a Katsina

Ana zargin DPO da yin lalata da karamar yarinya me shekaru 15 da aka tsare a fishin ‘yansanda a Katsina

Duk Labarai
Ana zargin DPO din 'yansanda dake Dutsinma, CSP Bello Gusau da yiwa karamar yarinya lalata wadda ake tsare da ita a ofishin 'yansanda. Wata kungiyar kare hakkin bil'adama HRTI ce shigewa yarinyar gaba inda suke nema mata hakkinta. Shugaban kungiyar Kwamared Maiyasin ya bayyana cewa sai da suka yi bincike suka tabbatar da cewa DPO din ya dauki yarinyar ya je ya kwana da ita a gidansa, ba'a ofishin 'yansanda ta kwana ba kamin su dauki mataki. Kwamishinan 'yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Musa ya bayyana cewa an dakatar da DPO din inda aka fara bincike kan lamarin.
Ba zamu iya ci gaba da biyan tallafin wutar Lantarki ba>>Gwamnatin Tarayya

Ba zamu iya ci gaba da biyan tallafin wutar Lantarki ba>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Shugaban kwamitin dake kula da yanda Gwamnatin tarayya ke kashe kudi, James Faleke ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ba zata iya ci gaba da biyan kudij tallafin wutar lantarki ba. Ya bayyana hakane yayin da ma'aikatar kudi ke bayanin yanda zata kashe kudadenta a shekarar 2025. Gwamnatin tarayya dai ta ware Naira biliyan 705 dan biyawa 'yan Najeriya tallafin wutar a shekarar 2025. Saidai Falake yace sam babu bukatar hakan musamman lura da yanda farashin wutar labtarkin ke ta kara tashi kullun da kuma yanda darajar Naira ke ci gaba da faduwa.
An kama wannan tsagerar da ta sha Alwashin zin lalata da maza 100 a rana daya

An kama wannan tsagerar da ta sha Alwashin zin lalata da maza 100 a rana daya

Duk Labarai
Hukumomi a kasar Turkiyya sun kama wata tsagera data yi suna wajan nuna tsiraici me suna Ezra Vandan 'yar shekaru 23 saboda Alwashin da ta sha na yin lalata da maza 100 a cikin awanni 24. 'Yansanda a birnin Istanbul sun kama matar ne bisa zargin cewa abinda take da niyyar aikatawa ya sabawa al'adar kasar kuma zai jawo gurbacewar tarbiyya. Matar dai ta yi aniyar daukar bidiyon lalatar da zata yi kai tsaye tare da nunawa Duniya. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da wata tsagerar me suna Brit Bonnie Blue ta yi ikirarin yin lalata da maza guda 1000 a rana daya.
Bamu yadda da karin kudin kiran waya ba, muna kiran ‘yan Najeriya su kauracewa kamfanonin sadarwa>>NLC

Bamu yadda da karin kudin kiran waya ba, muna kiran ‘yan Najeriya su kauracewa kamfanonin sadarwa>>NLC

Duk Labarai
Kungiyar Kwadago NLC ta bayyana cewa, bata yadda da karin kudin kiran waya na kamfanonin sadarwa ba da aka yi zuwa kaso 50 cikin 100. Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana haka ranar Laraba ga manema labarai inda yace hakan ya zo ne a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa gashi kuma babu kudin sayen kayan masarufi. Joe Ajaero yace amfani da kafafen sadarwa ya zamarwa 'yan Najeriya dole ta yanda suke kashe akalla kaso 10 cikin 100 na kudin shigarsu akan harkar sadarwa. Joe Ajaero yace kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da wannan lamari inda yace basu amince dashi ba.
Komai Nawa ya koma na mata, duk me kokwanto ya zo in nuna masa>>Inji Dan Daudu Bobrisky bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya haramta Luwadi

Komai Nawa ya koma na mata, duk me kokwanto ya zo in nuna masa>>Inji Dan Daudu Bobrisky bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya haramta Luwadi

