Wednesday, February 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

An saki Mubarak Bala, ɗan Najeriyar nan da ya yi suna wajen sukar addini bayan shafe shekara huɗu tsare a gidan yari kan tuhume-tuhumen da suka shafi ɓatanci ga addini

An saki Mubarak Bala, ɗan Najeriyar nan da ya yi suna wajen sukar addini bayan shafe shekara huɗu tsare a gidan yari kan tuhume-tuhumen da suka shafi ɓatanci ga addini

Duk Labarai
Ya shaida wa BBC irin ƙalubalen da masu aƙida irin tasa ta rashin yadda da kowane addini ke fuskanta. Mubarak Bala, shugaban kungiyar Humanist Association of Nigeria kuma fitaccen mai ikirarin rashin addini, ya samu 'yanci bayan shafe shekaru huɗu a gidan yari kan zargin batanci. An yanke masa hukuncin shekara 24 a kurkuku tun a fari a shekarar 2022, bayan ya amsa laifuka 18 da suka haɗa da batanci, tayar da zaune tsaye, da cin zarafin addini ta kafar sada zumunta. Hukuncin ya samo asali ne daga wallafa ra'ayoyinsa na sukar addinin Islama, Allah, da Annabi Muhammad (SAW) ta kafar sada zumunta, wanda ya haifar da fushin al'umma. Kafin a yanke masa hukunci, Mubarak ya yi shekara biyu yana jiran shari’a a tsare tun bayan kamashi a Kaduna a ranar 28 ga Afrilu, 2020. A cewar rahoton BB...
Adawa tsakanin tsofaffin gwamnoni na mayar da Kano baya – Garo

Adawa tsakanin tsofaffin gwamnoni na mayar da Kano baya – Garo

Duk Labarai
Tsohon ɗantakarar mataimakin gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023, Murtala Sule Garo ya ce adawar siyasar da ke tsakanin tsofaffin gwamnoni na hana jihar ci gaba. Garo ya kuma yi kira ga jagororin siyasar jihar su mayar da kubensu, tare da haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ciyar da jiharsu gaba. Garo ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ya ce, "babu daɗi ganin jihohi irin Zamfara da ba ta kai Kano ba, tsofaffin gwamnoninta suna ajiye bambancin siyasa suna haɗuwa domin ciyar da jihar gaba. Mu a nan Kano, da wahala ka samu tsofaffin gwamnoni sun haɗu domin tattauna hanyoyin da za a magance matsalolin jihar." "Ina kira ga tsofaffin gwamnoninmu, idan har da gaske suna ƙaunar Kano, su haɗa kai. Ba a samun ci gaba da rabuwar kai. Dole jagororin si...
Yarinyar da ake tuhuma da zuba wa miijinta guba a abinci a Jigawa ta amsa laifinta

Yarinyar da ake tuhuma da zuba wa miijinta guba a abinci a Jigawa ta amsa laifinta

Duk Labarai
Yarinyar nan mai shekara 14 da ƴansanda suka tuhuma da kashe abokin mijinta bayan zuba musu guba a abinci a jihar Jigawa ta amsa laifinta a gaban alƙali Al'amarin dai ya faru ne a ranar Lahadin 15 ga watan Disambar 2024 a ƙauyen Bakata da ke ƙaramar hukumar Kiyawan jihar Jigawa. Yarinyar dai ta saka wa mijinta da abokansa guba a taliya, kuma nan da nan suka fita daga hayyacinsu, inda aka kai su asibitin garin Jahun inda a nan ne ɗaya daga cikin abokan mijin ya mutu. Yarinyar ta amsa laifin saka gubar, sai dai kuma ta ce tsohon saurayinta wanda ɗanuwanta ne ya ba ta gubar domin ta saka wa mijin nata da abokansa a abinci. Sai dai tsohon saurayin ya ce ba ya garin lokacin da yarinyar ta je garin. Yanzu haka yarinyar tana tsare a hannun ƴansanda inda shi kuma saurayin ke tsare a gi...
Najeriya ta naɗa Éric Chelle a matsayin kocin Super Eagles

Najeriya ta naɗa Éric Chelle a matsayin kocin Super Eagles

Duk Labarai
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta naɗa tsohon kocin tawagar Mali, Éric Chelle, a matsayin kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles. Chelle mai shekara 47 ya jagoranci Mali har zuwa zagayen kwata fayinal a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 a Ivory Coast, kafin mai masaukin baƙi ta doke su. NFF ta ce ta amince da naɗin nasa ne bayan kwamatinta na musamman ya bayar da shawarar yin hakan a yau Talata. Naɗin nasa na zuwa ne bayan NFF ta kasa daidaitawa da Bruno Labbadia ɗan ƙasar Jamus game da batun biyan haraji bayan sanar da ba shi aikin a watan Agustan 2024. Kafin naɗin nasa, shugaban NFF Ibrahim Musa Gusa ya faɗa wa manema labarai cewa sabon kocin da za su bai wa aikin shi ne zai jagoranci tawagar Super Eagles ta 'yanwasan cikin gida zuwa gasar kofin Afirka ta CHAN - w...
Kwanaki kadan bayan da ya karyata labarin komawa PDP, An hangi tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a ofishin Jam’iyyar SDP

