Sunday, April 26
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Ji yanda Wani dansanda ya zangawa Sheikh Salihu Zaria Mqry

Kalli Bidiyon: Ji yanda Wani dansanda ya zangawa Sheikh Salihu Zaria Mqry

Duk Labarai
A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, an ga Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun na bada labari dalla-dalla kan dalilin dakatar da Sheikh Abubakar Salihu Zaria. Sheikh Yusuf Sambo ya bayyana cewa, DSS ne suka fara Neman Sheikh Salihu Zaria shiyasa aka dakatar dashi dan dakile fitinar. Ya kara da cewa, a baya akwai sanda aka taba kamashi, dansanda ya fallasa masa mari yace zai kara yin irin waccan maganar da yayi? Sai yace ba zai kara ba tallar Gwanjo zai koma, Sheikh Yusuf Sambo yace shine ya je ya karbo malam daga hannun jami'an tsaro. https://www.tiktok.com/@youngalkaligombe/video/7613911890586029320?_r=1&_t=ZS-94SMvR5pSWv
Allah Sarki: Ji yanda aka ga wani Kirista na sauraren wa’azin Sheikh Guruntum

Allah Sarki: Ji yanda aka ga wani Kirista na sauraren wa’azin Sheikh Guruntum

Duk Labarai
An hangi wani Kirista na sauraren wa'azin babban malamin addinin Islama, Sheikh Guruntum. Wani da ya shaida hakan ne ya fada a shafinsa na X Inda yace: "I just passed a Christian man in our area listen to Sheikh Guruntum’s Tafsir…" https://twitter.com/i/status/2029297705487327722 Wani ya bashi amsar cewa da yawa suna ji ai. https://twitter.com/i/status/2029409086475817394
Kalli Bidiyon: Labari me sanya Shauki, yanda wata mata data saba ciyar da karnuka, taje wajan Biki amma tasa aka kawo musu abinci

Kalli Bidiyon: Labari me sanya Shauki, yanda wata mata data saba ciyar da karnuka, taje wajan Biki amma tasa aka kawo musu abinci

Duk Labarai
Wata mata a kasar India da ta saba ciyar da wasu karnuka kullun da dare. Wata rana ta je wajan biki bata dawo ba sai ta sayi abinci, irin wanda ake kaiwa mutum har gida a mota ko a mashin. Da dan sakon ya je kofar gidanta sai ya kirata yace ga abincin an kawo, sai tace bata nan. Sai yace a ina zai ajiye? Sai tace masa ya duba kusa da gidanta akwai wasu karnuka ya basu abincin , ta saba basu ne kuma tasan suna nan suna jiranta amma yau bata nan shiyasa tasa a kawo musu. Haka dan sakon ya nemi karnikan ya basu abincin inda ya dauki Bidiyon lamarin saboda shima abin ya burgeshi. https://twitter.com/i/status/2029418361713791166
Kuma Dai: Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sake maka ICPC a kotu inda yake neman su biyashi diyyar Naira Biliyan 15.6

Kuma Dai: Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sake maka ICPC a kotu inda yake neman su biyashi diyyar Naira Biliyan 15.6

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya maka hukumar yaki da rashawa, ICPC a kotu inda yake neman su biyashi diyyar naira Biliyan 15.6 saboda bata masa suna. Hakan na zuwane yayin da ICPC tace ta gano na'urar yiwa waya kutse a gidan malam Nasiru Ahmad El-Rufai. Lauyoyin Malam Nasiru sun ce kalaman na ICPC abin damuwa ne kuma sun bata masa suna Dan haka El-Rufai yace wannan abu ya take masa hakkinsa na Bil'adama inda yace yana neman. Biliyan 15.6 na bata masa suna. El-Rufai yace ya baiwa ICPC awanni 24 su gaggauta biyansa wannan kudi in ba haka ba zai makasu kotu.
Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya ce har yanzu yaki Amsa k9 daya daga cikin Tambayoyin da ICPC suke masa

Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya ce har yanzu yaki Amsa k9 daya daga cikin Tambayoyin da ICPC suke masa

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, har yanzu bai amsa tambaya ko daya ba cikin Tambayoyin da ICPC suke masa. Malam Nasiru Ahmad El-Rufai dai ya shafe kusan sama da sati biyu kenan a hannun ICPC tun da suka karbeshi daga hannun EFCC. Ya bayyana cewa, dalilin da yasa ya ki amsa tambayoyin nasu shine binciken da ake masa na da alaka sa diyasa. A baya dai ICPC ta kai samame gidan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda tace ta gano abubuwa da yawa ciki hadda wata na'ura ta yiwa waya kutse. A baya dai malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi ikirarin yiwa wayar me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu kutse.
Allah Sarki: Wata mata ‘yar kasar Ukràìnè ta je Dubai cirani inda acan ta karbi Musulunci, saidai awanni kadan bayan karbar Musulunci ta ta rigamu gidan gaskiya

Allah Sarki: Wata mata ‘yar kasar Ukràìnè ta je Dubai cirani inda acan ta karbi Musulunci, saidai awanni kadan bayan karbar Musulunci ta ta rigamu gidan gaskiya

Duk Labarai
Wannan wata matace 'yar kasar Ukraine da ta je Dubai Cirani Ta karbi Musulunci yayin da ake cikin watan Azumin Ramadana. Saidai awanni kadan da karbar Musuluncita, ta rigamu gidan gaskiya. An yi jana'izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. An bayyana cewa shekarunta 29 https://twitter.com/i/status/2029300176620261727
Da Duminsa: A karin Farko, Sheikh Alkali Zaria ya fitar da sanarwa kan dakatarwar da aka masa

Da Duminsa: A karin Farko, Sheikh Alkali Zaria ya fitar da sanarwa kan dakatarwar da aka masa

Duk Labarai
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Alkali Zaria ya fitar da sanarwa kan dakatarwar da kungiyar Izala ta masa. Ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na Facebook. Ga abinda yace kamar haka: "Aslm Alkm wrhmtlh wbrkth magana Ta gaskiya shine fadin Allah s w t da sannu zakuyi ta son Abu ba Alkhairi bane Agareku saannan da sannu zakuyi ta kin Abu kuma shine Alkhairi gareku Allah shine mafi sani Alhali mu bamu sani ba inaso kowa ya sani Ni Dan kungiyar jamaatu izalatil bid.ah wa ikamatis Sunnah ne NHQ jos Karkashin Jagoranchin Fhadilatush sheikh Muhammad sani Alhaji Yahaya Jengre Sannan kuma ba Nine Na kai kaina Damaturu ba kungiya ce ta Turani Amatsayin me Tafseer Na wannan Shekarar 1447 /2026 Duk Dan wannan kungiya Ta Jamaatu izatil Bid.ah Waikamatis Sunna ya sanmu da Daa da biyayya b...
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Musulmai hadda Kiristocin Najeriya na Allah wadai da Rev. Ezekiel Dachomo saboda munanan kalaman da yayi akan Musulunci

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Musulmai hadda Kiristocin Najeriya na Allah wadai da Rev. Ezekiel Dachomo saboda munanan kalaman da yayi akan Musulunci

Duk Labarai
Shahararren malamin Kirista, Rev. Ezekiel Dachomo yayi wasu munanan kalamai ga addinin Musulunci da suka tayar da hankula sosai. Da yawa ciki hadda Kiristoci sun yi Allah wadai da wadannan kalaman Nasa. Danna Nan dan kallon Bidiyon abinda ya fada Rev. Ezekiel Dachomo dai yayi kaurin suna wajan sukar Addinin Musulunci da zarge-zargen da basu tabbata ba akan Musulunci.