Monday, December 22
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon Gwamnin Ban tausai inda Hukumomin sojan Najeriya suka kama wani soja me mukamin Kanal saboda yayi korafin an ki kara mai matsayi zuwa Brigadier General

Kalli Bidiyon Gwamnin Ban tausai inda Hukumomin sojan Najeriya suka kama wani soja me mukamin Kanal saboda yayi korafin an ki kara mai matsayi zuwa Brigadier General

Duk Labarai
Wannan Bidiyon wani soja ne gwanin Ban Tausai inda aka ganshi an aika sojoji su kamashi saboda yayi korafin an ki kara masa mukami. Sojan dai na da mukamin Kanal ne inda yake neman a kara masa mukami zuwa Brigadier Janar amma yace shekara da shekaru an ki a masa karin mukamin. An ga 'ya'yansa na ta kururuwa yayin da ake tafiya dashi. https://twitter.com/SaharaReporters/status/1995489166768160960?t=6MDKizrTjD5ueM7gUDiBbQ&s=19
Ba zaman taba bari a ci gaba da haka ba, dole Tinubu ya canja Shettima ya dauko Kirista >>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Ba zaman taba bari a ci gaba da haka ba, dole Tinubu ya canja Shettima ya dauko Kirista >>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Duk Labarai
Malamin Kirista, Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa Mulkin musulmi da Musulmi da ake yi a Najeriya ya isa zama cin zarafi na karshe ga Kiristocin kasarnan. Yace dolene Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauke Kashim Shettima ya dauki Kirista a matsayin mataimaki. Yace ba zai bari abubuwa su ci gaba da zama a haka ba dan kuwa nan gaba jikokinshi zasu iya komawa musulmai kuma ba zai so haka ba. https://twitter.com/channelstv/status/1995415057606271153?t=eSClaCFwX65qbNnNapFHmQ&s=19
Yayin da Dalibai Kiristoci ke zargin an hanasu gona coci a jami’o’in Kashere, Gombe dana BUK, Kano, Shima wani dalibi musulmi yayi zargin cewa an hana Musulmai gina masallaci a jami’ar Jos, UniJos

A dazu ne hutudole ya kawo muku rahoton yanda wasu Kiristoci dalibai daga jami'o'in BUK, Kano da Kashere, Gombe inda suke zargin an hanasu gina coci a wadannan makarantu yayin da aka bar musulmai suka gina masallatai. A martani ga wannan zargi shima wani dalibi musulmi yai zargin cewa an hana dalibai musulmai gina masallaci a jami'ar UNIJos, dake jihar Filato. Yace duk da akwai masalacin da aka fara ginawa amma an hana a karasashi. Sannan yayi zargin cewa an ma hana musulmai yin salla a masallacin da ba'a karasa ba. https://twitter.com/Abdul_Ahmad_/status/1995361298482385141?t=uxPj8rW8-jvRmbak-pY-BA&s=19
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yacewa shugaban Venezuela ya sauka daga shugabancin kasar ko kuma ya dandana kudarsa

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yacewa shugaban Venezuela ya sauka daga shugabancin kasar ko kuma ya dandana kudarsa

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, shugaban kasar Amurkar Donald Trump ya baiwa shugaban kasar Venezuela, Maduro Umarnin ya sauka daga shugabancin kasar ko ya dandana kudarsa. Rahotanni sun ce shugaba Trump na ikirarin yakar ayyukan masu safarar miyagun kwayoyi ne amma kuma wasu na zargin cewa, Trump na kokarin satar man fetur din kasar Venezuela ne. Hakan na zuwane bayan da Bidiyo ya bayyana ind aka ji Trump na bayyana son samun man fetur daga kasar Venezuela kyauta. Tuni dai rahotanni suka ce Amurka ta jibge jiragen ruwan yaki da dakarun sojoji a ruwan dake kusa da kasar ta Venezuela.
An fitar da jadawalin kasashen da suka fi mata masu kyau a Duniya guda 50 amma Najeriya bata cikinsu

An fitar da jadawalin kasashen da suka fi mata masu kyau a Duniya guda 50 amma Najeriya bata cikinsu

Duk Labarai
An fitar da Jadawalin kasashen Duniya dake da mata da suka fi kyau guda 50 amma babu Najeriya a cikinsu. Ga kasashen kamar haka: 1. S. Korea2. Brazil3. USA4. Japan5. Mexico6. Germany7. Colombia8. Thailand9. Italy10. Venezuela11. Argentina12. France13. Taiwan14. Spain15. Greece16. Türkiye17. Russia18. India19. UAE20. Saudi Arabia21. China22. Iran23. Lebanon24. UK25. Australia26. Canada27. Philippines28. Malaysia29. Egypt30. South Africa31. Switzerland32. Belgium33. Sweden34. Israel35. Kuwait36. Jordan37. Peru38. Ukraine39. Dominican Republic40. Netherlands41. Austria42. Chile43. Qatar44. Romania45. Portugal46. Morocco47. Singapore48. Poland49. Hungary50. Czech Republic
Kalli Bidiyo Da Duminsa: Maryam Booth ta tabbatar da abinda mutane ke tsammani

Kalli Bidiyo Da Duminsa: Maryam Booth ta tabbatar da abinda mutane ke tsammani

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth ta bayyana cewa yau ranar Bikinane. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo ta da aka gani a Tiktok. Hakan na zuwane bayan da hotuna ta da mawakin siyasa Tijjani Gandu suka karade kafafen sada zumunta inda ake rade-radin cewa aure zasu yi. Saidai Tijjani ya nace akan cewa a jira nan da wanni 24 kamin ya sanar da abinda suke nufi da wadannan hotunan;. https://www.tiktok.com/@maryam_booth97/video/7578756880734883090?_t=ZS-91r9awsn7Nx&_r=1
Kalli Bidiyo: Da cuwa-cuwa aka hada jama’ar da suka taru a wajan jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Kalli Bidiyo: Da cuwa-cuwa aka hada jama’ar da suka taru a wajan jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Duk Labarai
Wannan malamin yayi zargin cewa, da cuwa-cuwa aka tara jama'ar da suka taru a wajan jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Ya bayyana cewa kuma da wuya a samu mutane adalai 40 a cikin mutanen da suka taru a waja jana'izar malamin. Yayi zargin cewa duk 'yan Bindigar dake Arewa maso yamma 'yan darika ne inda yace an ga hotuna shehunan darika a jikin bindigun 'yan Bindigar. https://www.tiktok.com/@zaidou1taza/video/7578672250929433867?_t=ZS-91r33VPcVO4&_r=1