Matatar man fetur din Dangote da kamfanin man fetur na kasa, NNPCL sun samarwa kansu wutar lantarki inda suka daina amfani da wutar lantarkin Najeriya
Yayin da wutar lantarkin Najeriya ta zama marar tabbas, kamfanoni da ma'aikatu 250 ne suka daina amfani da wutar da gwamnatin Najeriya da kamfanonin rarraba wutar na Discos ke samarwa inda suka koma samarwa kansu wutar.
Mafi yawancin kamfanonin na amfani da wutar lantarkin sosai. Gashi Gas yayi tsafa, ga kudin wutar ana karba da yawa ga wutar ba tabbas shiyasa suka samarwa kansu mafita.
A shekarar 2021, tsohon shugaban kaa, Olusegun Obasanjo shima ya dana amfani da wutar lantarkin Najeriya inda ya koma samarwa kansa wutar a dakin karatunsa dake Abeokuta jihar Ogun.
Jimullar wutar da wadannan kamfanoni ke samarwa kansu ta kai karfin 6,500 megawatts wanda hakan ke nufin karfin wutar yafi wanda Gwamnatin Najeriya ke samarwa wadda ke da karfin 5,000MW a mafi akasari.
Gwamnati tuni ...