An Ba Su Madarar Yougot A Matsayin Gwarazan 'Yan Wasa A Wasannin Gasar Kwallon Ta Birnin Kudu Dake Jihar Jigawa.
Wani kamfani ne ke daukar nauyin bada kyautar domin karfafawa matasan 'yan wasan.
Me za ku ce?
Daga Imam Murtadha Gusau
Wasu jajirtaccin matasa 'yan sakai wadanda suka sadaukar da rayuwar su tare da lokacin su, wurin kariyar al'ummah, sune suka farmaki Kacallah Black tare da tawagar yaran shi, a daidai lokacin da suka samu labarin cewa shararren dan ta'adda Black ya fito zai je wurin wata aika-aika, an samu nasarar kashe Black da yaran shi akalla kusan su 10, a wani yanki na dajin mai tashi dake yamma ga 'Yar Tashar Sahabi dake kan hanyar Dansadau, an samu nasarar kwato mashuna da bindigogi tare da alburusai na wannan dan ta'addar da na yaran shi.
Rahotannin da suke zo muna daga mazauna yankin 'Yar Tashar Sahabi, suna nuni da cewa wannan gagarumar nasara ce aka samu domin wannan dan ta'addar shine ya addabi yankin hanyar Dansadau zuwa Magami da kuma wasu bangarora na yankunan....
Bayan Bidiyon farko da ya nuna Jarumar Tiktok Hafsat Lawancy tsirara tana wasa da kanta, Wani Bidiyon nata ya sake fita.
A wannan karin shima bidiyo ne na nuna tsiraici amma baikai na farkon muni ba saboda tana sanye da kaya.
Saidai duk da haka abin ya dauki hankula inda akai ta Allah wadai.
Tuni dai hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama Hafsat tare da wasu 'yan mata kan lamarin.
Shugaban Hukumar Hisbah na Kano. Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da kamun na Hafsat.
Kalli Sabon Bidiyon anan
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce Isra'ila ta kashe mutum aƙalla 100 a wasu hare-hare ta sama da ta kai ƙasar.
Hakan na kunshe ne cikin sabbin alkaluma da ma'aikatar ta fitar, inda ta ce an kuma jikkata mutum sama da 400.
Hezbollah ta harba gomman rokoki zuwa kudancin Isra'ila, a cewar ƙungiyar a wata sanarwa.
Ta ce ta far wa shingayen sojoji da kuma wuraren ajiye makamai ta hanyar amfani da makamai masu linzami,a wani matsayin martani ga hare-haren da Isra'ilar ta kai kudancin ƙasar.
A wata sanarwa ta daban, dakarun tsaron Isra'ila (IDF), sun ce an harba rokoki aƙalla 35 daga Lebanon kuma hakan ya shafi shingayensu.
An jikkata wani mutum mai shekara 50 a yankin Galilee, a cewar sojoji Isra'ila.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojin saman ƙasar sun kakkaɓo rokoki da dama da Hezbollah ɗin ta harba yayin da wasu kuma suka yi lahani a wasu yankuna kusa da garin Ami'ad.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin jihar ta karɓi kusan naira biliyan huɗu da rabi daga cikin fiye da naira biliyan 13 da aka yi musu alƙawari a matsayin tallafi ga waɗanda ibtila'in ambaliya ya shafa a Maiduguri.
"...naira 4,441,494,902.81 ne suka shigo hannunmu daga cikin alƙawuran N13,195,500,000 da aka yi mana. Za mu ci gaba da sanar da jama'a duk lokacin da aka samu ƙarin shigowar kuɗi" In ji gwamna Zulum.
Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kafa kwamitin mutum 35 da zai kula da raba wannan tallafi ga waɗanda al'amarin ya shafa.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijjani ya fitar, ya wallafa a shafin X na gwamna Zulum, gwamnan ya ce kwamitin zai ƙunshi wakilai daga hukumomi da ...
Wani tsoho dakw rawa a wajan Maulidi ya dauki hankula sosai bayan da aka ga bidiyonsa a shafukan sada zumunta.
Kalli Bidiyon a kasa:
https://twitter.com/bb_khamees/status/1837826273663414293?t=R_hZyH8aRHUgtZ0lNpgtmQ&s=19
Wasu dai na ganin hakan bai dace ba inda wasu ke cewa duk cikin shauki ne.
Ban Take Sunan Annabi Muhammad S.A.W A Jikin Kafet Dina Ba, Sunana Ne A Jiki, Amma Duk Wanda Yake Da Wata Gamsasshiyar Hujja Da Ta Fi Tawa, A Shirye Nake Da Na Karbi Gyara, Inji Sarki Muhammadu Sanusi II
Kasar Yahudawan Israela sun jefawa kasar Lebanon Rokoki 300 a wani sashi na ci gaba da yakin da suke da kungiyar Hezbollah.
Kasar ta Israela dai a cewarta ta gargadi fararen hula dasu tashi daga kusa da gidajen 'yan kungiyar Hezbollah kamin su kai hare-haren.
Kasar tace ta gano 'yan Kungiyar Hezbollah dake shirin kai mata hare-haren Rokoki shine ta dakile su.