Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Duk Labarai
Hukumar bayar da lamuni ta Duniya tace bata canja ba, har yanzu tana nan akan bakanta cewa shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur dana dala. Hukumar tace ta hakane 'yan Najeriya zasu samu saukin rayuwa daga matsin tattalin arzikin da suke fama dashi. Karin farashin man fetur dai yasa kayan masarufi sun tashi sama sosai inda talakawa ke cin abinci da kyar. Lamarin ya jawowa gwamnati tofin Allah tsine tsakanin Talakawa. Hakanan an sha zargin hukumar ta IMF da bankin Duniya da bayar da shawarwarin dake jefa kasashe da yawa cikin wahalar rayuwa.
Kalli Bidiyon matasan Kaduna suna murnar Nepa ta dawo

Kalli Bidiyon matasan Kaduna suna murnar Nepa ta dawo

Duk Labarai
Bayan dawowar wutar lantarki a jihar Kaduna, Matasa sun hau titi inda suka rika wakar cewa Nepa ta dawo. Bidiyon hakan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta: https://www.youtube.com/watch?v=caZd7slnLhs Wasu sun bayyana abin da Nishadi inda wasu kuma suka bayyana takaici da cewa 'yan Kaduna sun bayar da kunya da wannan murna. https://twitter.com/Abdool85/status/1851757048075051304?t=oy8qaPAfPahhKBfpfc46Tg&s=19 Kusan sati biyu aka kwashe ana fama da rashin wuta a yankin Arewa kamin a samu ta dawo.
Gwamnati na kai mutane Bango ta hanyar kara farashin man fetur>>NLC

Gwamnati na kai mutane Bango ta hanyar kara farashin man fetur>>NLC

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana cewa kara farashin man fetur da gwammatin tarayya ke yi na kai mutane bango. Kungiyar tace gwamnati ta kiyayi ranar da ran mutane zai baci su yi mata fitar ba zata. Ta kara da cewa shirun da 'yan Najeriya ke yi akwai randa zasu fusata idan aka kaisu bango dan kuwa ko da akuyace aka cika takura mata tana cizo. Wani dan kungiyar ta kwadago ne ya bayyanawa kafar jaridar Vanguard haka a wata hira da aka yi dashi inda yace baya son a bayyana sunansa. Yace matsin da gwamnati ke yi musamman na kara farashin man fetur zai kai kutane bango wanda kuma gwamnatin ce zata jawo a mata bore. Yace idan ka cire mutanen dake cikin gwamnati da danginsu da abokansu yawanci mutane suna cikin halin yunwa da kaka nikayi. Yace ba zai yiyu ka rika dukan yaro amm...
Kalli Bidiyo: An kama barawon Akwatin zabe a kasar Amurka

Kalli Bidiyo: An kama barawon Akwatin zabe a kasar Amurka

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} An kama wani dan kasar Amurka, Larry Savage saboda zargin satar kuri'a da lalata kuri'ar da cin amanar kasa. Larry Savage dan takara majalisar tarayyar Amurka ne daa Indiana saidai bai ci zaben ba. Lamarin ya farune a yayin da aka gudanar da zaben gwaji a Madison County dake Indiana. An tara kuri'u ana shirin zabe sai aka ga babu guda biyu, ko da aka duba kyamara sai aka hango Larry ya saka kuri'un guda biyu cikin aljihunsa. Larry ya sace kuri'un ne baya...
Ji yanda ta kaya bayan da Sanata ya cewa daya daga cikin ministocin da suke tantancewa tana da kyau

Ji yanda ta kaya bayan da Sanata ya cewa daya daga cikin ministocin da suke tantancewa tana da kyau

Duk Labarai
Sanata Osita Ngwu dake wakiltar mazabar Enugu West a majalisar dattijai ya yabi kyawun Bianca Odumegwu-Ojukwu wadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aike da sunanta majalisar dan a tantance ta a matsayin karamar Ministar harkokin kasashen waje. A yayin da ya tashi zai mata tambaya, ya fata cewa kyakkyawa, Bianca. Nan take kuwa kakakin majalisar, Godswill Akpabio ya taka masa burki inda yace ya daina yabon kyawunta dan babu inda ta rubuta cewa ita kyakkawan ce a cikin takardunta. Hakan yasa an fashe da dariya a majalisar.
Shugaba Tinubu ya nada shugaban sojoji na rikon kwarya

Shugaba Tinubu ya nada shugaban sojoji na rikon kwarya

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa. Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da riƙe muƙamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai koma ƙasar. Kafin naɗa shi a muƙamin, Oluyede ne kwamandan runduna ta 56 da ke Jaji a jihar Kaduna. Tun a makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa Janar Lagbaja yana jinya a wani asibiti a ƙasar waje bayan ta musanta rahotonnin da ke cewa ya rasu, tana mai cewa Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim ne ya maye gurbinsa a matakin riƙon ƙwarya. Daga baya hedikwatar tsaro ta Najeriya ta musanta batun, inda ta ce "babu wani batun muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa" a tsarin aikinta.
Kalli Bidiyon yanda aikin gyaran wutar lantarkin Arewa ke gudana

Kalli Bidiyon yanda aikin gyaran wutar lantarkin Arewa ke gudana

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana da ya nuna yanda ake ta kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace. Yau Kwanaki 10 kenan cif ba wutar lantarki a Arewa bayan da wasu bata gari suka lalata wutar. Lamarin ya jefa jihohi da yawa a yankin cikin duhu sannan ya sanya mutane da yawa tafka asara ta miliyoyin kudade a wasu Rahotannin ma har rayuwa an rasa. https://twitter.com/DOlusegun/status/1851505945152549093?t=hQXXb7qapmDDPO_IyFYxAw&s=19 Hukumar TCN dai tace ranar Lahadi 3 ga watan Nuwamba za'a kammala gyaran wutar lantarkin.
Kotu ta hana CBN baiwa jihar Rivers rabonta na kudaden shiga daga gwamnatin tarayya

Kotu ta hana CBN baiwa jihar Rivers rabonta na kudaden shiga daga gwamnatin tarayya

Duk Labarai
Babbar Kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta hana babban bankin Najeriya, CBN ci gaba da turawa jihar Rivers kudadenta na shiga da gwamnatin tarayya ke aikawa kowace jiha. Mai Shari'a, Joyce Abdulmalik ce ta yanke wannan hukunci bisa dalilin cewa gwamnan jihar Sim Fubara baya bin doka wajan kashe kudaden da ake turawa jihar. Dan hakane tace kada a sake turawa jihar wadannan kudade. Wasu masu sharhi da yawa dai sun bayyana wannan mataki da cewa ba ya rasa nasaba da rashin jituwa dake tsakanin Gwamna Sim Fubara da Nyesome Wike.
Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci

Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci

Duk Labarai
Majalisar tarayya ta dakatar da duk wani aikin da take a ranar Laraba inda ta fara tantance sabbin ministocin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mika mata sunayensu. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya aikewa da majalisar sunayen sabbin ministocin da ya nada bayan da yawa majalisarsa ta zartaswa garanbawul, inda ya hade wasu ma'aikatun sannan ya kirkiri wasu ya kuma kori wasu ministoci sannan ya nada wasu sabbi. Senator Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da fara tantance ministocin sannan sanata Abba Moro ya goya masa baya. Daga nan ne sai aka karanto sunayen sabbin ministocin da za'a tantance wanda ciki akwai Dr. Nentewa Yilwatda a matsayin ministan jin kai da rage talauci, Sai kuma Muhammad Maigari Dingyadi a matsayin ministan ayyuka da kwadago, Sai kuma Bianca Odinaka Odume...