Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya mika sakon jaje ga dan Damben Najeriya, Anthony Joshua bisa hadarin mota da ya rutsa dashi.
Yace yanawa Anthony Joshua fatan samun sauki da gaggawa.
Sannan kuma ya mika sakon ta'aziyya ga wadanda suka rasu.
A yau, Litinin ne aka samu rahotannin hadarin dan daben Najeriya, Anthony Joshua wanda ya faru akan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Ya tsira da wasu ciwuka ba masu hadari sosai ba.
amma mutane 2 sun rasu a hadarin
Wannan Bidiyon yanda aka zakuloshi ne daga cikin motar bayan hadarin.
https://twitter.com/whitenigerian/status/2005629578598080815?t=0P7ZEeBhoQjYqesYow9sLg&s=19
https://twitter.com/General_Somto/status/2005621696422879360?t=7b5CzZrOwo0daMpQS2mQ6A&s=19
An ga wani Bidiyon da ya Nuna yanda jami'in DSS ya warce wayar wani dake daukar Bidiyon shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a legas.
Lamarin ya farune yayin bikin Eyo Festival.
https://twitter.com/Cleverlydey4u/status/2005569149658186191?t=nRCe_JQUq7jxN_ohm4e1yw&s=19
Shahararren dan damben Najeriya, Anthony Joshua ya tsallake rijiya da baya bayan da wani hadarin mota ya rutsa dashi.
Mutane 2 ne suka rigamu gidan gaskiya a hadarin.
hadarin ya farune ranar litinin akan hanyar legas zuwa Ibadan.
Anthony Joshua ya ji raunuka wanda basu da tsanani sosai.
Dan jam'iyyar APC a jihar Katsina, Bashir 'Yandoma ya roki Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya samar musu hulunan Kwano.
Yace dalili kuwa idan ba'a yi gyara ba, mutane zasu jefesu da duwatsu.
https://twitter.com/jrnaib2/status/2005566799954272541?t=DjgBwMTjvdP2oPaV3mTM6g&s=19
A baya dai an jefi 'yan majalisa a jihohin Zamfara, Kaduna, da jihar Kebbi.
'Yar Siyasa daga yankin Arewa, Naja'atu Muhammad ta yi zargin cewa Donald Trump na America ne ke mulkin Najeriya ba shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba.
Ta bayyana hakane a wata hira da DCL Hausa ta yi da ita.
Tace tunda Najeriya ta samu 'yancin kanta Najeriya bata taba yadda sojojin wata kasa sun shigo cikinta sun kawo hari ba sai lokacin Tinubu.
Tace a yanzu Turawa na kara yi mana Mulkin mallaka ne da aka yi a shekarun baya.
https://twitter.com/Arewa_Source/status/2005562060768501999?t=NMvj60w3oaEW40g2Ad9GPg&s=19
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, ba zai yadda yawa kowa takarar mataimakin shugaban kasa ba a 2027.
Yace dalili kuwa yana da wayau sosai kuma ba zai yadda duk wayonnan da Allah ya bashi ba ya kare da mataimakin shugaban kasa.
Yace yasan yanda zai gyara Najeriya dan haka takarar shugaban kasa zai nema.
Peter Obi ya kara da cewa har Tinubu yafi wayau.
Wannan wani hamshakin dan kasuwar Arewa ne daya dauki hankula biyo bayan lika Naira Miliyan 6 a cikin abinda hai wuce sakan 30 ba a wajan wani Biki.
Bidiyon nasa ya dauki hankula inda ake ta muhawara akai.
https://twitter.com/honest30bgfan_/status/2005388158314369068?t=I83aXy6ixi_f3HSevVbUGA&s=19
An ga Bidiyon wani basaraken Yarbawa sanye da sarkar Gwal yana rawa tare da wasu mata.
Bidiyon ya jawo muhawara da yawa inda wasu ke cewa, bai kamata a matsayinsa na basarake hakan bai dace ba.
Wasu kuma na tambayar ina ya samu kudin sayen Sarkar Gwal.
https://twitter.com/1RitaSunshine/status/2005549299430752395?t=gF5Tucd-GJy750yqYWeidQ&s=19
Rahotanni sun bayyana cewa, Naira Biliyan 200 da EFCC ke zargin Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami da sacewa, ya samesu ne daga kudaden bashin da babban bankin Najeriya, CBN ya baiwa manoma bashi lokacin Buhari.
Da kuma kudin Abacaha da aka dawo dasu Najeriya da kuma kudin Paris Club watau bashin da Gwamnatin Tarayya da gwamnoni suka ciwo.
Kafar The Cable tace ta samu cewa Abubakar Malami ya sa matarsa me suna Hajiya Bashir Asabe ta ci bashin na manoma har Naira Biliyan 4 wanda kuma bata biya ba.
A yanzu dai EFCC sun sakata cikin wadanda za'a gurfanar dasu a gaban kotun tare, a baya dai Hutudole ya kawo muku cewa akwai dan Abubakar Malami da shima yanzu EFCC ke tuhuma.
A bangaren Kudaden Abacha da aka karbo, lauyoyi turawa aka dauka suka yi aiki, amma rahotan yace Abubaka...