Wasu Daga Cikin Kayayyakin Da Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina Ta Kama Hannun Masu Aikata Laifuka Daban-daban Katsina.
A Karkashin Jagorancin Kwamishinan Yansanda, Aliyu Abubakar Musa A Cikin Shekarar Da Ta Gabata, Wanda Jami'in Hulda Da Jama'a Na Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu Ya Baje-kolin Su Yau Alhamis.
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Duk da shigo da tsarin sayan tikitin shiga jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta intanet da gwamnatin Najeriya ta yi a shekarar 2021, har yanzu fasinjoji na shan dan karen wuya kafin samun shi.
Tsohon ministan sufurin kasar Rotimi Amaechi ne ya fito da tsarin a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, da nufin magance cuwa-cuwar saida tikitin da ake zargin ma'aikatan wurin na yi.
Gwamnatin Najeriya ta kashe naira miliyan 900 domin inganta hakan, sai dai bincike na baya-bayan nan da jaridar Solacebase ta fitar, ta raiwato a tashar jirgi ta Idu da Kubuwa a Abuja babban birnin kasar ya nuna bata sauya zani ba.
Dubban matafiyan da a kowacce rana suka dogara da jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna na shan dan karen wuya kafin samun tikitin, ko dai dalilin rashinsa a intanet...
Gwamnatin Najeriya ta ware naira biliyan 60 domin ciyar da 'yan makarantar firamare a sassa daban-daban na kasar a cikin kasafin kudin 2025.
Za ai aikin ne karkashin shirin gwamnati na farfado da tattalin arziki wato Economic Recovery Growth Plan (ERGP).
Jaraidar Dailty Trust ta tawaito cewa, kafin a sauya ministan ilimin kasar ya fara sanar da hakan wanda dama shirin ciyar da daliban yake karkashin ma'aikatarsa, kafin daga bisani a mayar da shi karkashin ofishin shugaban kasa.
An ware wa ma'aikatar ilimi kudi naira biliyan 348, cikin sama da naira tiriliyan 2. 517, wanda hakan na daga cikin fannin da ya fi samun kaso mai tsoka a kasafin kudin, duk da bai kai adadin da Bankin Duniya ya bayar da shawara na kashi 20 zuwa 30 cikin 100 na kasafin kudin ba.
Har wa yau, ma'aikatar il...
An kuɓutar da wani yaro ɗan shekara takwas, bayan shafe kwana biyar a gandun dajin zakuna da giwaye a arewacin ƙasar Zimbabwe.
Lamarin ya faru ne a lokacin da yaron mai suna Tinotenda Pudu ya yi ta gararamba a cikin gandun daji Matusadona Game Park, kamar yadda ɗan majalisar gabashin yankin Mashonaland, mai suna Mutsa Murombedzi ya kuma wallafa a shafinsa na X.
Kwanan sa biyar a dajin yana bacci kan duwatsu, ga kuma gurnanin zakuna da wucewar giwaye, babu abin da ya ke ci sai 'ya'yan itatuwa.
Gandun dajin Matusadona dai na ɗauke da zakuna 40, akwai lokacin da ya kasance wuri mafi yawan zakuna a Afirka, kamar yadda bayanan African Parks suka bayyana.
Wani jami'in ɗansanda da ya yi mankas da barasa a Zambiya ya saki wasu mutum 13 da ke tsare a ofishin 'yansanda domin su je su yi shagalin murnar sabuwar shekara.
Jami'ai sun ce an kama sufeto Titus Phiri bayan sakin mutanen da ake tsare da su a wani ofishin 'yansanda a Lusaka, babban birnin ƙasar.
Mutane 13 da ya saki, ana zarginsu da aikata manyan laifuka da suka haɗa da kisan kai da fashi.
Yanzu haka mutanen sun tsere, kuma tuni aka ƙaddamar da farautarsu.
Rundunar 'yansandan jihar Kano ta yi holen wata matashiya mai suna Shamsiyya da ake zargi da ƙwarewa wajen satar wayoyi a unguwanni daban-daban a Kano.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Abudullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an kama Shamsiyya ne ranar 21 ga watan Disamba bayan shafe tsawon shekara guda ana farautar ta.
''Shamsiyya ta ƙware wajen ɓullo da dabarun yaudara daban-daban don hilatar mutane wajen sace musu wayoyi'', in ji sanarwar.
Kiyawa ya ƙara da cewa wadda ake zargin kan yi aiki ne tare da wasu mutu huɗu da ke taimaka mata ciki har da ɗan adaidaita sahu da ƙwararre wajen cire wayoyi daga makulli, wajen gudanar da ayyukanta.
''Ƙwararriyar mai yaudara ce da ke shiga gidajen matan aure tare da sace musu wayoyinsu da kuma yin amfani da wayoyin wajen sace musu k...
Al’ummar garin shinkafin jihar Zamfara sun ce 'yanta’adda sun kai wani hari kasuwar garin inda suka tafi da gwammon mutane tare da jikkata wasu.
Mazauna yankin sun ce 'yanbindigar sun kai harin ne ana tsaka da cin kasuwar Shinkafin da ranar yau Alhamis.
Sai dai har kawo yanzu rundunar 'yansandan jihar ta Zamfara ba ta ce komai kan harin.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da gawurtaccen ɗanbindingar nan da ke cin karensa babu babbaka a jihar Zamfara, Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan al'umma.
A makon da ya gabata ne dai sojoji suka kama wani makusancin ɗanbindigar al'amarin da ya ce ya fusata shi kuma zai ɗauki fansa.
Babban malamin Kirista, Apostle Abel Damina ya bayyana cewa Annabi Adamu (AS) da Hauwa (AS) basu ci komai a gidan Aljannah ba.
Ya bayyana hakane a yayin da yake magana a cocinsa. Ya yi ta nanata cewa basu ci komi ba inda yace waye a wajan da zai iya bayar da labari?
Hakanan ya kara da cewa, Shan giya da shan taba ba haramun bane mutum ne da kansa zaiwa kansa fada dan daina yinsu.
Wadannan maganganu nashi sun jawo cece-kuce sosai inda da yawa suna tafi akan cewa baya kan daidai.
Kalli bidiyon jawabin nasa anan
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana hamayyarta ga ƙudirin dokar harajin da yanzu haka ke gaban majalisar dokokin Najeriya wanda shugaba Tinubu ya aike wa da majalisar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta ne ya bayyana haka a yayin bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2025 a dandalin Ma'ahaha da ke birnin Kano.
Wata sanarwa da ke ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba ta ce gwamnan ya ce "wannan kundin dokar harajin ba za ta magance matsalar tattalin arziƙinmu ba. Kano tana hamayya da wannan ƙudiri da zai shafi walwalaw al'umma."
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da tankiyya tsakaninta da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad wanda ya soki kundin.