Yanda na hadu da matata na musuluntar da ita>>Tsohon Shugaban kasa, IBB yayi bayani dalla-dalla
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB ya bayar da labarin yanda ya hadu da matarsa Maryam a cikin littafin tarihin rayuwarsa.
Babbangida yace asalin sunan matarsa shine Maria Okogwu kamin daga baya ta musulunta ta koma Maryam.
yace sun dade suna abuta kamin ya aureta.
Yace babban dalilin da yasa yayi aure shine an taba harbinsa a kirji aka kwantar dashi a gadon Asibiti a Legas, anan ne yayi tunanin cewa ya kamata ace yayi aure.
Yace yana kan gadon Asibiti ya rika tunanin irin 'yan matan da yake dasu da kuma da wacece cikinsu ya kamata ace yayi rayuwa a matsayin matarsa?
Yace anan tunanin Maryam ya fado masa, yace a lokacin tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon shima ya auri matarsa, Victoria inda abin ya kara karfafa masa gwiwa.
Yace yan...







