Saturday, January 3
Shadow

Duk Labarai

Su Kwankwaso da Abba suna son shiga APC ne dan su lalata mana ita>>Inji Ganduje

Su Kwankwaso da Abba suna son shiga APC ne dan su lalata mana ita>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa su Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf zasu shiga APC ne dan su lalatata. Saidai yace abinda basu sani ba shine ba zasu barsu ba. Yace idan suna tunanin suna Yaudarar Talakawa, su gogaggun 'yan siyasa ne ba zasu iya yaudararsu ba. https://twitter.com/KafinHausaa/status/2005922151933571520?t=4U2ryTNwQPRMV3Y2ayJb9g&s=19
Kalli Bidiyon: Ta bayar da shawarar a saka dokar yin wa’azi ta yanda idan an gama Sallah kowa ya tafi gidansa ya karanta Qur’ani

Kalli Bidiyon: Ta bayar da shawarar a saka dokar yin wa’azi ta yanda idan an gama Sallah kowa ya tafi gidansa ya karanta Qur’ani

Duk Labarai
Wannan baiwar Allahn tace ya kamata a saka dokar yin wa'azi musamman a Arewacin Najeriya. Tace wasu malaman basu cancanci su rika yin wa'azi ba lura da abinda suke gayawa mabiyansu. Tace zai fi kyautuwa idan an kammala sallah, kowa ya tafi gida ya karanta Qur'anin sa ba sai an zauna an yo wa'azi ba. https://www.tiktok.com/@excellency.sky/video/7588660919677226261?_t=ZS-92eQbmavJbN&_r=1
Da Duminsa:Kalli Yanda aka gurfanar da Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami tare da dansa a kotu inda ake zarginsa da karkatar da Naira Biliyan 212

Da Duminsa:Kalli Yanda aka gurfanar da Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami tare da dansa a kotu inda ake zarginsa da karkatar da Naira Biliyan 212

Duk Labarai
Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami a kotu inda ake zarginsa da laifuka 16. Wani abinda ya dauki hankula shine An kai Malamin kotu ne tare da dansa. Saidai ya musanta duka laifukan da ake zarginsa da aikatawa. https://twitter.com/NigeriaStories/status/2005931235583926579?t=1vEI1ddcXWm5DxMSwy3TvA&s=19
Kalli Bidiyo: Wushe nan, Inji Mawakin Najeriya, Burna Boy bayan da ake ce wai Ana rade-radin Dala Miliyan $22 ya mallaka

Kalli Bidiyo: Wushe nan, Inji Mawakin Najeriya, Burna Boy bayan da ake ce wai Ana rade-radin Dala Miliyan $22 ya mallaka

Duk Labarai
Mawakin Najeriya, Burna Boy, Ya bayyana cewa yafi karfin Dala Miliyan $22. Ya bayyana hakane yayin da ake hira dashi aka tambayeshi cewa, wai ana cewa dala Miliyan $22 ya mallaka a Duniya? Sai yayi dariya yace ba zai fadi nawa ya mallaka ba amma a bar mutane su yi ta hasashe. Da aka tambayeshi ko kudin nasa sun wuce haka? Yace sosai ma. https://twitter.com/festus23619/status/2005753740419276829?t=C0BAsZzzJY9v4eP02QP-QA&s=19
Kalli Bidiyon: Dama tun a watan October ni an min Wahayin Anthony Joshua zai yi Khàdàrì>>Inji Wata Fastuwa

Kalli Bidiyon: Dama tun a watan October ni an min Wahayin Anthony Joshua zai yi Khàdàrì>>Inji Wata Fastuwa

