Wasu Kiristocin Najeriya sun fito zanga-zanga inda suka nemi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gaggauta kawo musu daukin da ya musu Alkawarin kawowa.
Tsohon dansandan Najeriya, Sunny Anyanwu ya gabatar da Naira dubu 5 daga cikin dubu 49 da yake karba a matsayin kudin fansho ga sojan ruwa AM. Yerima.
Dansandan yace a aika masa da lambar asusun banki na Soja Yerima dan ya aika masa da kudin.
yace abinda sojan ruwan yawa Wike abin a yaba ne inda yace yana fatan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai baiwa sojan lambar yabo.
Turmutsutsu a gidan karamin ministan tsaro dake Gusau jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi sanadiyyar rasa rai daya wasu mutane 6 suka jikkata da yammacin ranar Alhamis.
Rahotanni sun ce lamarin ya farune da misalin karfe 7:30 na ranar Alhamis yayin da mutane suka taru a gidan nasa dan tarbarshi.
Zagazola Makama yace wanda ya rasun sunansa, Khalifa Uzairu kuma dan kimanin shekaru 23 ne.
Sannan akwai mutane 6 Ayuba Sani, Muhammadu Adams, Aliyu Aminu, Shaaban Hamisu, da Inusa Musa Shehu da su kuma suka jikkata suna karbar magani.
An kai jami'an tsaro wajan sannan an fara binciken yanda lamarin ya faru.
Wata tsohuwar malamar Jinya, Nurse ta dauki hankula saboda irin bayanan data fitar kan irin yanda ta gudanar da aikinta.
Tace wasu lokutan sukan canjawa me Jego Jariri ko kuma su dauke jariri me rai su ajiye matacce.
Tace suna sayar da Namijin Jariri akan Naira Miliyan 4.5 ko Miliyan 3. Hakanan sukan sayar da macen Jaririya akan Naira Miliyan 2.5.
https://twitter.com/instablog9ja/status/1989329219139051955?t=LzUAB8PG1hcsm4opoIK0ug&s=19
Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya rasu a Asibitin kasar Ingila.
Rahoton yace ya rasu ne bayan yayi fama da cutar zuciya da kuma cutar mafitsara.
Wasu na kusa dashi sun tabbatar da rasuwar tashi inda suka ce ya dade yana fama da cutar amma kuma ta zo mai ne yanzu farat daya.
Tauraron mawaki, Soja Boy ya sake yin waka da tsohuwar me saka Hijabi, Iftihal Madaki, a wannan karin ma dai ya sake kakkamata, kamar yanda yayi a baya.
Tuni Soja Boy ya saki Sabuwar Wakar.
https://twitter.com/OfficialSojaboy/status/1989245034622001235?t=kk0nH2_dTVnUmSfJCt6puQ&s=19
Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu, sun baiwa kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles Kyautar dala $30,000 akan kowace kwallo daya da suka ci, kamar yanda hukumar ta yi Alkawari.
An basu wadannan kudaden a dakin canja kaya bayan kammala wasan.
Kudin zasu kama jimullar Dala $120,000 kenan tunda kwallaye 4 'yan kwallon suka ci Gabon jiya.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1989341403743473669?t=PzA1PhpB30K0p8NJETDCqw&s=19
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, karya ake masa bai zagi sojoji ba a karawarsa da sojan Ruwa, AM. Yerima.
Wike ya bayyana hakane a ganawa da manema labarai inda ya fadi cewa ya tallafawa ayyukan jami'an tsaro a matsayin Ministan Abuja da yayi.
Saidai Sanata Dino Melaye ya bayyana mamaki da jin abinda Wiken yake fada.
https://twitter.com/_dinomelaye/status/1989321220186091774?t=qXOAiy_fMZ_s0x7gov8G8A&s=19
Wannan mutumin Yayi zargin cewa, Wani Asibiti a Abuja ya bari jaririnsa ya mutu saboda rashin iya aiki da kuma Naira dubu 8.
A Bidiyon da ya wallafa, an ganshi yana kuka a gaban asibitin yana zarginsu da rashin iya aiki da daukar 'yan Arewa aiki.
https://www.tiktok.com/@talk2davic/video/7572121131570728199?_t=ZS-91OQ4G8xWG8&_r=1
Malam Dr. Hussain Kano dake fadakarwa a kafafen sada zumunta ya mayarwa da Me Bakin Kiss martani bayan zagin da ta yi masa.
Malam yace yana mamakin mazan dake nemanta inda ya zargeta da kazanta.
Kalli Bidiyon jawabinsa anan:
https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7572492094338518328?_t=ZS-91OMOYZQMN6&_r=1