Ku sake Tunani, Musulunci bai farlanta kulle makarantu ba a lokacin azumin watan Ramadana>>Ministar Ilimi, Suwaiba Ahmad ta jawo hankalin Gwamnonin Arewa
Karamar Ministar Ilimi, Suwaiba Ahmad ta jawo hankalin Gwamnonin Arewa da cewa, su sake tunani kan kulle makarantu da suka yi saboda zuwan Azumin watan Ramadana.
Tace musulunci bai farlanta kulle makarantu ba a yayin azumin watan Ramadan.
Ta bayyana hakane a yayin wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na ChannelsTV.
Jihohin Kebbi, Bauchi, Katsina da Kano ne suka kulle Makarantu saboda zuwan Azumin watan Ramadana inda suka ce sun bayar da wannan hutu ne dan baiwa dalibai damar Azumtar watan da yin Ibada yanda ya kamata saidai hakan ya jawo cece-kuce.
A ci gaba da jawabinta, Minista Suwaiba ta bayyana cewa, A zamanin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) har yaki yaje a cikin watan Ramadana dan haka Azumi bai hana mutum gudanar da ayyukansa na yau da kullun.
Ta...








