Kalli Bidiyo: Wata Sabuwa ana rade-radin wani babban dan siyasar Najeriya dan luwadi ne, ya mayar da martani
Shahararren dan din din kudu kuma dan siyasa a jihar Legas, Desmond Elliot wanda aka bayyana cewa dan luwadi ne ya fito ya karyata wannan zargi da akw masa.
Shafin Gistlover ne ya wallafa sunayen wasu 'yan Fina-finan kudu inda yace duk 'yan luwadi ne wanda lamarin ya jawo hauragiya a kafafen sada zumunta.
Saidai a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na TV, Desmond Elliot ya musanta wannan zargi inda yace wasu ne kawai ke son bata masa suna.
Kalli Bidiyon jawabinsa anan
Yace yana da abubuwa da yawa da yake mayar da hankali akai fiye da irin wadannan gulmace gulmacen da ake yadawa akansa.