Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

Shugaba Buhari ya ce ba zai rubuta takarda ba kamar yadda sauran Shuwagabanni ke yi saboda gudun kada ya ɓatawa wasu mutane da iyalansu suna

Shugaba Buhari ya ce ba zai rubuta takarda ba kamar yadda sauran Shuwagabanni ke yi saboda gudun kada ya ɓatawa wasu mutane da iyalansu suna

Duk Labarai
Shugaba Buhari ya ce ba zai rubuta takarda ba kamar yadda sauran Shuwagabanni ke yi saboda gudun kada ya ɓatawa wasu mutane da iyalansu suna Mista Buhari ya ce ba zai yiwu ya rubuta takarda ba tare da ya ambaci sunayen wasu mutane ba wanda hakan ka iya jawo masu ɓacin rai ko bacin suna Me zaku ce?
Tawagar Gwamna Ta yi hadari

Tawagar Gwamna Ta yi hadari

Duk Labarai
Tawagar Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia ta yi hadari a garin Ihugh dake karamar hukumar Vandeikya dake jihar Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Lamari ya farune ranar Lahadi inda shaidun gani da ido suka ce daya daga cikin motocin tawagar gwamnan ce ta buge wani mutum ya mutu. Lamarin ya farune yayin da gwamnan ya je gida yin hutun bikin kirsimeti. Lamarin ya faru sau biyu ne a yayin da gwamnan ke zuwa gida da lokacin da yake dawowa. Saidai me magana da yawun gwamnan, Solomon Iorpev ya musanta faruwar hadarin da tawagar gwaman, yace mota daya ce wadda aka bari a baya sauran motocin tawagar gwamnan sun wuce ta yi hadarin. An tuntubi kakakin 'yansandan jihar,  SP Catherine Anene, saidai bata ce komai akan lamarin ba.
Yanzu Adadin ‘Ya’yana Da Suka Sauke Kur’ani Sun Kai Biyar, Inji Jarumin Finfinan Hausa, Iliyasu Tantiri

Yanzu Adadin ‘Ya’yana Da Suka Sauke Kur’ani Sun Kai Biyar, Inji Jarumin Finfinan Hausa, Iliyasu Tantiri

Duk Labarai
Ga abinda Tantari ya bayyana bayan wasu yaransa biyu sun sauke Kur'ani "Alhamdulillah!!! Allah cikin Rahamarsa da amincewarsa, a yau Lahadi 29/12/2024 aka yi bikin saukar Karatun AL'QUR'ANI na ya'yana guda biyu, ABDULMUMIN ILYASU ABDULMUMIN DA RAHAMA ILYASU ABDULMUMIN. "Yanzu Yarana biyar kenan suka sauke QUR'ANI da Izinin Ubangiji cikin su takwas da Allah Ya ba ni, ina alfahari da murna da wadannan yara matuka. Ina godiya ga Allah S.W.T da ya ba ni ikon kulawa da su har suka kai wannan matsayi. Allah Ya sa su amfani musulunci da musulmai a duniya".
NNPCL ya ce matatar mai ta Warri ta koma aiki

NNPCL ya ce matatar mai ta Warri ta koma aiki

Duk Labarai
Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPCL ya ce matatar mai ta garin Warri na jihar Delta ta ci gaba da aiki. Shugaban NNPCL Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a matatar mai ƙarfin tace gangar mai 125,000 a kullum. "Duk da cewa ba 100 bisa 100 take aiki ba, muna kan aikin gyaran," in ji shi yayin da shugaban hukumar kula da harkokin mai na kamfanin Farouk Ahmed ke yi masa rakiya. "Mutane da yawa na tunanin yunƙurin namu ba gaskiya ba ne. Suna tunanin ba zai yiwu a aiwatar da abubuwa na ƙwarai a Najeriya ba, amma muna so ku gani da idonku." Matatar da ke yankin Ekpan na Warri, an ƙaddamar da ita a shekarar 1978 domin samar da mai ga jihohin kudancin Najeriya bisa kulawar kamfanin NNPCL . A cewar mai magana da yawun NNPCL,...
Gwamnatin Nijar ta kori kamfanonin sadarwa na Faransa

Gwamnatin Nijar ta kori kamfanonin sadarwa na Faransa

Duk Labarai
A Jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin sojan kasar ta sanar da korar kamfanonin sadarwa na ƙasar Faransa na Camusat da Aktivko a duk faɗin ƙasar. Camusat na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a Nijar, da kuma Aktivko wanda ya ƙware wajen samar da makamashi ga turakun sadarwa na wayoyin salula. Wannan na zuwa ne a loƙacin da hukumomin mulkin sojan Nijar ke ci gaba da korar kamfanonin Faransa daga Nijar a ƙoƙarin raba gari da ita baki daya. Wata sanarwa da Ministan Sadarwa Sidi Muhammad ya fitar ta ce an haramta wa dukkan 'yan ƙasa yin aiki tare da kamfanonin, amma babu wani cikakken bayanin dalilin da ya sa gwamnatin ta ɗauki matakin a yanzu. Sai dai masu lura da al'amuran yau da kullum a Nijar na cewa matakin ba zai rasa nasaba da tsaron ƙasa ba. A gefe guda kuma, masu ...
Babu yarjejeniyar yin karɓa-karɓa tsakanina da Atiku – Kwankwaso

