Bayan kama ‘yan kimmashin da suka dawo daga aikin Hajji a jihar Katsina, wanda kuma ake zargin gwamnatin jiharce ta dauki nauyin zuwansu Saudiyya, Gwamnatin Jihar Katsinar tace ba zata ce uffan ba kan lamarin
An kama shuwagabannin mutanen daji a filin jirgin sama na Umar Musa 'Yaradua dake jihar Katsina bayan sun dawo daga aikin hajjin bana
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya tabbatar da kamen inda yace an kamasu ne ranar 18 ga watan Yuni kuma tuni sun mikasu hannun jami'an DSS.
Ministan yace sabuwar dokar katin dan kasa ta National Identity Management Commission (NIMC) ta taimaka sosai wajan kama mutanen.
Saidai bai bayyana sunayen wadanda aka kama din ba.
A hirarsa da BBCHausa, Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Katsina, Nasiru Mu’azu Danmusa ya tabbatar da kamen amma yace ba zasu ce komai akai ba saboda lamarine da ya shafi Gwamnatin tarayya
Shi kuma Kwamishinan al'adu da yada labarai na jihar Katsina, Bala Salisu Zango ya bayyanawa Daily Trust cewa bai s...






