Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Yanda Rikici ya bàrkè tsakanin wasu ‘yan Najeriya da ‘yan kasar Morocco bayan da aka yi yunkurin canja musu wajan zama a filin wasan da aka buga wasan jiya

Kalli Bidiyon: Yanda Rikici ya bàrkè tsakanin wasu ‘yan Najeriya da ‘yan kasar Morocco bayan da aka yi yunkurin canja musu wajan zama a filin wasan da aka buga wasan jiya

Duk Labarai
Wasu 'yan Najeriya da suka je kallon wasa a kasar Morocco sun yi rikici da hukumomin dake kula da filin wasan da aka buga jiya tsakanin Najeriya da Morocco. Sun shiga filin da wuri inda suka samu wuri suka zauna amma sai masu kula da filin wasan suka ce su tashi daga wajan su canja wajan zama. Saidai sun ce ba zasu tashi ba inda suka dauki abin suka watsa a Duniya. Sun yi zargin ana son a nuna musu banbanci ne da kaisu inda ba zasu iya baiwa Najeriya goyon bayan da ya kamata ba. A karshe dai masu kula da Stadium din sun kyalesu. https://twitter.com/i/status/2011494097614487592
An samu Karin ‘yan majalisar jihar Rivers 2 sun janye daga yunkurin tsige Gwamna Simi Fubara

An samu Karin ‘yan majalisar jihar Rivers 2 sun janye daga yunkurin tsige Gwamna Simi Fubara

Duk Labarai
Karin 'Yan majalisar jihar Rivers 2 sun janye daga yunkurin tsige gwamnan jihar, Simi Fubara. 'yan majalisar, Barile Nwakoh da Emilia Amadi sun bayyana cewa sun janye daga wannan shirine bayan da wasu manya suka saka baki. Sun bayyana cewa zai fi kyau a warware matsalar ta hanyar amfani da hanyar Sulhu. Hakan na zuwane kasa da awanni 24 bayan da wasu 'yan majalisar 2 suma suka janye daga yunkurin tsige gwamna Fubara. Yanzu dai 'yan majalisa 4 kenan suka janye daga yunk na tsige gwamna Fubara.