Monday, December 23
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Ko NLC na iya tilasta wa gwamnoni biyan albashi mafi ƙanƙanta?

Ko NLC na iya tilasta wa gwamnoni biyan albashi mafi ƙanƙanta?

Duk Labarai
Ƙungiyar ƙwadago NLC, ta Najeriya ta umarci ma'aikata a jihohin da gwamnatocinsu ba su aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙanƙanta ba da su shiryawa tsunduma yajin aiki nan da ranar 1 ga watan Disamba. Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewa jan ƙafar da jahohin ke ci gaba da yi wajen aiwatar da sabon tsarin albashin, wani nau’in cin zarafi da tauye hakki ne. Kungiyar kwadagon ta bayyana umurnin a cikin wata takardar bayan taro da shugabanta, Mista Joe Ajaero ya fitar, lokacin da suka kammala taron majalisar zartarwa ta ƙungiyar a birnin Fatakwal. NLC ta nuna da damuwa da rashin amincewa da jan kafar da wasu jihohin a Najeriya ke ci gaba da yi wajen aiwatar da tsarin albashin mafi karanci na 2024, kuma a cewar ta abu ne da ya saba ma doka, tare da taushe hakkin ma’akata musammam a wan...
Kungiyar IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

Kungiyar IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

Duk Labarai
Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya mai zaman kanta IPMAN ta ce mambobinta sun kammala cimma matsaya domin fara siyan tataccen man fetur daga matatar man Dangote kai tsaye. Sun bayyana haka bayan uwar ƙungiyar ta gudanar da taro da mambobinta domin bin bahasin yarjejeniyar da suka cimma da matatar da kuma hanyoyin samun man cikin sauki. Alhaji Zarma Mustapha, wani jigo a ƙungiyar ta IPMAN ya shaidawa BBC shirin da suka yi bayan tattaunawar da suka yi da shugabannin matatar a ranar litinin, inda ya ce wannan mataki da suka ɗauka zai haifar da wadatan man fetur a duk faɗin ƙasar. ''Ina bayar da tabbacin cewa muddin muka fara sayen mai kai-tsaye daga Dangote, ba za a rika samun ƙarancin man fetur a ƙasar nan ba, kuma muna sa ran cewa matatan gwamnati ma za su fara aiki nan bada j...

Tafarnuwa na maganin sanyi

Amfanin Tafarnuwa
Tafarnuwa na daya daga cikin abubuwan da aka dade ana amfani dasu wajan maganin gargajiya shekaru da yawa da suka shide a Duniya. Misali ana amfani da tafarnuwa wajan magance matsalar Ciwon zuciya, kara karfin tunani da magance ciwon mantuwa, tana karawa garkuwan jiki inganci, tana bayar da garkuwa ga cutar daji watau Cancer kala-kala. Amma a wannan rubutu, zamu yi maganane akan yanda ake amfani da Tafarnuwa wajan magance matsalar sanyi. Domin Maganin Sanyi ana tattauna Tafarnuwa ko a daddakata a rika sha. Hakanan bincike ya bayyana cewa, Cin Tafarnuwa yana baiwa mutum garkuwa daga kamuwa da ciwon sanyi da mura. Hakanan ko da mutum ya kamu da murar idan dai yana cin tafarnuwa kullun to murar ba zata dade ba zata warke, kamar yanda masana suka sanar. Masana sun ce ana son...
Atiku Abubakar ƙyashi yake yi wa Shugaba Tinubu – Fadar Shugaban Ƙasa

Atiku Abubakar ƙyashi yake yi wa Shugaba Tinubu – Fadar Shugaban Ƙasa

Duk Labarai
Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na shugaban ƙasa, muƙamin da ɗantakarar jam'iyyar PDP na muƙamin a 2023, ta ce yake ta faman nema har sau shida amma bai yi nasara ba. Fadar shugaban ta soki Atikun ne saboda shawarar da ya bayar ta sauye-sauyen tattalin arziƙi da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a wani saƙon Tweeter da ya sanya kwanan nan. Wani saƙo da ya fito daga fadar shugaban ƙasar, wanda mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ya ce, tun bayan da Atiku ya sha kaye a zaɓen 2023 a hannun Tinubu, ya fi mayar da hankali kan zagon-ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam'iyyarsa....
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Làkùràwà

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Làkùràwà

Duk Labarai
Mai riƙon muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Olufemi Oluyede ya nemi da a haɗakai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin arewa maso yamma. Janar Oluyede ya yi kiran ne a lokacin da ya kai ziyararsa ta farko a jihar Sokoto a jiya Lahadi, inda ya ziyarci sansanin dakarun da ke Tangaza da Illela. A kwanakin nan ne aka samu ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ta addabi yankin jihar Sokoto da Kebbi, wadda ake wa laƙabi da Lakurawa, da aka ce ta fito ne daga yankin Sahel. A ranar Juma'a al'ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi suka rasa mutum aƙalla 15 a wani artabu da suka yi da mayaƙan ƙungiyar ta Lakurawa. Yayin da ya ziyarci sansanonin Janar Oluyed, ya yaba wa sojojin tare da ba su tabbacin samun cikakken goyo...
Hukumar shari’a ta hukunta ma’aikatanta takwas a jihar Kano

Hukumar shari’a ta hukunta ma’aikatanta takwas a jihar Kano

Duk Labarai
Hukumar kula da harkokin shari'a ta jihar Kano a arewacin Najeriya ladaftar da wasu ma'aikatanta takwas ciki har da alkalai. Wani kwamitin ladaftarwa na hukumar ne ya bayar da shawarar ɗaukar matakin bayan kammala bincikensa kan ƙorafe-ƙorafen da wasu suka gabatar waɗanda suka haɗa da zarge-zargen karɓar rashawa. Kwamitin karɓar korafe-korafen jama'a na hukumar kula da harkokin shari'ar ya ɗauki matakin ladaftawar ne kan ma'aikatan shari'a su takwas ciki har da alkalan kotunan majisteret. Kakakkin hukumar Baba Jibo Ibrahim ya ce bincike ya gano yadda wani alkalin kotun majistare ya gudanar da wata shari’a ba tare da an rubuta ta ba, abin da ya saba dokokin shari’a. Bayanai na cewa an jima ana kokawa da jami’an kotu a jihar game da yadda suke karbar toshiyar baki da sauran laifu...
Za a binne gawar tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya a Abuja ranar Juma’a

Za a binne gawar tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya a Abuja ranar Juma’a

Duk Labarai
Ana sa ran binne marigayi babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Taoreed Lagbaja ranar Juma'a a Abuja. Yayansa da yake bi, Moshood Lagbaja, ne ya bayyana haka a garin Osogbo, jihar Osun a lokacin da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar St Charles Grammar School Osogbo, (SCOBA), ta kai wa iyalan ziyarar ta'aziyya. Moshood ya ce hukumomin soji sun ce ba za su ba iyalan gawar marigayin ga, amma sun bayar da tabbacin cewa za a yi masa jana'iza da ta dace a Abuja, ranar Juma'a. Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar rasuwar babban hafsan sojin na ƙasa ne da ta ce ya rasu ranar 5 ga watan nan na Nuwamba, 2024, yana da shekara 56 a wani asibiti a Lagos, bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba. Kafin tabbatar da rasuwar, an fara raɗe-raɗin cewa babban hafsa...