Babu yarjejeniyar yin karɓa-karɓa tsakanina da Atiku – Kwankwaso

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta raɗe-raɗin da ke cewa an cimma yarjejeniya tsakaninsa da tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun hamayyar ƙasar - Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP - kan cewa kowannensu zai yi mulki na wani wa'adi. A hirarsa da BBC, Kwankwaso ya ce bai san da maganar ba, amma ya samu labarin cewa ɓangaren Atikun na ta "yin taruka da shugabannin yankin ciki har da malamai, suna faɗa masu wannan magana".
Ni da ‘yan Najeriya muna cikin farin cikin gyara matatar mai ta Warri – Tinubu

Ni da ‘yan Najeriya muna cikin farin cikin gyara matatar mai ta Warri – Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce "shi da 'yan ƙasar suna cike da farin ciki" sakamakon gyara matatar mai ta garin Warri da kamfanin mai na NNPCL ya yi. Wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na X ya ce "hakan zai ƙara wa 'yan Najeriya ƙwarin gwiwa kan fatan da suke da shi game da alƙawuran da muka yi". Ya ƙara da cewa labarin "hanya ce mai kyau ta kammala shekarar 2024 idan aka ƙara da nasarar da aka samu kan matatar mai ta Fatakwal". Yayin wani taron manema labarai a yau Litinin, shugaabn kamfanin NNPCL Mele Kyari ya bayar da sanarwar cewa sun gyara matatar kuma ta ci gaba da aiki a matakin kashi 60 cikin 100 na ƙarfinta. A cewar Tinubu: "Tun da yanzu matatar Warri na aiki bisa kashi 60 cikin 100, tsarin gwamnatina na samar da tabbataccen makamashi yana kan hanya. "...
Zamu kawo Saukin Rayuwa>>Inji Gwamntin Tarayya

Zamu kawo Saukin Rayuwa>>Inji Gwamntin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan kudi da tattalin Arziki, Wale Edun ta bayyana cewa, zata kawo saukin rayuwa ga 'yan Najeriya ta hanyar saukaka farashin kayan abinci. Ya bayyana hakane bayan ganawa da shugaban kasar ranar Lahadi a Legas, yace gwamnatin zata samar da karin ayyukan yi a shekarar 2025 bayan samun saka hannun jari daga kasar Saudi Arabia Minista Edun bai dade da dawowa daga kasar Saudi Arabia ba biyo bayan ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai kasar kan maganar zuba jari a Najeriya. Ministan ya bayyana cewa sun dawo da albishir daga kasar Saudi Arabia cewa za'a saki karin ayyuka a Najeriya. Yace Kasar Saudi Arabia ta kara jarin da take dashi a bangaren kiwon dabboni a kanfanin Olam da dala Biliyan $1.2 Ya kara da cewa kuma a yanzu ana rani ne, zasu tabbatar an s...
Hankula sun koma kan Shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL yayin da saura kwanaki kalilan ya cika shekarun barin aiki

Hankula sun koma kan Shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL yayin da saura kwanaki kalilan ya cika shekarun barin aiki

Duk Labarai
Shugaban kamfanin mai na kasa, NNPLC, Mele Kolo Kyari, saura kwanaki kalilan ya cika shekarun barin aiki watau 60. Nan da ranar 8 ga watan Janairu ne dai Mele Kolo Kyari zai cika shekaru 60 wanda a doka ya kamata ya sauka daga kan mukaminsa dan a nada wani shugaban kamfanin. Mele Kolo Kyari shine shugaban kamfanin NNPCL da yafi dadewa akan kujerar tun bayan da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nadashi mukamin a ranar July 2019 inda a yanzu ya shafe shekaru sama da biyar akan kujerar kenan. Saidai inda gizo ke sakar shine Bayan da kamfanin NNPC ya koma na 'yan kasuwa ya fita daga hannun Gwamnati ya kuma canja suna zuwa NNPCL, doka ta baiwa Mele Kolo Kyari damar zai iya ci gaba da zama a matsayin shugaban kamfanin har nan da shekarar 2027. Wasu rahotanni kamar yanda jarid...
Mutanen dake zaune kusa da iyakar Najeriya da Nijar sun shiga fargaba biyo bayan sa in sar data barke tsakanin kasashen biyu

Mutanen dake zaune kusa da iyakar Najeriya da Nijar sun shiga fargaba biyo bayan sa in sar data barke tsakanin kasashen biyu

Duk Labarai
Wasu daga cikin mutanen dake zaune akan iyakokin Najeriya da Nijar sun shiga zullumi biyo bayan cece kucen da ya barke tsakanin kasashen biyu. Shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Brig Gen Abdourahmane Tchiani ya zargi cewa Najeriya ta girke sojojin kasar Faransa tare da kafa sansanin yiwa 'yan ta'adda atisaye. Saidai me baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya karyata wannan zargi inda yace Babu inda Najeriya ta kafa sansanin sojojin kasashen waje. Ribadu yace wannan kokari ne na kawar da hankalin mutane daga gazawar gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar. Da yake bayyana rashin jin dadinsa kan lamarin, wani mazaunin jihar Sokoto, Muhammad Illiyasu ya rantse da Allah cewa, cikin shekaru 30 da yake rike da sarautar Magajin garin Balle a karamar hukumar G...