Saturday, December 20
Shadow
Ya kamata a kama Soja Yerima a ladaftar dashi saboda abinda yawa Wike>>Inji Mujahid Asari Dokubo

Ya kamata a kama Soja Yerima a ladaftar dashi saboda abinda yawa Wike>>Inji Mujahid Asari Dokubo

Duk Labarai
Tsohon Tsageran Naija Delta, Mujahid Asari Dokubo ya bayyana cewa, ya kamata a kama sojan ruwa, Yerima a hukuntashi biyo bayan abinda yawa Wike. Asari Dokubo a sanarwar da ya fitar a wani Bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta yace ba wai yana goyon bayan Wike bane, yana goyon bayan gaskiyane. Yace a Najeriya ne kadai irin haka zata faru kuma sojan yasha Lallai.
Ba aikin Sojoji bane, bansan me yasa aka kai Soja, Yerima wajan ba>>Peter Obi yayi magana kan rykichin Wike da soja Yerima

Ba aikin Sojoji bane, bansan me yasa aka kai Soja, Yerima wajan ba>>Peter Obi yayi magana kan rykichin Wike da soja Yerima

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana damuwa kan abinda yace bai kamata ya faru ba. Peter Obi na magana ne akan rikicin da ya faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Sojan Ruwa Yerima. Peter Obi yace bai kamata ace an kai soja wajan harkar farar hula ba. Sannan shima Ministan Abuja Nyesom Wike abinda yawa sojan bai kamata ba. Ya bayyana hakane a sakon da ya fitar a shafinsa na X. Wike yace ya kamataba dauki matakin da ba za'a wulakanta jami'in tsaro ba hakanan itama hukuma ta gwamnati kada a wulakantata. Yace irin wannan abin baya koyawa matasa abu me kyau da kishin kasa.
Dalilin da yasa Soja Yerima ya ci banza kan abinda yawa Wike shine shi dan Arewane kuma Musulmi>>Inji Kirista Yohanna Nuhu

Dalilin da yasa Soja Yerima ya ci banza kan abinda yawa Wike shine shi dan Arewane kuma Musulmi>>Inji Kirista Yohanna Nuhu

Duk Labarai
Wani kirista daga jihar Adamawa me suna Yohanna Nuhu ya bayyana cewa, dalilin da yasa sojan ruwa Yerima ya ci banza kan dambarwarsa da Wike saboda shi dan Arewa ne. Yace 'yan Arewa Musulmai na da wata kariya ta musamman. Yace da dan Kudu ne yayi wannan abin da ya gane baida wayau. https://twitter.com/nuhuyohanna39/status/1988323576207077634?t=HyczG3RsgSyMJO0mngTC2g&s=19
Wata Sabuwa: Ji yanda wani barawo ya lallaba cikin gidan gwamnatin Kano ya sace daya daga cikin motocin tawagar Gwamna Abba Kabir Yusuf

Wata Sabuwa: Ji yanda wani barawo ya lallaba cikin gidan gwamnatin Kano ya sace daya daga cikin motocin tawagar Gwamna Abba Kabir Yusuf

Duk Labarai
Rahotanni sun ce wani barawo ya lababa cikin gidan Gwamnatin Kano ya sace daya daga cikin motocin dake bin ayarin tawagar Gwamnan, Kano Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida. Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a shafinsa na X inda ya kara da cewa wannan abin mamaki ne. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1988375087230447624?t=iv18fuHfAebDH5BWFffHjQ&s=19
Ji abinda Dan Gidan Wike ya cewa Sojan Ruwa Yerima

Ji abinda Dan Gidan Wike ya cewa Sojan Ruwa Yerima

Duk Labarai
Rahotanni na ta yawo a kafafen sada zumunta cewa, wai Dan gidan ministan Abuja, watau Nyesom Wike wanda bai dade da zama lauya ba, ya mayarwa da sojan ruwa Yerima da martani bayan sa in sar da suka yi shi da mahaifinsa. Rahoton wanda a kafafen sada zumunta ne kawai yake yawo ba'a tabbatar dashi ba yace dan gidan Wike yace zai yi maganin Soja Yerima. https://twitter.com/OfficialAzzaki/status/1988553415090164144?s=19 Tuni dai Ministan tsaro, Muhammad Badaru ya bayar da tabbacin baiwa Yerima kariya inda yace babu abinda zai sameshi.
Kalli Hotuna: Yanda wata ‘yar Kudu ta hada hotunanta dana Soja Yerima tace ta samu mijin aure

