Hukumar Hisbah ta Kano ta kama mutane 25 inda namiji ke shirin auren Namiji a Kano
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama mutane 25 dake shirin kulla auren Namiji da Namiji.
An kamasu ne a Fatima Event Center dake Hotoro ranar Lahadi.
Mataimakin Kwamanda na Hisbah, Mujahedeen Aminudeen ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Yace daga cikin wadanda aka kama akwai maza 18, mata 7.
Yace sun samu bayanan sirri ne kan daura auren 'yan Luwadin.