Duk Labarai
Wata Fastuwa ta bayyana inda tace tun a watan October aka mata Wahayin cewa shahararren dan Damben Najeriya, Anthony Joshua zai yi hadari kuma zai rasa was na kusa dashi. Tace tun a watan na October daya gabata ta bayyana hakan a wani Bidiyo data wallafa. Lamarin nata ya dauki hankula sosai. https://twitter.com/ChuksEricE/status/2005896633574125726?t=i5FVaMYoQNve5HFmCcDwmQ&s=19
Ofishin Jakadancin Ingila a Najeriya sun kaiwa Anthony Joshua ziyara a Asibitin da yake kwance

Ofishin Jakadancin Ingila a Najeriya sun kaiwa Anthony Joshua ziyara a Asibitin da yake kwance

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin jakadan kasar Ingila a Najeriya, Simon Field ya kai wa dan Damben Najeriya, Anthony Joshua ziyara a Asibitin da ya ke kwance a jihar Ogun bayan Hadarin da ya rutsa dashi. Sannan kuma ya gana da Gwamnonin Ogun, Dapo Abiodun dana Legas, Babajide Sonwo Olu kamar yanda me magana da yawun Gwamnan jihar Ogun,Kayode Akinmade ya bayyana. Yace suna bibiyar lamarin. A hukumance aka sanar da ofishin jakadancin kasar Ingila lamarin. Hakanan sauran wanda suka yi hadarin da Anthony Joshua suma an sanar da ofishin jakadancin kasashensu abinda ya faru.
Sai da na gargadi Anthony Joshua ya dana shigewa ‘yan Siyasar Najeriya, gashinan yanzu yaje yayi Hadari>>Inji Omoyele Sowore

Sai da na gargadi Anthony Joshua ya dana shigewa ‘yan Siyasar Najeriya, gashinan yanzu yaje yayi Hadari>>Inji Omoyele Sowore

Duk Labarai
Omoyele Sowore, dan Fafutuka kuma mamallakin Jaridar Sahara Reporters ya bayyana cewa, a baya yasha gargadin dan Damben Najeriya, Anthony Joshua kan ya daina shigewa 'yan siyasar Najeriya amma yaki. Yace gashinan yanzu ta fito fili, yayi hadari babu wani taimakon gaggawa na musamman da ya samu. Sowore yace shuwagabannin Najeriya cin hanci da rashawa ya musu yawa sannan kuma azzalumaine. A karshe yace yana taya AJ fatan Allah bashi Lafiya. https://twitter.com/sowore/status/2005896438425813219?t=XGLuxNIb8eJtHmye4dY_rA&s=19
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa zai tsaya takarar neman kujerar Sanata Natasha Hadiza Akpoti

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa zai tsaya takarar neman kujerar Sanata Natasha Hadiza Akpoti

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa, zai tsaya neman takarar sanata na kujerar da Sanata Natasha Akpoti ke kai. Ya bayyana hakane a fadar sarkin Ohinoyi dake Okene ranar 29 ga watan Disamba. Hakan ya kawo karshen rade-radin da ake kan cewa ko zai tsaya takarar ko kuwa. Yahya Bello dai na da case a EFCC inda suke Tuhumarsa kan zargin cinye wasu kudade har Biliyan 80 na jiharsa.
Kwankwaso da Sheik Isa Ali Pantami sun mika sakon jaje ga Anthony Joshua

Kwankwaso da Sheik Isa Ali Pantami sun mika sakon jaje ga Anthony Joshua

Duk Labarai
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da Sheikh Isa Ali Pantami duk sun aika sakon ta'aziyya ga dan Damben Najeriya, Anthony Joshua bayan da yayi Hadari. Sheikh Pantami yace yana mika sakon Jaje ga Anthony Joshua da iyalansa sannan yana mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/2005861959137145258?t=fl9bGYOHG6ZMOq5ksSCg7Q&s=19 Shima Kwankwaso ya nuna Alhini inda yayi fatan Allah ya baiwa Anthony Joshua lafiya. https://twitter.com/KwankwasoRM/status/2005708488199340207?t=ZhXdnfUTpZjYg7V3KAE6AA&s=19