Sunday, December 21
Shadow
Kalli Yanda aka gano wani Kirista da yayi amfani da hoton makabartar Musulmai da cewa Kiristane da aka Shyekye dan ya jawo hankalin kasar Amurka

Kalli Yanda aka gano wani Kirista da yayi amfani da hoton makabartar Musulmai da cewa Kiristane da aka Shyekye dan ya jawo hankalin kasar Amurka

Duk Labarai
Wannan hoton wata makabartar musulmai ce da wani Kirista yayi amfani da shi da nuna irin yanda a cewarsa aka kashe mutane da yawa a jihar Benue. Saidai musulmai da yawa sun ce wannan makabartar Musulmi ce. https://twitter.com/iambabangida_/status/1989723500848771543?t=rZWFLzzhU87whLXjREFbgA&s=19
Nima ban amince da kirar da akawa Wike daga PDP ba>>inji Gwamnan jihar Flato>>Caleb Mutfwang

Nima ban amince da kirar da akawa Wike daga PDP ba>>inji Gwamnan jihar Flato>>Caleb Mutfwang

Duk Labarai
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa, bai goyi bayan korar da akawa ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam'iyyar PDP ba. Ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Gyang Bere. Hakan na zuwane bayan da PDP ta sanar da korar Wike da wasu jiga-jigan jam'iyyar daga cikin jam'iyyar. Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ba a tattauna wannan masala a taron gwamnonin jam'iyyar ba hakanan ba'a san da ita ba dan haka shi baya goyon bayan korar Wike.
Kasar Angola ta karrama Tsohon Shugaban kasa, Janar Murtala Ramat Muhammad saboda taimakon da ya bayar wajan ci gaban Nahiyar Afrika

Kasar Angola ta karrama Tsohon Shugaban kasa, Janar Murtala Ramat Muhammad saboda taimakon da ya bayar wajan ci gaban Nahiyar Afrika

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Angola na cewa kasar ta karrama tsohon shugaba Mulkin soja na Najeriya, Janar Murtala Ramat Muhammad saboda taimakon da ya bayar wajan ci gaban Nahiyar Afrika Hakanan cikin wadanda aka karamma akwai tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Farfesa Ibrahim Gambari. An yi bikin karramawar ne a babban birnin kasar me suna Luanda.
Kalli Bidiyo: Wani mutum ya kai Sheikh Dr. Ahmad Gumi Kotu inda yace ya rike masa matarsa tun watan Satumba ta zauna a gidan Sheikh Gumi taki komawa gidansa

Kalli Bidiyo: Wani mutum ya kai Sheikh Dr. Ahmad Gumi Kotu inda yace ya rike masa matarsa tun watan Satumba ta zauna a gidan Sheikh Gumi taki komawa gidansa

Duk Labarai
Wani mutum me suna Alhaji Nasir Musa Idris a jihar Kaduna ya kai karar Babban malamin dadi Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi kotu inda yake zargin malamin da rike masa mata tun watan Satumba. Mutumin wanda yake auren balarabiya yace matar tasa ta yi yaji ta koma gidan malan Gumi da zama kuma ya hadu fa malam din yace yana son matarsa ta koma gida amma abu yaci tura. Ga cikakken bayaninsa anan: https://www.tiktok.com/@faruq_abuja/video/7572863094666415378?_t=ZS-91QoCDzJl7B&_r=1
Jam’iyyar PDP ta kori Nyesom Wike

Jam’iyyar PDP ta kori Nyesom Wike

Duk Labarai
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta sanar da korar ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu jiga-jiga daga cikinta, saboda abin da ta kira yi wa jam'iyya zagon-ƙasa. Cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta ɗauki matakin ne domin kawo haɗin kai da ladabtarwa a jam'iyyar da kuma mayar da hankali ga zaɓukan 2027 masu zuwa. Sauran mutanen da jam'iyyar ta kora sun haɗar da Samuel Anyanwu da Kamaldeen Ajibade da Ayo Fayose da Austin Nwachukwu da kuma wasu. Sanarwar ta ce matakin ya samu amincewar mafiya rinjayen wakilan jam'iyyar da ke halartar babban taronta na ƙasa da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Kalli Bidiyo: Kungiyar Tsaffin Sojojin Najeriya sun yi kira ga shugaba Tinubu ya sauke Wike daga mukamin Minista

Kalli Bidiyo: Kungiyar Tsaffin Sojojin Najeriya sun yi kira ga shugaba Tinubu ya sauke Wike daga mukamin Minista

Duk Labarai
Kungiyar Tsaffin Sojojin Najeriya ta nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya sauke Ministan Babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike daga mukamin Minista. Kungiyar tace Wike na takawa da wulakanta mutane da yawa inda ta nemi ko da ba'a saukeshi ba a canja masa ma'aikata. https://twitter.com/emmaikumeh/status/1989732131309064632?t=uEsh6BIihZvXReiaXN7o_Q&s=19 Hakan na zuwane bayan da Wike yayi dambarwa da sojan Ruwa, AM. Yerima akan wani fili da akw rigima akanshi a Abuja.
Kalli Bidiyo: Gwamnan Katsina, Dikko Raddah na shan suka bayan da yace Likitocin Najeriya basu da kishi suna fita aiki kasashen waje maimakon su tsaya Najeriya su taimakawa ‘yan uwansu

Kalli Bidiyo: Gwamnan Katsina, Dikko Raddah na shan suka bayan da yace Likitocin Najeriya basu da kishi suna fita aiki kasashen waje maimakon su tsaya Najeriya su taimakawa ‘yan uwansu

Duk Labarai
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Raddah ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda likitoci ke tserewa daga Najeriya suna zuwa kasashen waje aiki. Gwamnan yace abin takaici shine a baya likitoci mata daga Najeriya basa fita kasashen waje yin aiki amma a yanzu likitoci mata daga Arewa suma sun bi sahu. Yace irin wadancan kasashe mutanensu ragwayene basa iya karatun aikin Likita shiyasa suke zuwa su baiwa likitocin Najeriya Albashi me tsoka dan su daukesu. Ya zargi Likitocin da rashin kishin al'ummarsu. https://twitter.com/Yantumakii/status/1989583505148244410?t=JOBFJyaDyxiUrKcFDCejIA&s=19 Saidai hakan ya jawowa Gwamnan suka inda wasu ke cewa ba'a kula da hakkokin Likitocin ne sannan ba'a biyansu albashi me kyau shiyasa.