Duk Labarai
Shahararren me shigar mata da daudanci a Najeriya wanda aka fi sani da Bobrisky ya yi magana bayan da shugaban kasar Amurka ya haramta luwadi da Madigo. Bobrisky yayi suna sosai wajan daudanci inda har a karshe yace ya bar Najeriya da zama saboda takurawar da aka masa. A ranar da aka rantsar dashi a matsayin shugaban kasar Amurka a karo na 2, Donald Trump ya bayyana cewa, jinsin maza da mata kawai suka sani a Amurka. A rubutun da yayi a shafinsa na sada zumunta, Bobrisky ya bayyana cewa, Ya ji ance shugaban Amurka, Donald Trump yace maza da mata kawai ya sani, amma shi gashi ya koma mace, yace idan ana so, zai bude aga hujja.
Za’a samu saukin rayuwa, kayan masarufi zasu sauka kasa>>Inji Gwamnatim tarayya

Za’a samu saukin rayuwa, kayan masarufi zasu sauka kasa>>Inji Gwamnatim tarayya

Duk Labarai
Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa a shekarar 2025 za'a samu saukin hauhawar farashin kayan masarufi. Yace alkaluman hauhawar farashin kayan masarufi zasu yi kasa zuwa kaso akalla 15 cikin 100 inda a yanzu suke a maki 34.8 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana. Ya bayyana hakane a Abuja ranar Litinin yayin kaddamar da kwamitin kula da kudi inda yace zasu cimma burin samun kudin shiga na Naira Tiriliyan 47.9 da suka saka a gaba a shekarar 2025. Yace babban bankin Najeriya, CBN ya saka burin rage hauhawar farashin kayan abinci zuwa kaso 15 cikin 100 a cikin shekarar nan kuma zasu dage dan cimma wannan buri.
Kalli Bidiyo: An hango me kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg na kallon Nonuwan matar me kamfanin Amazon a wajan taron rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasa

Kalli Bidiyo: An hango me kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg na kallon Nonuwan matar me kamfanin Amazon a wajan taron rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasa

Duk Labarai
Abinda me kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg yayi a wajan rantsar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya dauki hankula. Bidiyo ya nuna Mark Zuckerberg yana kallon nonuwan matar me kamfanin Amazon, watau Jeff Bezos. Lamarin ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke ganin itama bai kamata ta yi irin wannan shigar ta nuna kirji ba a wajan taro me muhimmanci irin wannan ba. https://www.tiktok.com/@musicedits304/video/7462128836424092946?_t=ZM-8tFH4LH9YBh&_r=1 Kalli Bidiyin anan Manyan masu kudin Duniya da suka mallaki kamfanonin sadarwa dana kasuwanci irin su Facebook, Amazon, Tiktok, Apple da saransu duk sun halarci wajan taron rantsar da Donald Trump.
Donald Trump ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Amurka na 47

Donald Trump ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Amurka na 47

Duk Labarai
Donald Trump ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Amurka na 47, bayan nasarar da ya yi a zaɓen shugaban ƙasar na 2024. An rantsar da Donald Trump ne a cikin ginin Majalisar Dokokin ƙasar na Capitol, karon farko a cikin shekaru. Gabanin Trump, an rantsar da mataimakinsa, kuma tsohon mai sukarsa, JD Vance. Jim kaɗan bayan shan ranstuwa, Trump ya sanar da wasu tsauraran matakai da zai ɗauka, musamman a ɓangaren tsaron iyaka da kuma rage kwararar baƙi zuwa ƙasar. Wani abin kuma shi ne yadda Trump ya riƙa sukar magabacinsa, Joe Biden, a gabansa, jim kaɗan bayan shan rantsuwa. Donald Trump ya dawo kan mulki ne bisa alƙawarin kawo tsauraran sauye-sauye waɗanda suka sha bamban da na Biden. A jawabinsa na farko, Trump ya ce ''Sabon babin ci gaban Amurka zai fara ne daga yau''. '...