Saturday, December 6
Shadow
Da Duminsa: Sojoji 2 cikin wadanda akw zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki sun tsere an nemesu an rasa

Da Duminsa: Sojoji 2 cikin wadanda akw zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki sun tsere an nemesu an rasa

Duk Labarai
Rahotanni sun ce 2 daga cikin sojojin da ake zargi da yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Jhuyin mulki sun tsere. Jaridar Cable ce ta ruwaito labarin inda tace cikinsu akwai JM Ganaks wanda ke da mukamin Major da lambar aiki N/14363 sannan yana aiki ne a Jaji. Sannan akwai G Binuga wanda shi kuma Captai ne me lambar aiki N/167722 wanda dan Asalin jihar Taraba ne. Thecable tace zuwa yanzu akwai sojoji 30 da ake tsare dasu ake tuhumarsu bisa zargin yunkurin yin Jhuyin mulkin.
Da Duminsa: Kwanaki kadan da Bayyanar rahotannin yunkurin Jhuyin mulki, An sake canjawa sojojin Najeriya wajan aiki

Da Duminsa: Kwanaki kadan da Bayyanar rahotannin yunkurin Jhuyin mulki, An sake canjawa sojojin Najeriya wajan aiki

Duk Labarai
Rahotanni sun ce hukumar sojojin Najeriya ta canjawa manyan sojoji 60 guraren aiki. Hakan na kunshe a wata sanarwa ne data bayyana a yau 30 ga watan October inda aka ce sojojin su koma sabbin guraren aikin da aka turasu nan da 3 ga watan Nuwamba. Tun ranar Juma'ar data gabata ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da canjawa manyan sojojin wajan aiki. Hakan na zuwane bayan bayyanar rahotanni dake cewa an yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.
Da Duminsa: cikin sojojin da ake zargi da shiryawa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, SB Adamu ne aka baiwa aikin Shekye Malam Nuhu Ribadu

Da Duminsa: cikin sojojin da ake zargi da shiryawa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, SB Adamu ne aka baiwa aikin Shekye Malam Nuhu Ribadu

Duk Labarai
Rahotanni sun ce a cikin sojojin da aka kama da zargin yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, SB Adamu ne aka baiwa aikin Shekye babban me baiwa shugaban kasa, shawara kan tsaro, watau Malam Nuhu Ribadu. Shi dai SB Adamu an kaishi aiki ofishin Malam Nuhu Ribadu wanda kuma aka bashi aikin ya kula dashi ya shekye. Kafar Thecable ce ta ruwaito labarin inda tace wata majiyar gidan soji ce ta sanar da ita hakan. Tace ba kamar yanda ake yadawa cewa sauran sojojin da suka shirya juyin mulkin a ofishin me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro suke ba, tace SB Adamu ne kadai a ofishin. Majiyar sojin tace wannan alamace dake nuna cewa masu juyin mulkin sun kama manyan sojoji sosai a gidan sojan.
Da Duminsa: Sanata Natasha Akpoti ta shirya da Sanata Godswill Akpabio har ma ta gayyaceshi…

Da Duminsa: Sanata Natasha Akpoti ta shirya da Sanata Godswill Akpabio har ma ta gayyaceshi…

Duk Labarai
Rahotanni daga majalisar dattijai na cewa akwai alamu masu karfi dake nuni da cewa, an shirya tsakanin Sanata Natasha Akpoti da Sanata Godswill Akpabio. Hakan ya bayyana ne bayan da sanata Natasha Akpoti ta gayyaci Sanata Godswill Akpabio zuwa mazabarta Ihima, Kogi da kaddamar da wani aiki da ta yi. Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta takardar gayyatar a zauren majalisar Dattijai ranar Alhamis inda tace tana gayyatarshi da sauran sanatocin zuwa kaddamar da aikin. A baya dai Sanata Natasha Akpoti ta zargi Sanata Godswill Akpabio ta neman ta da lalata wanda lamarin ya jawo zazzafar Muhawara.
Kalli Bidiyon: Babban Yaron Nazir Ahmad Sarkin Waka, Abba C Sale yace ya janye maganar da ya taba yi cewa yana samun Naira Miliyan 5, Yace kada wanda ya sake mai maganar in ba haka ba zai dauki mataki

Babban yaron Nazir Ahmad Sarkin Waka, Abba C Sale yace ya janye maganar da ya taba yi a baya wadda ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta. Abba ya taba cewa, yana samun Naira Miliyan 5 a wata wanda hakan yasa mutane sukaita cece-kuce inda wasu da dama suka rika karyatashi. Idan ya wallafa Bidiyo akan rika rubuta masa 5M a comment kuma ya sha yin gargadin cewa baya so amma da yawa basu daina ba. A yanzu dai yace ya janye waccan magana kuma kada a sakw masa maganar idan ba haka ba zai dauki mataki. https://www.tiktok.com/@abbacsale2/video/7567051318188133653?_t=ZS-90zDPeqx1Bh&_r=1
Kalli Bidiyon: Sabuwar Wakar Naziru Sarkin Waka da masu rawarsa suka saka kayan ‘yansanda data jawo cece-kuce

Kalli Bidiyon: Sabuwar Wakar Naziru Sarkin Waka da masu rawarsa suka saka kayan ‘yansanda data jawo cece-kuce

Duk Labarai
Wata sabuwar waka da Naziru Sarkin Waka yayi i da aka ga 'yan Rawarsa sanye da kayan 'yansanda ta jawo cece-kuce. Wasu dai na ganin cewa hakan rashin ganin girman 'yansanda ne inda wasu kuma ke cewa ba komai bane. Danna nan dan kallon Bidiyon wakar https://www.tiktok.com/@sadeeqking__/video/7566789692826438924?_t=ZS-90zBtby2q3t&_r=1