Thursday, January 9
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Hotuna: Gawar marigayi shugaban sojojin Najeriya, Lagbaja ta isa Legas

Hotuna: Gawar marigayi shugaban sojojin Najeriya, Lagbaja ta isa Legas

Duk Labarai
Rahotanni daga Legas na cewa, gawar marigayi shugaban sojoji, Lt. Gen. Taoreed Lagbaja ta isa Jihar inda za'a yi jana'izarsa. Gawar ta sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas din da safiyar ranar Alhamis. A ranar Larabar data gabata ne dai gwamnatin tarayya ta tabbatar da mutuwar shugaban sojojin. Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da cewa ranar November 15, 2024 za'a yi jana'izar marigayin a makabartar sojoji dake Abuja
Sojojin Najeriya sun soma fatattakar Làkùràwà daga sassan jihar Kebbi

Sojojin Najeriya sun soma fatattakar Làkùràwà daga sassan jihar Kebbi

Duk Labarai
Rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da hare-hare kan ƙungiyar 'yanbindiga ta Lakurawa da ta ɓulla a wasu sassan jihohin Kebbi da Sokoto na arewa maso yammacin ƙasar. Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Augie na jihar Kebbi, sun ce sojojin ƙasar sun shiga wuraren da 'yan ƙungiyar suka kakkafa sansanoni tare da lalata su. Sojojin sun kuma kori Lakurawan a dazukan ƙaramar hukumar, tare da kuɓutar da wasu daga cikin dabbobin da masu gwagwarmaya da makaman suka sace. Matakin na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da 'yan ƙungiyar suka yi artabu da mutanen gari Mera na yankin ƙaramar hukumar, tare da kashe mutum 15 da sace shanu masu yawa. Shugaban ƙaramar hukumar Augie, Hon Yahaya Muhammad Augie, ya shaida wa BBC cewa bayan dakarun ƙasar sun soma ƙaddamar da hare-hare kan ƙungiyar, yanzu ha...
Kalli Bidiyo: Matashi da ya kammala karatun Digiri daga jami’ar Umar Musa ‘Yar’Adua da sakamakon Digiri mafi daraja watau First Class na tallar Ruwa a Titin Abuja

Kalli Bidiyo: Matashi da ya kammala karatun Digiri daga jami’ar Umar Musa ‘Yar’Adua da sakamakon Digiri mafi daraja watau First Class na tallar Ruwa a Titin Abuja

Duk Labarai
Wani matashi me suna Ishaq dake sayar da ruwa wanda aka fi sani da Pure Water a Abuja ya bayyana cewa yana da kwalin kammala Digiri mafi daraja watau First Class. Matashin an yi hira dashi ne inda bidiyon hirar ta watsu sosai a kafafen sada zumunta. https://twitter.com/Ummieey_k/status/1856821597476184530?t=eH65h9aWtgN1D3gr8mPRrA&s=19 Yace tun da ya kammala karatun bashi da aikin yi. Saidai Tuni wata baiwar Allah ta bukaci da a nemo mata shi dan ta taimaka masa.
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ICPC ta gurfanar da tsohon dan majalisa a kotu bisa zargin satar Naira Miliyan 18 inda kotu ta bayar da belinsa akan Naira miliyan 20

Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ICPC ta gurfanar da tsohon dan majalisa a kotu bisa zargin satar Naira Miliyan 18 inda kotu ta bayar da belinsa akan Naira miliyan 20

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ICPC ta kama tsohon dan majalisar tarayya daga jihar Benue John Dyegh bisa zargin cin hancin Naira Miliyan 18 inda ta gurfanar dashi a kotu. Dan majalisar wanda ya wakilci mazabar Gboko/Tarka daga jihar Benue ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya dake babban birnin jihar Makurdi ranar Litinin. Kakakin ICPC, Demola Bakare a sanarwar da ya fitar ranar Talata yace John a ranar May 19, 2014, ya karbi kudi da suka kai N18,970,000. Yace kudin na aikin gina makaranta ne a karamar hukumar Guma amma aka karkatar dasu zuwa asusun bankin wani kamfani me suna Midag Limited wanda John ke da hannu jari me yawa a ciki. Hakan ya sabawa dokar aikin gwammati. Mai Shari'a na kotun,Justice Abubakar ya bukaci a aika da John gidan yarin dake Makurdi har sai ...
Jirgin sama daga Abuja zuwa Legas yayi saukar gaggawa bayan da yayi karo da tsuntsu

Jirgin sama daga Abuja zuwa Legas yayi saukar gaggawa bayan da yayi karo da tsuntsu

Duk Labarai
Jirgin saman Air Peace yayi saukar gaggawa bayan da yayi karo da tsuntsu. Jirgin dai zai tashi ne daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja zuwa Legas inda tsuntsun ya fado masa wanda dole hakan tasa aka fasa tafiyar. Lauya me rajin kare hakkin bil'adama, Inibehe Effiong dake cikin jirgin yace suna shirin tashine inda jirgin yayi karo da tsuntsun wanda hakan ya jawo iface-iface a cikin jirgin. Yace an saukesu daga cikin jirgin inda suke jiran a gyarashi ko kuma a canja musu wani jirgin. Yace abin jin dadi shine jirgin bai kai ga tashi sama ba yayin da hadarin ya faru.
Gwamnati za ta fara kama yaran da ke yawo a titunan jihar Kano

Gwamnati za ta fara kama yaran da ke yawo a titunan jihar Kano

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai yi aiki kwashe yaran da ke gararamba a titunan birnin. Hukumomi sun ce ɗaukar matakin ya zama wajibi kasancewar barin yara ƙanana suna yawo a tituna babbar barazana ce ga tsaro da kuma ci gaba al'umma. Kwamitin zai kuma bai wa gwamnati shawarar kan yadda za a mayar da yaran garuruwan da suka fito. Kwamitin ƙarkashin shugabancin kwamandan hukumar Hisba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa zai bi diddigi tare da zaƙulo yaran da suke yawo a kwararo da tituna suna kwana a kasuwanni da ƙarƙashin gada a sassan birnin Kano domin samar musu da kyakkyawar makoma da kuma maslahar al’umma. "Yaran da za mu fara kamawa sune waɗanda suke kamar an zubar da su yawo kan titi, waɗanda ba su da wata makoma, mafi y...
Zan iya yin mulki a karo na 3>>Donald Trump ya fada cikin Raha

Zan iya yin mulki a karo na 3>>Donald Trump ya fada cikin Raha

Duk Labarai
Zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa zai iya yin mulkin kasar a karo na 3. Trump ya bayyana hakane yayin ganawa da 'yan majalisar Republican. Inda yace ba zai iya sake tsayawa takara ba sai idan sune 'yan majalisar suka ga cewa yayi kokari suka bashi dama. An fashe da dariya a yayin da yayi maganar. Bayan zaman nasu, da aka tambayi 'yan majalisar sun ce maganar Trump yayi ta ne cikin raha.