Maganin pimples da black spot
Ana samun maganin pimple da black spot a gida ba tare da amfani da maganin asibiti ba.
Hanyoyin magance pimples da black spot sun hada da:
Amfani da Aloe Vera: Ana samun ruwa ko man Aloe Vera wanda ba'a hadashi da komai ba a shafa a fuska wanda yana maganin pimples da black spot sosai.
Idan ba'a samu na kemis ba, ana iya hadawa a gida ta hanyar yanko ganyen Aloe vera a fere koren bayan a tatso ruwan a rika shafawa a fuska.
A lura idan fuska ta nuna alamar reaction, sai a daina amfani dashi a tuntubi likita, idan kuma bata yi ba, sai a ci gaba har fuska ta dawo daidai. Ana iya karanta karin bayani kan amfanin Aloe vera wanda muka rubuta
Ana kuma amfani da Man Zaitun wajan magance matsalar pimples da black spot:
Ana amfani da man zaitun kai tsaye a shafa a fuska ba tare da ...