Kwanaki kadan bayan da ya karyata labarin komawa PDP, An hangi tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a ofishin Jam’iyyar SDP

Duk Labarai
Tsohon gwamman jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya saka mutane rudani bayan da aka ganshi a hedikwatar Jam'iyyar SDP a ranar Talata. Hakan na zuwane kwanki biyu bayan da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya karyata labaran da suka ce ya bar Jam'iyyar APC zuwa PDP. Tsohon shugaban NIMASA, Ahmad Tijjani Ramalan ne ya wallafa hotunan zuwan El-Rufai ofishin SDP. Ya bayyana cewa an yi zama tsakanin El-Rufai da SDP ne a kokarin da ake na yin hadaka dan samo hanyar yin nasara akan Jam'iyyar APC a zaben shekarar 2027.
Za mu fitar da Afirka da ga talauci, in ji Tinubu

Za mu fitar da Afirka da ga talauci, in ji Tinubu

Duk Labarai
Shugaba Bola Tinubu, a yau Talata ya ce shugabannin Afirka za su ci gaba da jajircewa wajen fitar da al’ummarsu daga kangin talauci da gina tattalin arzikinsu a matakan da su ka dace. Tinubu, wanda ya kasance babban bako na musamman, ya bayyana haka ne a wajen rantsar da shugaba John Mahama a birnin Accra na kasar Ghana. “Ba mu da wani abin da za mu tabbatar wa kowa sai kanmu. Mun sami hanya mai mahimmanci don samun nasarar mu. Za mu fitar da al'ummarmu daga kangin talauci, mu gina tattalin arziki mai dorewa a kan kan mu. "A yau, na zo nan ba kawai a matsayina na shugaban Najeriya ba, har ma a matsayina na dan Afirka mai cikakken goyon baya ga Ghana da mutanenta," in ji Tinubu
Yarabawa miliyan 60 sun shirya ficewa daga Najeriya – Akintoye

Yarabawa miliyan 60 sun shirya ficewa daga Najeriya – Akintoye

Duk Labarai
Shugaban Ƙungiyar Ƙudirin samar da 'Yancin Kai ta Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye, ya jaddada cewa ƙungiyar ba za ta janye daga neman kafa ƙasar Yarabawa ba. A cewar Akintoye, kimanin Yarabawa miliyan 60 ciki har da mazauna gida da 'yan ƙasashen waje, suna goyon bayan ƙudirinsa na kafa ƙasar Yarbawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Da ya ke tattaunawa da jaridar The PUNCH a jiya Litinin, Akintoye ya ce, “Ba za mu koma baya ba. Dole ne mu fice daga Najeriya, ko kuma ƙasarmu za ta shiga matsala. “Ba kwa jin muryar mu a tituna? Ƙasar Yarabawa yanzu, babu gudu ba ja da baya. “Muna nufin Yarabawa da ke Nijeriya, kusan mutane miliyan 55 zuwa 60. Muna so mu kafa ƙasa ta kanmu. Ba za a samu Najeriya ba idan muka kafa ƙasarmu. Amma idan sauran suna son ci gaba da kasancewa a matsay...
Nijeriya Ta Yi Nasarar Haƙo Gangar Mai Milyan Daya Da Rabi A Karon Farko Cikin Shekaru Hudu

Nijeriya Ta Yi Nasarar Haƙo Gangar Mai Milyan Daya Da Rabi A Karon Farko Cikin Shekaru Hudu

Duk Labarai
Najeriya ta yi nasarar cimma burinta na cike gibin da take samu wajen hako mai wanda Kungiyar ƙasashe masu albarkatun mai OPEC ta kayyade mata na haƙo ganga miliyan 1.5 a kowace rana. Wannan shinekaron farko cikin shekaru hudu da Najeriya ta sami irin wannan gagarumar nasara tun bayan dawowar matsalar masu fasa bututun mai da gwamtocin baya suka fuskanta Wasu alkaluman binciken Bloomberg sun nuna cewa yawan man da Najeriya ke haƙowa ya ƙaru da ganga 40,000 zuwa miliyan 1.51 a watan Disambar bara. A baya dai ƙungiyar OPEC ta ware wa Najeriya damar haƙo ganga Milyan 1.8 a kowace rana, sai dai ƙungiyar ta rage wannan adadi zuwa milyan 1.5 sakamakon gazawar Najeriya na cike giɓin da take samu wajen haƙar man ta dalilin matsalolinta na cikin gida, hakan ya janyo wa kasar koma-baya a ba...
Akan Bashin Naira Dubu 300 Da Ake Binsa, Kotu Ta Siyar Da Gidansa Na Kusan Milyan 20 A Naira Milyan Biyu A Kano

Akan Bashin Naira Dubu 300 Da Ake Binsa, Kotu Ta Siyar Da Gidansa Na Kusan Milyan 20 A Naira Milyan Biyu A Kano

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Malam Surajo Yarima ya ce a lokacin da aka kai karar kotu ya samu karaya ne inda yake jinya a jihar Adamawa, kuma ya nuna musu hotunan lokacin da yake jinya domin su zama hujja, amma duk da haka ba a karbi uzurinsa ba. Ya ce yanzu haka an watsar da kayan su waje, inda ba su wajen kwana duk da cewa yana mata da hara tara. Don haka ne Yarima ya roki gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kai masa ɗauki domin shiga lamarin.