Kalli Hotuna: Yanda wata ‘yar Kudu ta hada hotunanta dana Soja Yerima tace ta samu mijin aure

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wata 'yar Kudu ta hada hotunanta daga soja Yerima da ya hana Wike shiga wani fili a Abuja inda tace ta samu mijin aure. https://twitter.com/cjayluv/status/1988552971626381442?t=7Zes9xGgDBvpVgeUWVNq4Q&s=19
Yaron Sojannan da muka lara dashi jiya sam bai da Kunya ga girman kan tsiya>>Inji Ministan Abuja, Nyesom Wike

Yaron Sojannan da muka lara dashi jiya sam bai da Kunya ga girman kan tsiya>>Inji Ministan Abuja, Nyesom Wike

Duk Labarai
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa Sojan Ruwa da ya hanashi shiga wani Fili Jiya bashi da da'a sannan yana da girman kai. Ministan ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Lere Olayinka a yayin da ake hira dashi a gidan talabijin na Channels TV. Yace abin mamaki shine yanda ko da aka kira shugaban sojoji CDS aka baiwa sojan bai wani nuna kaduwa ba. Lamarin rikicin Wike da Sojan ne babban labarin da ake ta tattaunawa akansa a fadin Najeriya.
Da Duminsa: Naji Dadin Abinda sojan Ruwa, Yerima yawa Ministan Abuja, Wike, yayi daidai, kuma zan tabbatar babu abinda ya samu sojan>>Inji Ministan Tsaro, Muhammad Badaru

Da Duminsa: Naji Dadin Abinda sojan Ruwa, Yerima yawa Ministan Abuja, Wike, yayi daidai, kuma zan tabbatar babu abinda ya samu sojan>>Inji Ministan Tsaro, Muhammad Badaru

Duk Labarai
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru ya bayyana goyon bayansa ga Matashin soja da ya tare Ministan Abuja, Nyesom Wike ya hanashi shiga wani fili a Abujan. Minista Badaru yace suna goyon bayan abinda Sojan yayi kuma sun jinjina masa sannan zasu bashi kariya saboda yana bakin aikinsa ne. Badaru yace zasu ci gaba da baiwa kowane soja Kariya da goyon baya muddin ya tsaya tsayin daka a bakin aikinsa. Hakan na zuwane bayan da a wajan rikicin ma sai da Wike ya kira shugaban sojoji, CDS.
Wata Sabuwa: An fara Kiraye-Kirayen a kori sojan daya tare Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesome Wike daga aiki

Wata Sabuwa: An fara Kiraye-Kirayen a kori sojan daya tare Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesome Wike daga aiki

Duk Labarai
Wasu musamman masu goyon bayan Ministan babban Birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike sun fara kiran a kori sojan ruwa da ya tare ya hana Ministan shiga wani fili a Abuja. Masu kiran dai na ganin abinda sojan yayi ya sabawa dokar kasa da kuma hana hukuma yin abinda ya dace. Sojan dai ya hana Wike Shiga wani fili ne a Abuja inda yace umarni aka bashi. Dole Wike ya fasa shiga filin inda ya tafi yana zage-zagi.
Kalli Bidiyon wasannin Barkwancin da aka fito dasu dan tsokanar Ministan Abuja, Nyesom Wike biyo bayan Tirka-Tirkar da yayi da sojan Ruwa

Kalli Bidiyon wasannin Barkwancin da aka fito dasu dan tsokanar Ministan Abuja, Nyesom Wike biyo bayan Tirka-Tirkar da yayi da sojan Ruwa

Duk Labarai
Biyo bayan Tirka-Tirkar data faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Sojan Ruwa, da ya hanashi shiga wani fili a Abuja, wasu sun rika yin wasannin Barkwanci dan tsokanar Ministan. Kalli Bidiyon wasannin Barkwancin kala-kala. https://twitter.com/PoojaMedia/status/1988549632952058286?t=ccTdSosFTEtPOikVvs0z_w&s=19 https://twitter.com/dammiedammie35/status/1988549108601106647?t=1gJd4DL3a_cKe1GOtSje8A&s=19