Saboda jin dadin Cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tinubu ta yi da kakaba Haraji kala-kala akan ‘yan kasa, bankin Duniya ya baiwa Najeriya bashin Dala Biliyan $1.5
Rahotanni sun bayyana cewa, biyo bayan cire tallafin man fetur da kakaba haraji kala-kala akan 'yan Najeriya da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi, bankin Duniya ya baiwa Najeriya bashin dala Biliyan $1.5.
Cire tallafin man fetur da kakaba haraji, sharudane da bankin Duniyar ya gindayawa Najeriya wanda sai ta cikasu kamin ya bada bashin da ake nema.
Bankin Duniyar da farko ya fara sakin dala Miliyan $750m a cikin watanni shida wanda masana suka ce shine mafi saurin lokaci da Najeriya ta samu bashi.
Saidai sauran kudin bankin Duniyar yayi jan kafa wajan amincewa ya bayar dasu saboda Najeriya ta ki saurin kaddamar da fara karbar haraji.
Sauran kudin dai a hankali za'a ci gaba da sakarwa Najeriya su bisa sharadin cika wasu sharudda da bankin Duniyar zai gindaya.