Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gwamnatin tarayya ta sanar da sabon harajin VAT da ‘yan Najeriya masu amfani da banki zasu biya

Gwamnatin tarayya ta sanar da sabon harajin VAT da ‘yan Najeriya masu amfani da banki zasu biya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bukaci bankuna su fara karbar sabon Harajin VAT na kaso 7.5 akan duk wani amfani da masu hulda da banki suke yi. Za'a rika cire harajinne akan aika kudi, karbar katin ATM, duba balance da sauransu. Kuma Harajin zai fara aiki ne nan da ranar 19 ga watan Janairu, watau Ranar Litinin me zuwa. Tuni dai bankunan suka aikawa masu hulda dasu sanarwar fara karbar Haraji.
Wai dama har yanzu akwai irin wannan Rafalin?>>Dan wasan Najeriya Bright Osayi-Samuel ya tambaya

Wai dama har yanzu akwai irin wannan Rafalin?>>Dan wasan Najeriya Bright Osayi-Samuel ya tambaya

Duk Labarai
Dan wasan Najeriya, Bright Osayi-Samuel yayi tambayar cewa shin wai dama har yanzu akwai irin wannan Rafalin? Ya bayyana hakane bayan wasan Najeriya da Morocco wanda Moroccon ta fitar da Najeriya. Ya bayyana cewa ba wai yace Rafali ne ya fitar dasu ba amma maganar gaskiya ba'a musu Adalci ba. https://twitter.com/i/status/2011601494760444006
Kalli Bidiyon: Wata magana da Kwankwaso yayi da tasa ake ta cewa ko zai koma APC ne

Kalli Bidiyon: Wata magana da Kwankwaso yayi da tasa ake ta cewa ko zai koma APC ne

Duk Labarai
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa shi fa bai ce ba zai koma APC ba. Yace amma kamin ya koma sai an gaya masa me za'awa Talakawa. Sannan sai an gaya masa shi wane matsayi za'a bashi. Sannan sai an gaya masa matsayin gwamnatin jihar Kano da 'yan majalisarsu. Yace amma har yanzu babu wani da ya sameshi akan hakan. https://twitter.com/i/status/2011530907920806366
Kalli Bidiyon: Mawakiyar Najeriya, Teni ta kwanta Rashin Lafiya saboda an cire Najeriya daga gasar AFCON

Kalli Bidiyon: Mawakiyar Najeriya, Teni ta kwanta Rashin Lafiya saboda an cire Najeriya daga gasar AFCON

Duk Labarai
Tauraruwar mawakiyar Najeriya, Teni kenan inda ta kwanta rashin lafiya saboda an cire Najeriya daga gasar AFCON. Ta yi Bidiyo inda take gayawa 'yan kasar Ghana cewa sin ga abinda dan uwansu ya haddasa koh. Ta yi kira ga Shugaba Tinubu ya tura jirgin yaki zuwa kasar Ghana. https://twitter.com/i/status/2011708327647182982 Rafalin da ya hura wasan Najeriya da Morocco dai dan kasar Ghanane.