Sunday, March 8
Shadow
Farashin kayan Abinci zasu tashi a Najeriya saboda babu Network a bankuna

Farashin kayan Abinci zasu tashi a Najeriya saboda babu Network a bankuna

Duk Labarai
Matsalar rashin Network a bankunan Najeriya yasa ake tsammanin samun hauhawar farashin kayan abinci. Manyan jiragen ruwa sun kawo abunci kala-kala daga kasashen waje inda suke gabar tekun Legas suna jira a kammala duk takardunsu na haraji wadanda suka makale a bankuna saboda matsalar rashin Network. Rahoton daga jaridar Naigerian Tribune yace kayan auna kan ruwa inda masu kayan suke jiran takardunsu, inda matsalar take shine duk kwana daya da kayan suka kara sai mai kaya ya sake biyan kudin haya na Kwantena da kayansa suke ciki. Wakilin masu kawo kayan Mr. Frank Ogunojemite ya bayyana cewa, suna bukatar gwamnati ta rika basu wani dauki ko tallafi a irin wannan yanayi saboda ba laifinsu bane. Yace duka kudin hayar da suka biyawa kayan nasu akan wanda zasu sayi kayan zasu fanshe...
Kalli Hotuna da Bidiyo sun bayyana na wannan dan kasuwar yana lalata da matan manyan mutane

Kalli Hotuna da Bidiyo sun bayyana na wannan dan kasuwar yana lalata da matan manyan mutane

Duk Labarai
Wannan mutumin wanda dan kasuwane dan kasar Equatorial Guinea ya shiga idon duniya bayan da bidiyo sama da guda 400 suka bayyana inda suka nunashi yana lalata da mata. Wani abin karin ban mamakin shine cikin matan da yayi lalata dasu hadda matan aure da kuma matan manyan 'yansiyasa na kasar. Rahotanni sun ce cikin matan manyan mutanen da yayi lalata dasu akwai matar ministan shari'a na kasar, da matan sauran ministoci. Akwai kuma matar kaninsa. Da matar kawunsa. Da matar Faston cocin da yake halarta. Da matar uban gidansa. Da matar me tsaron lafiyarsa. Da abokan kanwarsa da dai sauransu. Rahoton yace mutumin baya amfani da kwandam wajan yin lalata da matan. Tuni dai an garzaya dashi kotu inda kotun tace a je a gwadashi ko yana dauke da cutar dake yaduwa ta...
Mu talakawa ne ba za mu iya yin belin yaranmu ba – Iyayen yaran da aka tsare

Mu talakawa ne ba za mu iya yin belin yaranmu ba – Iyayen yaran da aka tsare

Duk Labarai
Iyalan yaran da aka tsare kan zargin yin zanga-zanga a Kano da Kaduna sun koka kan a yi masu adalci. Iyaye da ƴan uwan yaran sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa yaran su basu da hannu kan zargin da ake masu na cin amanar ƙasa, inda suka roƙi hukumomi da su sakar masu ƴaƴansu. Mutanen sun bayyyana cewa su talakawa ne basu da ƙarfin da za su cika dukkan sharuddan beli da kotu ta bayar a Abuja. An kama masu zanga-zangar 76 a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa daga ɗaya zuwa 10 ga watan Agusta, inda aka gurfanar da su a gaban babbar kotun Abuja a ranar Juma'a. Al'umma a faɗin Najeriya na ci gaba da bayyana takaicinsu kan bidiyon yaran da aka gurfanar gaban kotu daga wasu jihohin arewacin ƙasar. Yaran waɗanda gwamnati ta zarga da cin amanar ƙasa, sun bayyan...
Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci

Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci

Duk Labarai
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da sababbin ministocin da ya naɗa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsar da su, Tinubu ya ce, "mun fara ƙoƙarin dawo da tattalin arzikinmu cikin hayyacinsa," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "muna kan tafarki mai kyau domin cika burinmu, ba ma don mu kaɗai ba, har da jin daɗin ƴaƴanmu da jikokinmu." Shugaban ƙasan ya ce duk da ƙalubalen da ake fuskanta, ana ci gaba da aikin inganta tattalin arzikin ƙasar. Sai ya bayyana wa sababbin ministocin cewa an zaɓo su domin su bayar da gudunmuwarsu domin ceto ƙasar. A ranar 23 ga Oktoba ce Tinubu na cire wasu ministoci guda biyar, sannan ya naɗa wasu guda bakwai. A ranar 30 ga Oktoba kuma Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da sababbin ministocin wato...
Rikicin Jam’iyyar NNPP: Gwamna Abba Gida-Gida yaki daga waya bayan sa Kwankwaso ya kirashi

Rikicin Jam’iyyar NNPP: Gwamna Abba Gida-Gida yaki daga waya bayan sa Kwankwaso ya kirashi

Duk Labarai
Rikicin cikin gida na jam'iyyar NNPP na kara kazanta bayan sa rahotanni suka bayyana cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yaki daukar wayar Kwankwaso bayan da ya kirashi kuma yaki halartar taron ganawa da Kwankwason. Sarar Abba Tsaya da kafarka wadda ke nufin Abba ya raba gari da Kwankwaso na kara samun yaduwa a siyasar ta Kano. Jam'iyyar ta rabu gida biyu inda wasu ke son a hada kai da APC a matakin tarayya, wasu kuma sun je kotu suna son a basu iko da shugabancin jam'iyyar dan kwace ragamarta daga hannun Kwankwaso. Rahoton jaridar Daily Nigerian ya bayyana wanda ke kokarin ganin sun zuga Abba ya bijirewa Kwankwaso kamar haka: Sakataren Gwamnatin Jihar, Baffa Bichi. Kwamishinan Tafiye-tafiye, Mohammed Diggol. Kwamishinan Ilimi, Umar Doguwa. Sanatan dake wakilta...
A karshe dai da daudu Bobrisky ya samu fita daga Najeriya bayan da aka kamashi

A karshe dai da daudu Bobrisky ya samu fita daga Najeriya bayan da aka kamashi

Duk Labarai
Shahararren dan daudu, Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky ya samu fita daga Najeriya kwanaki kadan bayan da aka kamashi amma aka bayar da belinsa. Ana dai zargin Bobrisky da laifin rashawa da cin hanci ne Bobrisky ya bayyana fitarsa daga Najeriya ne zuwa kasar waje ta hanyar shafinsa na sada zumunta saidai bai fadi kasar da ya tafi ba. Yace Naira Miliyan 30 ya kashe wajan siyan tikitin jirgin First Class. A baya dai an ga yanda aka kama Bobrisky aka fitar dashi daga cikin jirgi da karfin tsiya a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Birnin Landan na kasar Ingila. Daga baya ta bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ce ta kamashi. Daga baya an daukeshi daga Legas zuwa Abuja. Kuma hukumar ta EFCC ta bayyana cewa ta kamashine saboda yaki amsa gayyatar d...
Najeriya ta zo ta 5 a Duniya wajan yawan masu amfani da kafafen sada zumunta

Najeriya ta zo ta 5 a Duniya wajan yawan masu amfani da kafafen sada zumunta

Duk Labarai
Najeriya ta haura zuwa matsayi na 5 a Duniya a cikin kasashen da suka fi amfani da kafafen safa zumunta. Kafafen Cable.co.uk da We Are Social ne suka bayyana hakan a wata sanarwa da suka fitar. A bayanin an ga cewa, 'yan Najeriya na yin akalla awanni 3 da mintuna 23 akan kafafen sada zumunta. Kasar Kenya ce ta zo ta daya sai kasar Kasar Africa ta kudu ke take mata baya inda kasar Brazil ta zo ta uku sai kasar Philippines ta zo ta 4. Ga jadawalin kasashen da suka fi yawan Amfani da kafafen sadarwar zamanin kamar haka: Kenya – 03:43 South Africa – 03:37 Brazil – 03:34 Philippines – 03:33 Nigeria – 03:23 Colombia – 03:22 Chile – 03:11 Indonesia – 03:11 Saudi Arabia – 03:10 Argentina – 03:08 Mexico – 03:04 Malaysia – 02:48 Ghana – 02:43 Egy...
Na yadda da shawarar daka bani cewa in rika tausayawa ‘yan Najeriya>>Tinubu ya gayawa Atiku

Na yadda da shawarar daka bani cewa in rika tausayawa ‘yan Najeriya>>Tinubu ya gayawa Atiku

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa ya amince da shawarar da dan takarar shugaban masa na jam'iyyar PDP a shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bashi ta cewa ya rika tausayawa da tallafawa talakawa saboda matsin tattalin arzikin da ake ciki. Shugaban kasar ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga a sanarwar da ya fitar ta mayar da martani ga Atikun akan shawarar da ya baiwa Tinubun ta cewa ya dauki tsare-tsaren sa dan gyara kasa da fitar da mutane daga matsin rayuwar da suke ciki. Tinubu...
Tsadar Rayuwa tasa Tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ya ragu da kaso 60 a Najeriya

Tsadar Rayuwa tasa Tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ya ragu da kaso 60 a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa tafiye-tafiye zuwa kasashen waje daga Najeriya ya ragu sosai saboda tsadar rayuwa. Mutanen da aka saba gani a filayen jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da na Murtala Muhammad dake Legas sun ragu sosai da kaso 60 cikin 100. Rahoton na jaridar Leadership yace hauhawar farashin dalar Amurka na daga cikin abubuwan da suka jawo wannan matsala. A baya dai da rayuwa ke da sauki ana samun 'yan Najeriya dake zuwa kasashen waje yin hutun karshen mako ko hutun nishadi da sauransu. Rahoton yace a shekarar 2023 mutane miliyan 2.4 ne suka fita daga Najeriya zuwa kasashen waje inda a shekarar 2024 da muke ciki kuma mutane 816,000 me suka fita. Rahoton yace tikitin jirgin sama zuwa kasar Amurka wanda a baya ana sayansa akan Naira 350,000 a yanzu ya koma Nai...
Da kyar muke samun na Abinci>>Inji Mazauna Abuja

Da kyar muke samun na Abinci>>Inji Mazauna Abuja

Duk Labarai
Mazauna babban birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa da kyar suke samun na abinci saboda tsadar rayuwar da ake ciki. Hakanan sun kuma koka da tsadar kudin ababen bayan wanda hakan ya biyo bayan kara farashin litar man fetur ne da aka yi. Mutanen sun zanta da kamfanin dillancin labaran Najeriya ne NAN inda suke kokawa da irin halin matsin rayuwar da suke ciki. Sun yi roko ga gwamnatoci a kowane mataki dasu dauki matakan ragewa al'umma radadin rayuwa da suke ciki.